Skip to content
Part 64 of 76 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

“Koma waye Kika Kira Bai Isa Raba wannan Auren naku da Alh Aminu ba mutuwa ce kawai zata Raba shi Wallahi Amma ba dai Dan Adam ba.

“Sai mutuwar ta Raba ai in na kashe shi Kuma Wallahi ke Zan ce Kika bani wannan shawarar Kinga sai mu SHIGA kason tare dake ! Cewar Husna wadda tayi maganar da tabbaci Akan fuskar ta, Hajiya ta juyo ta dubeta, “Kikace me Husna? Itama ta dubeta tana Kara maimaita mata abinda ta fada.

“Cewa nayi idan ya mutu sai Auren ya Rabu don wallahi Zan kasheshi ne in Kuma mayar da maganar ta koma zance ince ke Kika dorani Akan hakan don Haka sai ki shirya.

Hajiya tayi gwale da baki da ido tana kallon Husna cikin takaici da mamaki.

“To don ubanki dake kwance a kushewa in kin fasa kashe Alh Aminu Baki haihu ba Ni Kuma Zan nuna Miki in ma Mai Kano ne ya Baki wannan shawarar wahala kawai Yake kokarin jawo Miki Ni Kuma Zan nuna muku Baku Isa ba don Haka tashi kije ki shirya don yanzu zai Zo ku wuce.

Ta yiwa Hajiyar wani mugun kallo tana Jan tsaki ba tare da tankawa hajiyar ba Bata Kuma yi niyar tashi ba don tana ganin Bata da amsar bawa hajiya muhsin kawai take tsumayi don zuwan shi ne kawai Raba gardama.

“Ba ki ji abinda nace bane wai ? Hajiya ta fada tana zaro mata ido, “Naji yine ba Zan ba.

Zuciya ta ciwo hajiya ta yi nufin dukan ta Amma Husna tayi maza ta Rike hajiyar da duka karfin ta.

“Hajiya nafa gaji da yi Miki kawaici kina duka na bafa fin karfina kikayi ba in Kuma kince A a to na Rantse Miki Zan Rama ne Aure ne nace banayi tunda Kuma kika nace Wallahi kece da kuka don abinda na fada haka nake nufi.

Kugin motar da Husna tajiyo shi ya sata sakin hajiya ta kwasa aguje ta nufi waje hajiya ta Rufa Mata baya don ta San muhsin ne yazo zasu gudu ita Kuma ba zata taba Bari su sake guduwa ba. Sai dai kafin su Kai ga ficewa Alh Aminu ya sayo kai soron gidan inda Husna ke shirin fita ta ganshi Haj Kuma tace ya taro Mata Husna Kar ta fice ai kuwa ya Cabo ta ya yi RAM da ita ya Rike hajiya na fadin ta godewa Allah da ya kawo shi don Haka ya wuce da ita kawai tunda guduwa take nufin yi.

Alhaji Aminu ya bude mota Yana saka Husna wadda ke kuka ba kukan komai ba sai na jinkirin muhsin da ya kasa isowa har ta fada tarkon da suka D’ana Mata.

Hajiya ta koma ta dauko katon mayafin ta yafawa Husna dake Duke da kanta tana zubar HAWAYE don ganin tazo hannu.

“Munafuka Ina jiran duk abinda kike sakawa a Ranki Zaki Gane taurin Kai matsala Yake bawa me yin shi haka Hajiya ta gama rufe ta da mayafin tana jan kunnen ta kafin ta mayar da murfin motar ta Rufe tana cewa Alh Aminu ya turo mota ta kwashi kayan ta na kichen da na daki.

“To Haj Zan turo koma nazo na dauka da kaina da Haka ya jawo motar Yana ficewa daidai da muhsin ya karyo kwana ya hango motar Daddyn shi da Husna a ciki inda itama kamar ance ta dago ta hango muhsin Yana fitowa a motar idon su ya gauraya inda taji wani kuka ya keto Mata tayi saurin saka hannu tana Rufe bakin ta don kar ya fito.

Muhsin da yayi tsaye kamar Wanda aka dasa Yana kallon yadda Alh Aminu ke fafarar motar kamar zai tashi sama har ya kulewa ganin shi sai kawai ya tsuguna Yana dafe kanshi dake sarawa tamkar zai tsage sai Kuma HAWAYE suka SHIGA wanke mishi fuska don yasan Daddyn ya gama dashi tunda har yayi nasarar daukar Husna har gashi zai kebe da ita meye ba zai faru ba?

Sai Kuma yaga wautar da ya tafka ta barin Daddyn ya wuce ba tare da ya bi bayan shi yaga inda zai Kai mishi Mata ba.

Kamar Wanda aka zabura ya Mike Yana SHIGA mota ya figeta ya hau titi Yana fatan ya hango Daddyn Amma ko kyallin motar shi bai hango ba.

