Skip to content
Part 61 of 76 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Suna kewaye da Mai Kano Wanda Bashi da maraba da gawa suna shakar kuka kamar wadan da suka Rasa lissafin su sai Kuma Husna ta cewa Amal.

“Anty Amal mu bar kukan Nan ba mafita bace mu kaishi Asibiti

Amal ta tsayar da kukan ta suka Kama Mai Kano suka saka mota suna nufi Asibiti inda aka bawa Mai Kano gado aka Kuma SHIGA bashi agaji har ya dawo aka jona mishi drif . Kudin da aka nema na magani babu komai a hannun Husna sai Amal ce ta koma gida ta dauko ATM akayi komai ta Kuma SHIGA hidima da Mai Kano don tana ji a Ranta itace tafi kowa Dacewa da tayi abinda yafi Haka don Haka daga ita sai Husna ke jinyar Mai Kano Wanda idon shi ke bude Yana kallon su suna mishi hidima Amma ganin Amal na tuno mishi da ita din ta fito daga Ahalin da ba zai taba yiwa sassauci ba Kuma yake Jin tsana fiye da tsanar da akewa mutuwa. Tun Daren da ya farko a gadon Asibitin yaso ya fatattaki Amal Amma Kuma sai yaga Bata cancanci wulakanci ba musamman da Husna ta kankame hannun shi Wanda yasha yankan wukar tsini tana fada mishi irin kokarin da Amal tayi tun daga Ranar har yau da yafarko take wahaltawa da jikinta da aljihun ta Ashe kuwa gaskiya batayi Kama da karya ba Amma Kuma Aran shi Yana Masifar jin tsanar Amal Aran shi ba don ita kanta ba sai don Rabar Alh Aminu da tayi. A da can lamarin Bai Fara ba yanzu ne zai Fara Dole ya hadiye ya barwa tashin sa Akan gadon likitan.

Su tsini kuwa da suka auna aguje helux din ta Mara musu baya tana dab da cimmasu da suka ga zasu fada komar kwalawan sai suka haura wani kango inda Kuma tsini dake da Rabon wahala suma kwalawan da suka ga zasu tsere sai suka auna su da bindiga aka Kuma yi nasarar samun tsini a kafa cikin gwiwa Amma dai yayi nasarar haura kangon Dole kwalawan suka juyo . Abinda ya faru Kuma shine tun Ranar da su tsini suka cakumo Mai Kano a bakin titi wani Dan sanda da hakan ta faru Kan idon shi shine ya biyo bayan su Amma kwanar da suka biyo ita ce ta batar dashi ya kasa Gane inda su tsini suka nufa . Sai hakan ya bada damar kullum sai Anzo sabeyin a wurin har Ranar da dubun su ta cika aka gansu Ashe Allah shine Allah ba Rabon wahala ga Mai Kano sai Allah ya tona asirin su tsini aka tarwatsa su shi Kuma Mai Kano Allah ya hada shi da Yar Uwar shi da masoyiyar shi suka Kuma dauki abin su. Amma Kuma har gobe ba a bar bibiyar gidan na su tsini ba da son a mamaye su.

Barrister nura da barrister Ahmed ne suka shigar da maganar tsare Muhsin da akayi inda kotun tasu ta Rubuto takardar neman beli Dole Kuma aka bayar da belin.

Yana fitowa aka danka mishi komai nashi ya fito Kai tsaye gidan baba Hassan ya nufa wurin Mami inda sukayi kicibus da Alh Hassan din Yana gaishe shi shi Kuma Yana fadin ya akayi ya fito? Ya sanar dashi kotun su CE tayi belin shi.

“Ai ina Nan Ina jiran uban ku ya tako kafar shi gidan nan zai Gane akwai maza a gaban shi shi din karyar iskancin yake har Ni Alh Aminu zai duba ya fada min babu Ruwana da sabgar gidan shi to Ni Allah yasa kuskure ya kawo shi nawa gidan sai na tuna mishi abinda ya manta. Shi dai muhsin hakuri Yake ta bayarwa inda ya wuce ya barshi Yana fadin Suma Kar ya Kuma ganin kafar dayan su a gidan su tabbata a gidan uban su marar mutunci.

