Skip to content
Part 49 of 68 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Napep ya dire muhsin a masanawa ya Kira wayar Husna ya sanar da ita gashi a kofar gidan. Cikin sa a kuwa haj na bandaki tayi wuf ta fito don a cewar hajiyar Wai ta gama taka ko Ina sai fa Ranar da za a Mika ta gidan miji.

Aguje ta fito sukayi Arba da muhsin Wanda ido ya Rikide jajur kamar Mai ciwon ido

Suka zubawa juna ido HAWAYE na kwaranya kafin Husna ta Rushe da kuka tana fadin
“Kaga abinda Daddy yaja Mana Yaya muhsin? Kaga maganar Anty Amal ta tabbata?.
Na Rasa dalilin da Daddy ke son kashe Ni da Raina. Saboda Allah ta Yaya Zan iya duban Mami ? Da wane idon? “Ba Zan boye maka ba Yaya muhsin ban shirya karbar Daddy a matsayin mijin Aure na ba Wallahi ko za a daka Ni daka irin na sakwarar Yan Legos na Rantse maka ba zanyi zaman Aure da Daddy ba ko da kuwa Kai din ka badawa soyayya ta kasa a ido.

Ya fito da kyallen share zufa daga aljihun shi Yana share mata HAWAYE.

“Husna Daddy yayi Mana ta Yan Duniya Nima Kuma nayi nufin yi mishi ta Yan zamani ko da kuwa yayi nasarar Raba zukatan mu da gangar jikin mu to shima kuwa zuciyar shi da gangar jikin shi ba zata taba hutawa ba .

Ya zube Mata katin gayyatar Auren su Yana fadin “Duba Nan Wai Daddy Ni Yake bawa katin Auren ki Husna Wai na Raba ban sani ba ko Daddy Yana zaton Babu zuciya a kirji na? Koko Yana ganin ban Kai sanin Darajar so ba?

“Yaya muhsin Ina son Jin abinda ka yanke akaina don in San matsayin katin Nan a wurinka? Ya damki hannunta ya Rike.

“Na kula hajiya ta karbi maganar Nan da muhimmanci saboda Daddy Yana Mata kyauta.

“Hajiya ta dakeni Yaya muhsin tamkar aikakkiya saboda kawai nace bana yin Daddy to Dama nayi shiru ne don inji mahangar da ka aje soyayya ta.

“Bani minti biyar na dauko mota ta gida na Gama yanke hukunci Akan soyayyar mu Husna.

“Minti biyar a yanzu na komawa ta gidan Nan daidai Yake da shekaru dari biyar don yanzu ma saboda hajiya ta SHIGA ban daki ne na samu fitowa idan na koma kamar nayi sake da damar mu ne don Haka muje kawai dama gobe zuwa jibi nake da sauran hikima ta yankewa kaina shawara don Sai dai su shafa suji Babu Ni.

Ai kuwa suka taho ya tsaida musu napep suka taho har kofar gidan su inda ya barta ya SHIGA ciki ya dauko key din motar shi ya fito ya sallami me napep ya ajewa Daddy tarin katinan shi a kofar SHIGA falon shi . Husna ta shigo motar ya fafareta tamkar zai daga sama har Yana daukar over taking fatan shi dai yayi nesa da garin katsina.

Jirgi ya sauke Mai Kano Wanda duk saurin tafiyar sai yaga jirgin yayi mishi nawa don Haka jikin shi har Rawa Yake Akan ya karaso gidan hajiya ai kuwa ya iso gidan inda ya iske hajiya tana ta lissafin kudade don batayi zaton Husna ta fita ba azaton ta ma tana daki kwance sai da taga Mai Kano ya shigo Yana Huci tamkar mesa kafin ta tattere kudin ta ta Adana. Ta dubeshi a sheke tana jiran yace Mata kulle tace mishi casss don ta gama Gane kaf yaran Halima babu fitinanne irin Mai Kano tun gurzawar da sukayi.

Aka Rasa me tankawa tsakanin su sai kallon kallo suke kafin shi ya tanka a zafafe.

“Yaya Mubarak ya kirani Yake sanar Dani Auren Husna Wai Nan da kwana biyar saboda Allah hajiya har nayi lalacewar da Zaki kasa sanar Dani Auren Yar Uwata ? Wai hajiya wace irin tsana Kika yi Mana ne don Allah? Wai kin manta mune iyayen Husna ko da iyayen mu na Raye? Kuma duk mutanen Duniya masu mutunci ki Rasa Dan iskan da Zaki Aura Mata sai wancan matsiyacin? Wai Dame mutumin Nan Yake siye Ra ayin ki ne da imanin ki? To hajiya a bar abinda ake kokarin aiwatarwa don ban yarda ba ba Kuma Zan yarda ba idan mazan Duniya zasu Kare sai Alh Aminu na Rantse Miki sai dai Husna ta mutu a gwauruwar ta in ma kudi kike karba to ki mayar mishi da abinshi kice ya sameni muyi magana Amma muddin Kika nace da maganar Auren Nan na Rantse da Allah ke dashi sai na farke cikin ku na fito da kayan cikin ku waje. Kece kawai Zaki tsira daga hakan idan kin cire bakin ki daga maganar Auren Husna shi kuma dama na fada nine AJALIN shi Kuma a yau Zan nuna Miki Husna Bata da wani uba bayan Ni don Zan tafi da ita ne inda Baku Isa isketa ba.
Hajiya da ta kawo Marin taji Rokon da yayiwa hannun nata sai ta SHIGA surfa mishi zagi tana la antar shi.