Sai tunanin shi ya bashi gida ya nufa sai ya wuce gidan Amma babu motar Daddyn inda ya Gane ba gidan ya yo da Husnar ba sai Kuma ya Kuma fita a motar Yana zaga gari tamkar wani zautacce Yana fatan yaga Uban nashi Amma ko Mai Kama dashi Bai gani ba. Sai ya koma gefen titi Yana kuka me cin Rai da zuciya matar shi ce Wai uban shi ya dauka a matsayin tashi me yasa Daddyn yayi mishi Haka bayan yasan an daura Auren su? Wani tunani ya darsu a zuciyar shi sai kawai ya jawo wayar shi Yana Kiran layin Daddyn sai da tayi Ringing sau uku tana tsinkewa sai a Kira na Hudu yaji ya dauka Yana tambayar lafiya?

“Daddy da gaske ka Auri Husna bayan na fada maka akwai igiyar Auren mu ? Na Roke ka don girman Allah Daddy Kar kace zakayiwa Husna wani Abu matata ce Daddy na Roke ka kayi min komai akan kula Husna.

“Kar ka sake Kiran wayata Muhsin kana jina? Babu wata igiyar Auren ka Akan Husna in ma Akwai ta na sakar maka ita kaje masanawa hajiya zata baka tabbaci so Kar ka Kuma tuna cewa Husna matar kace in kuwa ka kwata haka Zan baka mamaki shashasha marar tunani Kai da kayi son zuciyar ka me nace maka Koko sai Nima don nayi son zuciya ta zaka kirani kana min magiya?

“Don girman Allah Daddy Kar kayi min Haka.

Ya antaka mishi ashariya Yana fadin in ya Kuma yi mishi magiya zai la ance shi karshe ma sai datse Kiran yayi ya kashe wayar gaba Daya

Husna dake zaune ta hade Kai da gwiwa tana rizgar kuka a cikin dakin hotel din a huta hotel don Bai nufi kowane gida ba sai hotel don can Yake ganin zai Fi sakewa Akan tace daya daga cikin gidajen zai sauka

Ya kwabe babbar Rigar shi ya zauna kusa da Husna dake share hawaye Yana Rarrashin ta.

“Kinga ya Isa Haka Husna kinji Daina kukan Nan don Allah Yana tada min hankali me kike so yanzu nayi Miki shi? Ki Gane Mana tsananin kaunar ki da nake Babu abinda ba Zan iya yi Miki ba kinji Yar Amarya ta? Ya fada Yana Rage murya cikin Rarrashi.

“Daddy ka cuceni na fada maka muhsin nake so bakai ba me yasa kake son kashemu da Ran mu ? A Ina ka taba ganin an yi Aure Kan Aure? Da wace fuskar Zan dubi Mami ace na aurar Mata miji? Da wace fuskar Zan dubi Anty Amal ace na Aurar Mata mahaifi? Daddy don Allah ka Bari nayi ta kallon ka a matsayin Uba ba ba miji ba don ban shirya hakan ba idan da gaske zakayi min abinda nake so to ka mayar Dani ga mijin da Ubangiji ya bani wato Yaya muhsin sakin da kake fadar kayi mishi Bai yi ba shine me ikon sakin Auren shi da kanshi ba wani ba don Allah don Annabi Daddy ka Rabu Dani ka mayar Dani inda ka dauko Ni ta fada tana karawa kukanta sauti. Yayi shuru Yana kallon ta sonta na Kara Huda zuciyar shi inda Yake Jin ko Bai saki Auren ta ba tunda ta shigo hannun shi ai ba zai maida ta ga muhsin ba shi din yafi Muhsin sonta don Haka ya Rarrashe ta Yana fadin ta Bari ya kawo Mata abinci.

Ya fita Yana Kiran wayar lauje da Yake fada mishi ga fa Husna tazo hannu da Kuma irin abinda take fada mishi.

Laujr ya kyalkyale da Dariya Yana Fadin.
“Zata Soka ne ko don Dole mutumina Ina tozalin Nan da na baka?

“Na Gane shi lauje Yana cikin mota ta don kar na Kai shi gida na Rasa inda Yake sai kawai na saka shi a dash.

Yauwa to ka dauko shi ka shafa a idonka ka tabbatar da kunyi Ido Hudu da ita tana kallon ka zata mance wani Muhsin a Duniya sai Kai kadai zata ji tana kauna har gadon ka sai ta iske ka duk ajin Nan nasu na Mata kuwa sai ta nuna maka kauna fiye da zaton ka don Haka Kar kayi garajen da sabbin angwaye keyi tunda Kai din ai ba sabon SHIGA bane m”Sabon SHIGA ne Mana lauje Kai dai ka saurari goron ka don har ga Allah na manta da batun wani tozali wallahi Amma yanzu Nan ma Zan shafa shi a idona idan har aiki yayi kyau babu wani daga kafa da zanyi wa yarinyar Nan don na wahala akan sonta Kai dai sai na xo kaji kome kenan da Haka ya aje wayar Yana lalubo kwallin cikin sa a kuwa ya samo shi ya daga tandun Yana Kare mishi kallo kafin ya bude ya Soma shafawa a idanun shi duka shafi kuwa me yawa don dai ya shafu da kyau ya kuwa budada shi ya mayar ya aje kafin ya mayar da gilashin ya kuwa kwashi lededin kajin da kayan sanyin ya haura dakin da Husna take Yana fatan komai ya tafi daidai.

<< Hawaye 63Hawaye 65 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×