Skip to content
Part 68 of 76 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Bude dakin yayi da key ya SHIGA da gudu Husna ta makale ajikin shi Yana Bata hot kiss tare da Kara kankame ta ajikin shi itama har tana kwantar da kanta a kafadar shi.

Ya zube Mata kayan kwalam da makulashe da ya jibgo Mata Yana cire hular shi ya Dora Akan kujera Yana nufar ban daki . Ta bude fan vanilla tana tsotsa cikin shauki

.Mai kano da ya shigo riseption sukayi magana da time service din sai ya haura sama dakin me lamba Sha takwas cikin sa a kuwa ya tura yaji shi a bude idon shi ya hasko mishi Husna dake Shan fan hankali kwance

Jin an turo kyauren yasa ta dago Kai sukayi Arba da Yaya Mai Kano Wanda yaso kifa Mata Mari saboda tsabar takaici amma sai ya fasa saboda ganin in yace zai mareta Aikin shi zai kwana tunda har yayi sa ar samun ta ita kadai sai kawai ya ficiko hannunta ya ingizo suka Soma saukowa inda take nufin yi mishi bore ai kuwa ya falleta da wani matsiyacin Mari Wanda ya sata shiga hankalin ta da Haka ya tsayar da napep suka nufi Tasha don baya Jin zai barta ta Kara kwana a garin katsina.

Zuwan su tashar ya sallami napep ya yi Shatar mota guda wadda ta tashi dasu ta nufi garin Legos

Kai tsaye gidan Uban gidan shi Alh sulaiman Dan sodangi ya nufa da Husna dake sharar HAWAYE Kuma hawayen ba na komai ba sai na Rabuwa da Alh Aminu Wanda Mai kanon Bai fahimci hakan ba da ya fahimci hakan kasheta ne kawai ba zaiyi ba a zaton shi ma yadda Rayuwa ke gyare da ita ne damuwar ta .

Bayan sun gaisa da haj Laila matar Alh sulaiman ne Yake fada Mata Amanar Husna ya kawo Mata don Allah ko kofar gidan baya son ta leka har zuwa lokacin da komai zai warware

Haj Laila Bata San abinda kenan ba ta Kuma amsa da babu komai dama su yaran su ba fita suke ba sai da Dalili.


Ya nemi ganin alhajin inda haj Laila ta sanar dashi sunje kurmiyal gaisuwar matar abokin shi Alh Dan iro

Tabbas ya San abokin shi Alh Dan iro har matar tashi ma haj naja mace Mai kirki don sunyi mishi kirkin lokacin da Alh sulaiman ke Aiken shi wurin Dan iron Dole ne in ya nutsu yaje yayi mishi gaisuwa. Don Haka yayiwa haj Laila gaisuwa Kuma yace in Sha Allah zaije can kurmiyal din yayi musu gaisuwa

Da zai tafi ne ya kebe da Husna Yana hararar ta. “Wato ke ga makwadaiciya an Tara Miki kayan kwalam kin bude Baki kina lamushewa har Yana yaudarar ki ya kaiki hotel . Halan ma yayi Miki wani Abu? Ya fada murya a ksurare.

Tayi saurin kada kanta.

“Me yasa Kika tsaya har hajiyar ta danka mishi ke Baki gudu ba? Ba kece Kika ce min an daura Auren ki da muhsin ba? Tayi tsai da ido tana son tunawa waye muhsin ma? Ganin Shirun ta ya sa ya Dora kashedin shi


“Ba Uban muhsin ba ko shi muhsin din in har wahayi akayi musu dake sai jinin su ya bi Rariya Wallahi ki tsaya a Nan Zan Rika Zuwa Ina duba ki kafin nasan yadda Zan iya sanin halin da mama take ciki kafin na dawo kanki ke da wadan can Ahalin marassa mutunci.

Da Haka ya fice ya bar Husna da tsabar begen Alh Aminu Wanda takejin tamkar zuciyar ta zata tarwatse har ma ta Fara tunanin hanyar da zata bi ta koma gareshi don shine takeji amatsayin Rayuwar ta.