“Allah ya tsine maka Mai Kano in baka tafi da Husna ba Kai dai yaro ne marar Albarka Ni da Kai sai Naga me karfin iko Uwar ka ma Bata Isa na gitta Kara ta ketare ba bare Kai abin banza.

“To Bari Naga ikon naki a kanta.

Ya Mike da sauri Yana bankada labulen dakin Yana jefa idon inda zai hango Husna inda itama hajiyar ta shige dakin a guje don ta Rike Husna sai dai shiru ta Basu labari.

Ta SHIGA laluben Husna kusfa kusfa na gidan Amma ko kyallin ta Bata hango ba inda Kuma hajiya ta kwalla uban ihu tana fadin akawo Mata agaji mai Kano zai kashe ta. Wani sabon sharri ma sai da ta maida kofar dakin ta Rufe su ita da Mai kanon don ma Kar ya gudu.

Ai kuwa Kan kace me? Gida ya cika dankam da mutane mussamman matar kawu Amadu wadda katanga ce kawai ta Raba su inda ta Kira kawu Amadu ta fada mishi abinda ke faruwa sai dai baya kusa Yana bisa hanyar Kano don zuwa kasuwa inda hankalin shi yayi masifar tashi Jin ance Wai za a kashe mishi Uwa.

Duk bugun kofar da akeyi don hajiya ta bude Taki budewa sai kwala ihu take tana fadin Akira Mata Alh Aminu yazo ga Mai Kano Nan yazo sun hada Baki da Husna ya sace ta ya Kai ya boye yazo Kuma Yana tuhumar ta.

Ai kuwa ba a Rufa minti Sha biyar ba Alh Aminu ya bayyana inda Kuma hajiya ta bude dakin tana fadin ya Kira hukuma ya danka me Kano har sai yayi bayanin inda Husna take.

Da sauri kuwa Alh ya Kira DPO ya sanar dashi abinda Yake bukata sai ga motoci har uku na kamun Mai Kano inda hajiya ke ta Rattabo bayani sharri kala kala inda hankalin Alh Aminu yayi masifar tashi yadda yake son Husna in ya Rasa ta kuwa ai akwai damuwa
Agefe guda Kuma da ma Yana so ya samu damar da Mai Kano zai shigo hannun shi sai gashi abin yazo mishi da Zaki da Kuma madaci. Burin shigar Mai Kano a hannun shi da Kuma asara Rasa Husna da Yake kokarin yi.

Don Haka sai ya kulla makircin shi na cewa Mai Kano Yana neman Rayuwar shi bayan satar matar da Yake Shirin Aure karshe ma sai yace Yana daya daga cikin masu yi mishi barazana ta sacewa da neman kudin fansa. Wannan maganar ita ta Dame Al amarin Wanda aka tsananta ga Mai Kano da son lallai sai ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa laifi kuwa kusan kala takwas Wanda Bai San da su ba.

Rashin sanin laifukan da ake tuhumar sa yasa ya kasa amsawa har ta Kai da an Fara dukan shi duka Kuma ba na wasa ba amma ya tsaya Akan Bai San komai ba Akan abinda ake tuhumar shi Dole aka SHIGA bincike.

Ranar asabar su Mubarak suka tawo daurin Aure shi da Zaidu sai dai sun Tara’s da sabon labari Wai Mai Kano ya hada Baki da Husna ta gudu koma ace ya boyeta amma fa cewar hajiya. Da sauri Mubarak shi da Zaidu suka nufi station inda Mai Kano yake Amma aka Hana su ganin shi Wai Wanda ya kulle shi ne Bai bada umarnin abar kowa ganin shi ba duk magiyar su ba a saurare su ba Dole suka hakura suka juyo.

Sai da suka dawo gidan hajiya ne take fada musu ai Alh Aminu ne yasa aka daure shi don shine dama Wanda zai Auri Husna.

Zaidu ya Mike Yana fadin Amma dai gaskiya baba Aminu baiyi min nisan tunani ba Yana ganin hakan zai sa asamu mafitar da ake nema? Ya dubi Mubarak.

“Taso muje wurin baba Aminun mu Roki da yasa a saki Mai Kano in ma da gaske ne shi yasa Husna guduwa zamu sa ya fito da ita fatan mu dai ya sa a saki Mai kanon.

“Kai Zaidu fita idona kaima in ko kace ba Haka ba kaima zancewa Alh Aminu ya hada da Kai a Rufewa don bakaji abinda Mai Kano ke fada ba ? Yana fadin sai ya farke cikin mu?

“Hajiya Ina kokon to Akan yadda Auren Husna ya faro na tabbata husna Bata muradi kuke kokarin tursasata ko ke ko Mai Kano to duk abinda Alh Aminu zaiyi min Akan Mai Kano Zan dauka don Mai Kano jini na ne Kuma Ina da yakini Akan bisa gaskiyar shi yake ko da Mai Kano ke da fitina baya yin marar tushe wannan ma tabo shi akayi don Haka zamuje mu sameshi ko da zai hada mu ne ya Rufe duka mun shirya hajiya.
Ya Kama hannun Mubarak suka fice zuwa gidan Alh Aminu.

<< Hawaye 48Hawaye 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×