Skip to content
Part 48 of 54 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Mai Kano yayi maza ya Rike hannun hajiya dake ta jibgar Husna tamkar wadda aka Aiko sai dura mata Ashar take Wai tayi butulci Akan tace Bata son Alh Aminu.

Hajiya Bata San da zuwan Mai Kano ba sai ganin shi tayi yana rike mata hannu.

Ta dubeshi tana mayar da numfashi sai kace wadda tayi gudun fanfalaki.

“Haba hajiya me tayi Miki haka da har kike Mata irin wannan dukan Kuma kina yi kina zaginta ? Ya fada Yana zuba Mata idon shi da ya gama cika tab da masifa.

Hajiya ta kwada mishi harara tana fadin. “To ko zaka Rama Mata ne kake zare min idanu?

“Ba Zan Rama Mata ba amma gaskiya ki Daina dukan ta Baki tausayawa maraicin ta kina duka Kuma kina zaginta? Gaskiya ba Zan dauki wannan abun ba hajiya Uwar ta ce ikon ki Amma ita ba ikon ki bace.

Sai saukar Marika yaji a fuskar shi hagu da Dama…

“Ai kai Kam na Dade da Gane ba karamin Dan iska Halima ta Haifa ba tunda ka tsoma kafarka a Legos kukayi bankwana da mutunci to ba a Nan zaka gwada min kalar iskancin da ka koyo ba ku da Halima duka akarkashin ikona kuke mutumin banza tashi ka bace min da gani.

Ya Mike Yana kallon ta kallon da ya Bata tsoro matuka Gaya.

“Ni Zan iya shanye komai da Zaki ce hajiya Amma na Rantse Miki idan kika Kuma kirana Dan iska Zan nuna Miki iskancin da akeyi a garin Legos ba irin na katsina bane.

Kuma mu babu wani ikon da kike dashi Akan mu uwar mu ce kawai ikon ki Kuma ko ita din a yanzu ba kowane ikone Zan Bari ki nuna Mata ba don Haka Husna Kuma koma me tayi Miki Baki da hurumin dukan ta cikinta Kika dauka Koko nakudar ta kikayi? To in ma don tana zaune agidan ku NE Kika gaji kike Mata wulakanci tana da gidan uba Kuma tana da NI yanzun Nan zata bar Miki gidan ki bare ki zageta don Kinga kasa ta Rufe idon mahaifin ta Uwar ta Kuma da Baki damu da sanin halin da take ciki ba ta faku. .

Ya kamo hannun Husna ya finciko Yana fadin tashi mu tafi can Legos ki zauna a hannu na.

Hajiya da tayi maza ta Cabo hannun Husna ta Rike tana ja shima Yana ja suka Soma janta tamkar zasu tsaga ta gida biyu.

Fizga guda yayi Mata sai gashi tana Shirin cin kasa inda Kuma Allah ya kawo kawu Amadu kanen Halima Wanda shi hajiya ta ce ya karbo mata Husna daga hannun Mai Kano.

Amadun shi yace ya saki hannun Husnar ya Kuma saki Yana Huci.

“Kai wannan yaro anyi shaidani. Cewar hajiya wadda ta tausa husna daki don tasan idan Mai Kano ya tafi da Husna ya maida Mata aiki Baya.

Mai Kano kuwa da zuciya ta ciwo Bai ko tsaya sun gaisa da kawu Amadu ba sai dai cewa da yayi da kawu Amadu.

“Kar a sake dukanta don Bata da banbanci da marainiya. Daga Haka ya fice kawu Amadu na fadin.

“Ho Mai Kano ikon Allah shi dai Bai dauki wargi ba. Ya dubi hajiya Yana fadin.

“Hajiya me hado ku da Mai gidan naki ne haka ? Ya fada Yana murmushi hajiya ta ce.

“Akan Auren Yar Uwar shi ne yake kokarin zagina shi Dan iska Wai har yarinyar Nan ta iya bude Baki tace Wai Bata son Alhaji Aminu.

“Au Wai hajiya dama Baki tambayi Husna ko tana Ra ayi ba kuke ta shige da fice Haka? Gaskiya haj idan yarinyar Nan Bata muradi a hakura tun yaushe aka Daina yayin wannan Auren? Indai Haka ne ai Mai Kano Yana da gaskiya hajiya.

“Kai tashi ka bani wuri Amadu kaima in an biye taka kana layin masu butulcin Ni Kuma babu Ni a layin masu butulcin. Duk yadda yaso nunawa hajiya illar dake akwai akan abinda suke Shirin yi Bata saurare shi ba karshe ma cewa tayi idan ya Kuma sako bakin shi a maganar Ranshi ne zai baci Dole ya kyale amma Kuma Yana ganin kamar an SHIGA hakkin yarinyar da yawa.

Husna da taso bin Yaya Mai Kano ko don ta tsira daga Auren Alh Aminu Amma Kuma hakan Bai yuwu ba Kuma tana da yakinin idan da yaji dalilin dukan ta da hajiya keyi akan auren Alh Aminu ne da zai tsaya Mata tsayiwa irin ta daka don ganin ba a yi Mata wannan Kama karyar ba sai ta jawo wayar ta ta SHIGA laluben layin Mai Kano inda Kuma tunanin ta ya koma Kan Yaya muhsin Wanda shine asalin Wanda yafi cancantar yaji abinda ke faruwa tunda ya sanar da ita duk abinda ake ciki ta Kira ta sanar dashi don Haka sai ta Rabu da Mai Kano ta komawa Yaya muhsin.

