Karar da Alhaji Aminu ya saka ita ta tsorata goloko me gadin gidan ya taho da sauri sukayi taho mu gama da Mai Kano dake kokarin fita fuska murtuk Yana wurgawa golokon harara
Isar falon na Alh Aminu ya hango halin da yake ciki ya na dafe da Mara ga jini na nashe wandon farar shaddar shi.
Ya Isa gare shi daidai da sumar da ya yi yana shirin kifewa amma goloko ya tare shi ya dauko shi a kafada ya fito Allah Yasa yaga key din motar shi sai kawai ya wuce dashi Asibitin kudi na Dr K Dara. . .