Skip to content
Part 76 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Hajiya Wasila ta kamo Anty maimuna dake ta watsi da kayan gidan Wai aljanu alhalin kunya ce kawai tasa ta hawan borin ba wasu aljanu.

“Maimuna ba wannan ne abinyi ba asan yadda Za ayi da mutumin da yayiwa Safina wannan Aikin shine abinyi ba tashin aljanun karya ba abinda ya faru a baya ya wuce gaba ya kamata mu duba da neman hanyar gyara. Safina ya ta ce in kina zaton Zan tona Asirin ta to Zan tonawa Amal mu Kori shaidanin da ya SHIGA tsakanin mu kawai ba gaba da adawa ba.

Sai ga Anty maimuna ta dawo kyandamas har aljanun sun sauka. Ta Rungume Yar Uwar ta tana bata hakuri da neman yafiya suka kuma yafi juna har suka aje magana Kan a Kira su murtala Samarin Safina duk da ita kanta ba zatace ga uban cikin ta ba Amma ance a sanar dasu Wanda in ta haihu za ayi gwajin jini agano uban Dan ko diyar Wanda haj wasila tace za a danka mishi abin shi Kuma Haka maimuna ta yarda don tace duk yadda tace haka za ayi.

Amal da tajawo trolly tana shirin ficewa sukayi kicibus da Alh Aminu inda taji bakin ciki na neman shaketa.

“Ina zuwa Haka Amal? Ya tambaya Yana kallon ta ganin yadda ta hade rai.

“Daddy Zan bar gidan Nan don nayi nesa da Kai don bana bukatar a kalle Ni akuma kalli abinda kayi ace ubana ne yayi shi. “Daddy Duniya ce kake so Koko giyar kudi ce ta kaika aikata wannan abun me kama da a wata Duniya ba Duniyar musulmi ba? Sai kuka ya kwace mata tayi ta shekawa ya zuba Mata ido yana Jin lallai karshen shi ne ya taho tunda har Amal ta Soma shako wannan sirrin na boye

Ya Riko hannun ta Yana son su fahimci juna Amma sai ta kwace hannun ta tana share HAWAYE.

“Daddy ka gama Bata Mana suna ka Gama kunyata Ni a inda nake Jin kunya.

“Daddy da wane idon Zan kalli su Husna da mahaifiyar su? Daddy me matar Nan tayi maka? Me tayi maka Haka da zabi hargitsa Mata Rayuwa?

Anan ya Gane komai ya faru har ya Kare tunda Amal ta San abinda yayiwa Halima.

“Ki saurare Ni Amal na sanar dake abinda Baki sani ba.

“Babu abinda ban sani ba Daddy komai yazo Akan idona na kumaji na Kuma gani shine ma Zan bar gidan Nan Daddy Kai Kuma zanyi maka ADDU A Allah Ubangiji ya ganar dakai ya kuma yafe maka Amma kafin na tafi Zan Roke ka Alfarma guda Daya Tak don yanzu ne kake da sauran Dama Allah ba zai jiraka har ka tuba ba Daddy idan Duniya kake so shin yau Ina mahaifan ka? Daddy Ina mutanen da ka taso ka gansu suna Rayuwa yau Ina wasun su? Duk abinda kaga ya faru to akwai Ranar da zai Kare DUNIYA zata Kare abin cikin ta ma zai Kare tuba ce kawai Bata karewa ga masu Rabauta kafin Rufewar kofar . Daddy ka yafe Ni ka Kuma yi min wannan Alfarmar na ta komawa ga Ubangiji na tafi wata kila mu sake haduwa wata kila Kuma sai a lahira Yana kallo ta ja akwatin ta tayi gaba tana kuka shima ga mamakin shi sai yaji idanun shi sun kawo HAWAYE jikin shi Kuma ya mutu Akan nasihar Yar tashi wadda shi da kanshi yasan yazo gargara sai da ya gama share hawayen shi kafin ya hau sama inda Kuma ya iske haj wasila tana dakon shigowar shi Amma Bai saurare ta ba ya maido kyauren dakin ya Rufe inda yaga hayaki na fitowa ta ban dakin shi ya karasa da sauri Yana neman ta inda Yake fitowa sai ya ga ta cikin lokar dake ban dakin hayakin Yake fitowa ya karasa da sauri don tunawa da yayi Nan dodon kod’in shi Yake ciki ya fizgo handle din lokar sai yaga akwatin da dodon kod’in ke ciki ne ke hayaki ya jawo akwatin Yana budewa duk ya hada zufa
Halittar dodon kod’in ce ta kone kurmus har ta juye wata kalar halittar me abin tsoro inda yajiyo ihun haj wasila ta kwarara ihu saboda abinda ta gani Wanda Bai San ta shigo dakin ba don Haka sai ya Kara Rudewa har ya saki akwatin kasa ya tarwatse. Aguje haj wasila ta fice daga dakin shima da sauri ya dauko akwatin ya nufi gidan lauje sai dai me zai Tara’s? Tun a kofar gidan Laujen ya hango yadda wuta ke toroko tana daga harshen ta sama Alamar komai na gidan take son lashewa agefe ya yi parking motar shi Yana kallon gidan inda zuciyar shi ke sanar dashi babu ko tantama Zubaina ce da wannan Aikin yayi tsaye da akwati na bulbular hayaki Yana Kuma kallon wutar da ke ci saman gidan Laujen.