Bugu Biyu kawai ya daga yajiyo shesshekar kukan ta inda take sanar dashi ta faru ta Kare Auren ta da Daddy.

“Kina Ina yanzu? Ya fada murya na Rawa. “Ina masanawa ta bashi amsa. Ya fito a Rikice Yana nufar kofar fita sukayi kicibus da Alh Aminu Wanda ya Kira shi.

Ya taho Yana duban mahaifin nashi da wani kallo na ka kusa kasheni.

Ya karaso gaban motar ya sunkuya Yana mishi barka da dawowa

Ya amsa fuska murtuk Yana dauko tarin IV Yana Miko mishi.

“Karbi wannan katin ka kaiwa Alh bukar wannan Kuma ka kaiwa Alh sabo wanna Kuma ka kaiwa Alh Rabe kace ya bawa su Alh Adamu da su Alh Sani Mai canji wannan Kuma ka Rabawa duk mutanen da kasan Ina mu Amala dasu.

“Daddy katin meye? Ya fada Yana duba katin Wanda ya Fara Arba da sunan Husna da na Daddyn da sauri ya saki tarin katinan suka zube kasa kafin ya damke kafafun Alh Aminu Yana gunjin kuka.

“Daddy kayi min Rai don Allah kace min mafarki nake wallahi idan na Rasa Husna na Rasa farin ciki Mai yawa daddy da son ta na Rayu don girman Allah kace min mafarki nake dama na karanto soyayyar Husna a fuskar ka har na karyata Ashe Daddy da gaske kake.

Kyawawan Marika ya bashi har Biyu.

“Kana zaton ban San halin da kuke ciki bane Kai da Husna? Ina sane da hakan sai dai Kai da kanka ai kasan Husna ba sa ar ka bace Ni nafi Dacewa da ita don Haka daga yau sahu Daya husna take takawa da uwarka ka manta da ka taba son ta a Rayuwar ka Zan Haram ta maka duk wani Abu da zai tuna maka ka taba son Husna ko da kuwa zaman ka a gidan Nan ne zai tuna maka hakan shiyasa nayi maza na Aura maka Safina ai na fita hakkin ka ko? To tashi maza kaje inda na aike ka . Cikin tsananin jiri da hajijiya ya Mike abin tausayi ya Soma tafiya Yana tangadi har ya fice kafin ya kwala mishi Kira ya dawo.

Ya dubeshi a fusace Yana fadin, “Akasa zakaje can ne? “Kayi hakuri Daddy bana cikin nutsuwar da zanyi tuki. “Matsalar ka ce in ma da Rarrarfe zakaje.

Ya shige gida ya barshi shi Kuma ya fita Yana waswasi Akan Ina zai Fara zuwa ? Kai katin ko kuwa wurin Husna? Kawai sai zuciyar shi ta Raya mishi yaje ya ga wane Hali Husna take ciki sai kawai ya tsayar da napep ya nufi masanawa.

Mubarak ya dubi Zaidu bayan ya gama waya da hajiya dake sanar dashi daurin Auren Husna Ranar asabar. Cikin mamaki Mubarak ke fadin.

“Wane irin Aure ne Haka bagatatan? Kuma ma mu ai ba ta Auren Husna muke ba ta uwar mu muke Amma ita hajiya sai wannan ikon Allah da Rayuwar takeyi? Zaidu da haushi ya kule shi yace.

“Ka sani ko ita Husnar ce ta ce taji ta gani?”

“Ko ita tace taji ta gani zaidu zamu biye Mata ne? Bana zaton hakan ma daga Husna Kai dai zakaji Amma. Bari na Kira Mai Kano shi nasan yasan komai.

Ya kuwa doka mishi Kira ya daga bayan sun gaisa Yake tambayar shi ba asin auren Husna.

“Wane irin Aure Kuma Yaya Mubarak? Husna ce da Aure? Ko dai bakaji daidai ba?

“Yanzu muka gama waya da hajiya take fada min wai Ranar Asabar ne daurin Auren shine na kiraka don inji waye zata aura Haka kamar tashin Duniya.

Mai Kano yayi shiru cikin nazari kafin ya hada uku da biyar suka bashi takwas cikin bacin Yace.

“Naje katsina shekarn jiya Amma ya akayi Ni hajiyar Bata sanar Dani ba? To ko Auren ne Husna Bata so Wanda har yayi dalilin da hajiyar ta ke dukan ta? Naje na samu hajiya ta Rufe Husna da duka to amma Bari na Kira Husna naji daga bakin ta Zan Kira ka idan mun gama magana . Da Haka sukayi sallama ya Kuma Kira layin husna ta daga cikin dasasshiyar murya Wanda kukan da ta Sha ya haifar Mata da mura da zazzabi

Bayan sun gaisa ne Yake tambayar ta dalilin dukan da hajiya tayi Mata. Ta kuwa kwance mishi jakar sirrin tiryan tiryan akan maganar Auren ta da baba Aminu.

“Wane Alh Aminu? Ya fada da Amon murya ta tabbatar mishi baba Aminu dai.

Bai Ida Jin abinda zata fada ba ya katse wayar da sauri ko shiri babu ya nufi tashar mota Amma babu mota don Haka Kai tsaye ya nufi murtala muhd ya yanki tikitin jirgi ya nufo garin katsina.

<< Hawaye 47Hawaye 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×