Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Ibtissam by Aysha Galadima

3:00 am nayi ko munti d’aya be gotaba aka bude kofar shirgin da aka kulle Abla, Zinariyya ce tashigo sai tangad’i take Ganin yanda Abla bata motsine yasa Zinariyya sanar da Uwar karuwai, umarni ta bada akawo mata ruwa masu sanyi a fridge guda biyar, hakan kuwa akayi cikin d’an karamun roba.

Zanariyya ta juye ruwan masu bala’in sanyi. Dakin shirgin suka nufa ita da Zinariyya sai wata da ake cewa Yar shila , a yadda zinariyya ta barta a haka sukazo suka sameta, kar’ban ruwan uwar karuwai tayi cikin rashin imani ta juyewa Abla shi a jikinta.

A gigice Abla ta farka tana Ambatan sunan Allah, gabaki d’aya jikinta rawa ya d’auka sabida wani irin sanyi da yake ratsa jikinta, kallanta uwar karuwai tayi a wulakance “ ku tashi ku fara aikin da kuka saba dan ba Hutu ne ya dace da kuba, matsiyata kawai”, tana kai karshen zancenta ta kalli ‘Yar shila  “ jeki taso mun ragowar tsinannun yaran, lokaci kankani na baku su kammala ayyukansu, idan ba haka ba ku zanesu suji a jikinsu.“

Tana kai karshen zancanta tayi waje , a duniya idan akwai wacce ‘yar shila ta tsana be wuce Abla ba , shiyasa uwar karuwai na fitowa taja ta kamar kayan wanki , Daidai lokacin da Zinariyya ta fito dasu Anee suma ko wannansu a jike sai rawar sanyi suke. Cikin kuka arwa ta karaso Inda Abla take.

”Abla sanyi nake ji , ga yunwa ina ji, ga bacci da be isar mu, jikina duk ciwo yake mun ga wasu cunnaku dasuka cijeni “, kwallarta Abla tayi saurin gogewa “ wata rana sai labari, kafun su dawo ku tashi muyi aikin mu ko zamu samu in lokacin sallah yayi muyi kafun musamu na abincin, kunsan idan bamu kammala ba, bazasu ta’ba bari muyi sallah ba” gyada mata kai sukayi gabaki d’ayansu, Babban falon da ya baci da kwalaben barasa da abubuwan sigari suka fara gyarawa , gabaki d’aya falon wari yake amma duk da haka sai da suka gyara shi tsaf sai faman haki suke sabida galabaitar da sukayi.

D’akuna biyar da suke jere a kasa ko wannansu ya nufi d’aya da niyar gyarawa, d’akin da Abla ta shiga wani irin amaine ya taso mata sabida kazantar da ta dunga cin karo dashi a dakin, gabaki d’aya d’akin a har gitse yake , da kyar ta Samu ta gyara d’akin kafun ta nufi toilet. Tana shiga aman da take rike wa ne ya kwace mata Sabida karo da ta dungaci dasu condom gawani uban Kazan tar dake cikin nan dakin, da kyar ta samu ta wanke ban dakin, tana fitowa sai da ta jira su Husna suka fito Suma, ko wannan su a waji gace sai faman toshe hanci suke, sama suka nufa shima saida suka gyara falon tass da ya fi na kasa baci kafin su gyara rooms din cikin falon, lokacin da suka gama wani irin juwace ta soma kamasu ga kiran sallah da ake faman yi amma badamar suje suyi.

Inda kwanukan wanke wanke suke suka nufa, sosai an ‘bata kwanuka haka suka zauna suka fara wankewa, sai wajan 8:30 na safe suka kammala wanke wanken, Dole su gyara kitchen din gidan ga tsakar wajan da zasu gyara shima , ga lokacin sallah na tafiya, murya a dusha she da ‘kyar take magana ta furta “ Lokacin sallah na tafiya , ya kamata muyi sallah “ a tsorace suka kalleta gabaki d’aya “ Abla kinsan hukuncin da zasuyi mana idan suka san munyi sallah ko”, manyan idanuwanta Abla ta saka musu.

”Kuna nufin mu zauna karmuyi sallah sabida hukunci?“ Da sauri duk suka d’aga mata kai kamun ilham tafurta “ sai muyi sallar daga baya danni tsoron muguntar su zinariya nake “same Arwa ma abunda ilham ta fada shi ta maimaita, Anee ce ta kalleta “ Abla Nima zanyi sallah , Taho muje “, kallan Husna Abla tayi ko zataje amma ko kallan inda Ablan take batayi ba.