Fatowar Alh Aminu daga ban dakin ya samu falon wayam babu Husna Babu dalilin ta.

Ya Soma wurga idanu da son ya hangota Amma ko kyallin ta Babu.

Ya saka Rigar shi da sauri Yana Jin gaban shi na faduwa gaba Daya ya Rikice wace irin Rashin sa a ce dashi ? Yau din da ta tabbatar mishi jinin ya tafi Kuma me ke shirin faruwa?

Ya sauko da sauri Yana tambayar time service din Husna shi Kuma ya fada mishi Bai ganta ba saboda yanzu ya karbi abokin Aikin shi.

Da sauri ya fice ya SHIGA motar ya figeta zuwa masanawa gidan hajiya yake zayyane Mata abinda ke faruwa na Rashin ganin Husna

Haj da gefen fuska ya kumbure Mata saboda watsin alatsinen da Mai Kano yayi da ita acikin kayan kichen har ta kume da tukunyar karfe Wanda ya kwalje Mata gefen fuska Dole ta kawu Amadu ya Nemo Mata confo tana shafawa

Ta dubi Alh Aminu da kumburarriyar fuska tana fadin.

“Ba kowa ya dauke ta ba sai Mai kano don Nan yazo Yana wulakanci dubi abinda yayi min dama yace sai ya bar min tabon da Zan tafi kiyama dashi gashi Kuma ya bar min.

Ya kadu matuka Gaya da jin Mai Kano ya sake SHIGA lamarin shi a karo na biyu inda yake dab da cikar buri ta leko ta koma kenan ko ga koshi ga kwanan yunwa.


“Wannan yaro na Rasa ko wane irin shaidani ne shi kadai Daya Amma ya addabi mutane? Cewar Hajiya


Ya dubi hajiya Yana tambayar ta inda Mai kanon Yake a yanzu?

“Wallahi ban San inda Yake ba sai dai ko ka Kira lambar shi kaji. Da sauri kuwa ya Kira layin Amma a kashe Dole ya hakura yayi wa haj sallama ya nufi gida da son gano inda Husna take. Isar shi gida ya Tara’s da muhsin sai kawai yayi ta faskawa Muhsin din Mari don yanzu yafi ganin Muhsin din ne ya hada Baki da Husna tunda shi Mai kanon ai Bai San suna hotel ba.

“Ina Husna take? Ya fada Yana zarewa muhsin ido.

“Daddy ai Kai Zan tambaya tunda na ganta a motar ka… Ya Kuma faska mishi Mari Yana fadin Wallahi sai ya fada mishi inda Husna take ko ya hada shi da hukuma wadda zata iya batar dashi idan Bai Fadi gaskiya ba.

Wayar shi tayi tsuwwa ya dakata da sababin da Yake zubawa muhsin ganin bakuwar lamba yasa ya mayar da wayar Yana fuskantar muhsin Yana Kara tutsiye shi. Amma nacin da akeyi wa kiran nashi yasa ya dauka a fusace Yana fadin waye? Shesshekar kukan tace ta bashi amsa


“Daddy don Allah kazo

“Husna kina Ina ne? Ya fada ya manta da Muhsin Yana wurin

“Daddy gani Nan Legos Yaya Mai Kano ya kawo Ni don Allah kazo Daddy.

“Relax my baby kwantar da hankalin ki yanzu kuwa zanzo a ina kike ne? Muhsin da yayi mutuwar tsaye Jin abinda ke faruwa inda Kuma ya juyo kwatancen da Husna ke bashi na unguwar har da sunan Mai gidan wato Alh sulaiman Dan sodangi. Da sauri ya nufi dakin shi don yin Shirin zuwa Legos inda muhsin ma yafi shi sauri don kafin ma ya gama Shirin shi har ya fice ya yanki tikitin jirgi.

<< Hawaye 68Hawaye 69 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×