Can ya hango laujen ya fito da Jan gindi daga gidan ya karasa gareshi da sauri Yana neman kamo shi Amma laujen ya tsayar dashi da hannu Alamar Kar ya tabashi saboda Yana ganin shine silar faruwar komai don Haka shima ya jira sakamakon shi.

“Wai me ke faruwa ne Lauje?

“Uwarka ce ke faruwa mutumin banza har bakin tambaya ma gareka? To ka saurari sakamako ka Ni daga taimakon ka na samu wannan sakamakon kaima zasu Zo gareka Dan iska me kunnen Kashi da kayi abinda suke so da zaka ja Mana wannan Bala in ne? To Zubaina tace an konata an kashe Mata dodon kod’i da Ya’yan ta ta Rantse ta Kuma tace Ni da Kai sai ta kassara Rayuwar mu gashi Kuma ta Fara da Kona min gida Wanda iyaye da kakanni na gajeshi yau ta kone shi har da kayan Aikina ta kone Kuma duk sanadin abinda kayi ne.

“Kaga lauje Nima hayaki na gani a inda dodon kod’in Nan Yake shine na duba sai gani nayi ya kone shine na taho naji meye abin yi?

“Nace maka uwarka ce abinyi bakaji abinda nace bane Wai? Babu wani abinyi sai in har suka kasheni ta silar ka na Rantse maka Babu Kai babu zaman lafiya don duk Zan sauke maka bakaken aljanun Nan da bakaken Rauhanai su Hana ka zaman lafiya Kai duk wata tsiya ma Zan bar maka ita akanka yadda Kaine zaka girbi mugun Aikin da na shuka tunda Kai kaja min.

Lauje Bai dire maganar shi ba suka ga wuta ta nufo su a guje Alh Aminu ya saki akwatin hannun shi ya nufi mota inda Kuma wutar ta iske lauje Wanda yaso ya motsa shima ya gudu Amma kafafun shi suka Fara kawo mishi gardama tuni Kuma wutar ta Soma sukuwa ajikin shi Akan idon Alh Aminu Wanda yayiwa mota key ya auna aguje zuwa gida inda ya iske sakon Kiran Alkali Wanda a yau akayi Zama kotu Amma Bai Zo ba inda sako ya Riske shi Akan lallai gobe ya iso kotu in kuwa ba Haka ya Raina kotu kenan kuma zai fuskanci hukunci ya dafe kanshi yanajin Duniya na gyare gyare da shi.

Karar jawo kofa yasaka shi dagowa yayi Arba da haj wasila ta nufo shi da takarda a hannun ta wadda ta Miko mishi tana Kara murtuke fuska.

“Yanzu nags wannan takardar a dakin ka Wanda bincike ya kaini na Kuma ga abubuwa na mamaki da suka nuna min Aminu Duniya ka Aura har ka karkace ka ke neman tabewa koma nace ka tabe Amma dukkan abin mamakin da nagani Babu Wanda ya tsorata Ni irin wannan takardar da ke nuna min wai ka samu matsala part pravet Kuma saboda Kai Azzalumi ne kake ikirarin ka mayar da igiyar Aurena? Dama kunbiya kumbiyar da kake min kenan kana fada min baka da lafiya? To ai Kai da kanka kasan ba Zan iya Rayuwa dakai a Haka ba ko Babu wannan bakin fentin da ka gamayiwa Ya’ya da Ahalin ka har da ZURIA Dole ne mu Rabu Rabuwa Kuma ta har Abada.

“Kar kiyi min Haka wasila Wallahi Allah shaidan ne ya Ribace Ni ke kanki ai kin San ba halina bane.

‘kaima shaidanin ne Aminu koma nace ka zarta shaidan shaidanci don Haka ya Zama Dole na barka duk yadda nake son ka don Bala in da kajawo Kai kadai ya kamata ya hadiye tunda ai kasani ko a LAHIRA laifin wani baya shafuwar wani don Haka na tafi Kar Kuma kayi tunanin Bina don ba zan Kuma sauraranka ba.

Da sauri ya Riko ta Yana Kuma Yana magiya Wai Kar tayi mishi Haka Amma ta fincike hannun ta ta Kuma fice ta barshi Yana zare idanu sai kuma ya Mike Yana safa da marwa don ya tabbatar Zubaina na gamawa da lauje shi ta nufo tashi Kuma zata fi ta lauje Muni in lauje ya ci wuta shi jahannamar Duniya Zubaina zata jefa shi sai ya SHIGA tunano manyan ibadojin da ya Dade baiyi ba irin su sallar asubahi da juma a da Kuma la asar har da Isha I shi kanshi ba zaice ga lokacin da ya kwashe baiyi ba wata nadama me kama da ta Rainin wayo ta soma sauko mishi Wai sai yaji bakin shi na furta kalmar istigifari Wai Allah ya tuba Amma hakan Bai Hana shi jiyo wata irin sukuwa a Rufin dakin shi ba kafin yaji iface iface suna sauka Akan Rufin dakin Wanda baya ko bukatar a sanar dashi Zubaina ce don muryar Mai Kama da kukan jaki ya tabbatar Zubaina ce tafe Wanda abinda tazo dashi din ne Kuma Yake tsoro har yayi nufin ficewa aguje daga gidan Amma me? Sai ji yayi anzargo kafafun shi ya hantsila kasa ya Kuma ci da kasa har Yana dauje hanci.

<< Hawaye 75Hawaye 77 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.