A d’arare suka samu suka fita daga cikin gidan, saida sukai tafiya me Nisan gaske kafun su samu wani masallaci da suka ga butocin  ciki da ruwa, Alwala suka samu sukayi kafun Suje bayan masallacin su tayar da sallar su, suna idarwa tsoran hukuncin da za ayi musu ya kamasu. Cikin fargaba suka nufa gidan, tsallan kwado suka tarar ansaka ilham da arwa, fuskarsu gabaki d’aya ta baci da hawaye, yar shila tana ganin su Abla ta rufe su da duka da wata jungegiyar doruna, kafin suma akasu tsallan kwad’an, tun sunayi da karfin jikinsu har suka somayi a hankali kafun su fadi a kan tiles din suna nun farfashi, yar shila ta daga hannu zata kara zuba musu wani bulalan uwar karuwai ta fito cikin wankanta da kallo d’aya zaka mata kasan cikakkiyar karuwa ce.

“Ya isa haka yar shila so kike ki kashe mun kasuwa ne, ga kosai can ko wanne ki basa guda bakwai kafun ku basu wankin da aka had’a kunsan yau akwai casu, ko bara banaso suje yau sabida akwai aiki”tana kammala zancanta tasa kai ta bar gidan, kosan yar shila ta dakko amaimakon ta basu kamar yanda aka umarceta sai ta bawa ko wannansu biyar biyar, tana zuwa kan Abla ta Wulla mata guda uku ba kamar sauran ba, Husna ce kawai babu a cikin falon, ayun wace suka fara cin kosan da ko rabin cikinsu be zoba , banda abla da take bun kosan da kallo, tayi wa kanta alkawari bazata kara cin abinda ya fito ta kazamun hanya ba , shiyasa ta rabawa su arwa kowa daddai, harda murnarsu suka amsa kuwa kafun a tulo musu uban wanki me shegen yawa, basu suka kammala ba sai wajan 2:30, anan ma satar hanya ilham da Abla sukai sukaje sukai sallah suka dawo.

A wannan karan Allah ya temakesu ba aga dawowarsu ba, har lokacin su Arwa kuwa basuyi ko sallahr asuba ba duk yadda Abla take musu magana har ta gaji. Wata iriyar masifaffiyar yunwa suke ji , Ga uwar karuwai ta hana su zuwa baran da suke nemo abinci, La’asar nayi Abla takara guduwa wannan karan itama ilham bata bita ba. Tana idar da sallah ta ta’be jikin masallaci ko zata Samu sadaka amma har tagama bulayinta bata samu ko biyar ba , shiyasa ta nufi hanyar komawa gida abunta, tana shiga ta tarar da abunda ya tada mata hankali, da sauri ta karasa Wajan su tana tanbayarsu ina zasuje da wannan shigar, Anee na kuka ta soma magana “ Abla nagaji, bazan iya rayuwar yunwar nan ba, idan na kara awa d’aya banci abinci ba mutuwa zanyi , shiyasa na yadda da bukatar su Zinariyya, Sunce ba sex zasuyi damu ba, wasa ne kawai zasuyi, kuma zasu dunga biyan mu.”

A firgice Abla ta saka salati “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,me kuke kokarin yiwa rayuwar ku, bakusan hakan wata Babbar illace ba arayuwar ku, me zakucewa mahaliccin ku”, a kufule Husna ta kalleta“ Ya isheki haka IBTISSAM, ke komai kinfi kowa sani, ko ca’akai miki mu bamu da addinin ne, kullum mutum zai yi abu sai kin kawo naki, idan muka zauna da yunwa zaki bamu abincin da zamu dunga cine,ko zamu zauna kina hanamu abu yunwa ta kashe mu, na dad’e da fahimtar dama ba san cigaban mu kike ba, in baki sani ba ki sani yau bazan kara zama yunwa ta kashe niba, Nima dole na samu kudi, ga hanyar samun kud’i cikin sau’ki , idan ke bakya san rayuwar ki to mu muna so.“

Tana gama maganar ta taja dogon tsaki tayi wucewarta, Arwa da Anee ma bin bayanta sukai, ilham ce kadai ta Matso kusa da Abla “ kuncin rayuwar nan ta ishe mu Abla , Bamu da gatan da ya wuce mu samowa kan mu ‘yancin kai, bazan iya rayuwa cikin yunwa ba, duk da bamu dad’e da sanin juna sosai ba amma tabbas ke din Ablan muce me kaunar mu, kin nuna mana soyayya irin yanda yaya take nuna wa kannanta” itama tana kai karshen zancen ta tabi bayansu Husna , zubewa Abla tayi a kasa tana faman nanata sunayen Allah, babu abunda bakin ta yake furtawa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” wannan masifa har ina, batasan lokacin da wani kukan ba’kin ciki ya kwace mata ba.

