"Daddy me kayiwa Mai Kano a matsayin shi na dan ka Dan abokin ka? Ka bani amsa ta Daddy.
Wani matsiyacin Mari Muhsin yaji ya sauka Akan fuskar shi Wanda har wata walkiyar da Babu hadari ya gani. Da sauri kuwa ya dafe kumatu Yana kallon yadda Daddyn Yake cika da batsewa tsabar fushi.
"Duk zanci Kan abun ubanku Kai da Mai kanon idan ya Isa ya fada maka abinda Yake ikirarin nayi mishi don uban shi shine ka Zo ka sakani gaba tana tuhuma ta Kai ubana? Wato bakaji kashedin da nayi maka na tsame kanka daga lamarin Husna. . .