Haj wasila tayi murmushi tana karewa muhsin kallo ganin yadda ya fita a hayyacin shi itama tambayar yadda ya fito take mishi ya Kuma fada Mata yadda kotun tayi belin shi. “Kar ka sake dai kace zaka bar garin Nan a yanzu Amma ka tabbatar ka zamo cikin sirri don yadda mahaifin ka ya zamo a yanzu komai zai iya faruwa Amma Kar ka yarda kace zaka bar gari ni Kuma dama na gaji da Zama dashi sai gashi ya furta da Bakin shi baya bukatar ganina kusa dashi to sai kowa ya tsaya matsayin sa.

“Hakuri Zakiyi Mami shima zai sauko ne.

“Inyi hakuri ayi Yaya kenan? Bakaji abinda na fada maka ya ce min ba? Ai tunda na Gane burin shi matar ka Toni Kuma Zan tsaya har sai Naga burin nashi Bai cika ba ada ne bana Ra ayin ka da Husna Amma yanzu tunda nagane itace burin Aminu to kuwa zai mutu burin shi Bai cika ba don Haka tashi kaje Allah yayi maka Albarka ya Kuma tsareka daga sharrin uban ka dama duk abin halitta ka Kuma dauki matar ka kuje ku.

Da haka ya yi Mata sallama har tana bashi kyautar kudi Amma yaki karba Yana fada Mata yana da kudi a account.

Yana zuwa gidan Hamis yayi wanka sai ya Nemo lambar Salma ya Kira Yana neman Husna inda salmar ta sanar dashi Bata Nan taje Asibiti.

“Waye Babu lafiyar Salma? Ya tari salmar ita Kuma ta fada mishi yaya Mai Kano ne Amma yaji sauki…

“Wane Asibiti Yake ne Salma? Ya tambaye ta ta sanar dashi K Dara Yake yanzu ma zataje wurin su ya Bari idan taje zata hada shi da Husnar.

“Bari dai nazo sai muje tare ko Salma? Ok to Bari na jiraka. Minti biyar kuwa ya Isa kofar gidan su Salma ta fito suka nufi Asibiti.

Amal tana zaune Akan gadon da Mai Kano Yake Yana bacci Amal ta zuba mishi ido tanajin yadda son shi ke narka zuciyar ta sai Kawai taji HAWAYE na bin idon ta ba don komai ba sai don Rashin sa ar ta ga soyayyar Yaya Mai Kano don kallon da ta kula Yana Mata kallo ne irin na Wanda ya zubar maka da abin shanka na bude Baki dab da Kiran magruba . Dama tuni ta gano Rashin sa ar da ta tako Mai Kano baya yinta ita kuma a Duniya tace ba maza sai shi kadai.

Ta kamo hannun Mai Kano ta jimke anata hannun tana magana tamkar idon shi Biyu. Me nayi maka da zafi Haka? Wane irin aibu ne Dani da har nakasa samun zuciyar ka ? Zan iya yafe maka idan har so gaskiya ne Zan iya yafe maka idan har sonka yayi Ajalina. Allah idan har Wanda nake so ba zai karbeni ba to ka gaggauta yin Ajalina in huta da azabar son shi. Mai kano da ya Jima da farkawa yajiyo kalaman ta Wanda suka Kona Ran shi matuka Gaya har yayi nufin fincike hannun shi sai kuma yaci gaba da sauraron ta inda Kuma Salma ta sayo kai Kuma kalamar ta karshe da Amal ta furta ta doki kunnen ta har taji jiri na neman kayar da ita . Mai kanon ne wata ke furta mishi irin wannan kalmar? Watan ma hamshakiya irin Amal? Sai taji ta kurma ihu koma ta juya ta bar Asibitin Amma Dole ta SHIGA saboda Amal din ta ga shigar ta bayan ta Kuma Yaya muhsin ya biyo Wanda yayi daidai da fitowar Husna daga bandaki sukayi ido Hudu da muhsin yayin da Kuma Mai Kano ya bude idon shi fess Akan salma.

<< Hawaye 60Hawaye 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×