United States

Zaune Adil yake cikin shigar kayan ball a ‘kayataccen filin ball da yake cikin gidan , ball d’in hannunsa yake ta faman bugawa shikadai, yana cikin bugawa Prince ya karaso inda yake cikin shigar kananan kaya masu shegen tsada, “yaya Prince “cewar Adil, shima Prince gira d’aya ya d’aga wa Adil yana zama gefen sa , cikin rad’a rad’a ya furta “Little Yaushe zamu je siyayyar da mukace zamuje kafun after your graduation?“

Kallansa little yayi kamar me tunani kafun ya furta “kasan ko mun tanbayi Big Boss zai ce mu lissafo ko me mike so, amma bazai barmu mufita ba “, gyada masa kai Prince yayi , kafun little ya cigaba “ yaya bobo ma bazai barmu ba , Indai ba wani muhummanci ne da abun ba , shima sai an had’a ka da sojoji sai kace wani ‘barawo”,lallausan gashin kansa Prince ya taba “ Little let’s go to uncle iron man, kasan yaya bobo yanajin maganarsa sosai, kawai yawon 2 hours zamuyi mu dawo.”

Mikewa sukai gabaki d’ayansu ba yan Adil ya ajje ball din hannunsa, cikin kayataccen babban falourn su suka nufa kafun su karya kwana Zuwa wata kofa, suna shiga nan ma wani kayataccen falo ne babba a wajan da taya tara kayan more rayuwa a cikinsa , falon ba karamun kyau yayi ba , cikin d’aya daga cikin kujerun falon suka tarar dashi yana karatun jarida , “Assalamu Alaikum “, suka hada baki wajan fada, d’an Dago da fuskarsa yayi kadan kafun ya amsa musu salamar tasu “ oh my boys sai yanxu ake ganin ku ko “, sosa ke ya suka fara yi kamar marasa gaskiya kafun Adil yayi saurin zama kusa dashi “ my iron man , you know I don’t have any one like you ko?“

Sakin baki Prince yayi a zuciyarsa kuwa yana auna irin ma yau darin yaro da za’a yi meshegen wayo, murmushi iron man ya saki “daga baya kenan , yanxu kana ganin big boss zaka nuna baka sanni ba”, dan karamun mursushi Adil ya saki “No uncle , you know kaima ina sanka , I don’t have any one like you guys “, girgiza masa kai uncle kawai yayi kafun ya kallesa shida Prince.

“Tunda naganku ku biyu akwai abunda kuke bukata, just ku fadamun ,if not ku tashi ku bani waje “, suna jin haka suka kalli junansu , kafun ko wannan su ya gyara zama , Prince ne ya soma magana “ uncle please munaso mu d’an fita yin siyayyane , and kasan yaya bobo bazai bari muje ba sai dai yace mu lissafo abinda mukeso “, sai da ya gama sauraransa tsaf bece musu komai ba , ya dakko wata telephone room, number 7 Kawai ya danna, kusan mintuna 2 , “ ina falona , am waiting for you “, yana fadar Hakan ya kashe kiran , ba Prince ba hatta Adil dake zaune kan kujera sai da ya sakko kasa kamar zaiyi kuka ya kalli uncle iron man.

“Yanxu uncle cin amanar mu zakayi , ai se kace mana baza muje ba , ni wallahi ban shirya yin tsallan kwado ba , “be karasa kalamansa ba yaji saukar muryar bobo “ you are very stupid”, a mugun tsorace Prince da Adil suka mike tsaye , kallan bobo da ke sanye cikin half wando da ya kai masa har gwiba black colour da wata white T-shirt da ya fito da murdaddun muscle dinsa waje, fuska a had’e ba fara’a ya karaso cikin falon, ko kallan inda suke be ‘karayi ba , sai sassauta face din shi da yayi kafun ya furta.

“Uncle gani”, shima uncle din nuna masa su Adil yayi da ko wannansu ya dukar dakansa kasa ,” they want to go out“ batare da bobo ya kallesu ba ya furta “ su lissafa abunda suke so, captain zai karbo musu” yana fadar hakan ya juya ya bar falon, hawaye ne suka fara sakkowa Adil , gabaki d’aya yaji besan zuwa shopping d’in , tsoran shi d’aya ma kar yaya bobo yayi fushi da su, kallansu uncle iron man yayi “ why the pity face kuma, kuje kuyi masa magana , zai barku “, cikin dan marairaice Prince ya furta “ uncle yanxu muna zuwa Wajan sa idan Bamuyi wasa ba sai mun fito da kunburarrun fuska”kallan baku daddara ba  Uncle ya bi Prince dashi , wato ya mayar da bobo boxer kenan , “uhm “ kawai yace tare da mayar da hankalinsa kan jaridarsa.

Jan hannun Prince , Adil yayi  har suka fito falo babu kowa a ciki sai sanyin Acn da yake busosu, direct inda zai sadasu da bangaran bobo suka nufa , suna isa Daidai part din ko wannansu ya ja burki kowa na kallan dan uwansa akan ya fara yin gama , cikin dan rad’a rad’a Prince ya rad’a wa Adil abu a kunne, gyada masa kansa yayi kafun suyi knocking , kusan tsawan 2 minutes ba a amsa ba , kara knocking din kofar Adil yayi nan ma shiru ba a amsa musu ba , kamar zai yi kuka Adil ya kallin Prince , shima Prince din kallan Adil yayi cikin fuskar tausayi ,”come in “, sukaji muryar bobo , babu Wanda bai saki a jiyar zuciya a cikin su ba , a hankali Adil ya tura kofar falon bobo, ko wanne bakinsu dauke da sallama , a hankali ya amsa musu ba tare da ya kallesu ba, gabaki dayan su shan Jinin jikinsu sukai.

Tsugunnawa sukai kasa kowannansu ya rike kunnuwansa “ we’re sorry yaya bobo “, cikin had’e rai yace “ get out “, Adil kamar zaiyi kuka ya kara cewa “ we’re sorry please “, a zafafe bobo ya daka musu tsawa “ I said get out “, ba Adil ba hatta Prince mikewa yayi da Sauri suka nufi hanyar barin part d’in, cikin dan sakin murya bobo ya furta “ come back”, cikin sanyin jiki ko wannan su ya koma inda yake a tsugunne, hannunsa bobo ya miko musu , da Sauri ko wannansu ya rike hannun kafun a hankali su kara furta “ kayi hakuri yaya bobo “, da ido ya kallesu kafun cikin dan sassauta murya ya soma magana “ where are your manners , haka aka koya muku magana “, girgiza masa kai sukayi “ speak “ cewar bobo , “ sorry sir”, Prince be kai karshe ba yaji saukar rankwashi akan sa , da sauri ya dafe wajan yana furta “ ouchhh yaya da zafi”, shima Adil yana cikin kumshe dariyarsa yaji saukar nasa rankwashin.

“Naga Alama harynxu baku horuba “ ya nuna Prince “ you bari yayanka ya dawo horon LTG zansa yayi maka “ and you , ya nuna Adil “ baruwana kai dashi”, sassaita muryarsa Adil yayi “ yaya bobo kasan Little dinka yana sanka , please karka fadawa yaya big boss ,munyi alkawari zamu zama Good Samaritan kaji best yayan mu “, sakin baki Prince yayi yana kallan Adil , cikin zuciyarsa yake furta.

“wai yarannan shi zasuyi wa bariki, Allah ya dawo da big boss hmmm “, ganin yanda yake kashe masa ido ne shima Prince ya kara da “ yes yaya bobon mu zamu zama Good Samaritan “ Sarai yasan halinsu sun fara saka masa ciwan kai shiyasa ya furta ,” go and get ready captain zai kaiku” kafun ya karasa yana jan kunnansu “ and if you guys misbehave, kunsan sauran.“

Kallan da gaske kake Adil ya bishi dashi, Prince kuwa da sauri yayi hugging dinsa gudur karya ce ya fasa “ thank you yayan mu, we love you so much “, shima Adil rungume bobon yayi “ thank you yaya “ kafun yace komai kamar wasu kananan yara suka bar falan a guje , goshinsa bobo ya shafa,“ you guys are not matured har yanxu.“

Tsadaddiyar wayarsa kiran Samsung new design ce ta dauki ringing din BIG BOSS ,kallan wayar bobo yayi da take langwashe gida hudu, Big Boss d’inne ya kara fitowa cikin wayar, cikin sallama ya kara wayar a kunnansa, duk da na cikin wayar baya ganinsa hakan be hanashi saramasa ba “ salute BIG BOSS”bansan me aka ce masa ba kusan 2 minutes kafun ya saki yar karamar dariya , cikin sakin fuska ya furta “ yanxu ni kake cewa Small child , don’t worry duk lokacin da kaji Ance maka na zama Daddyns son zaka san ni ba yaro bane.“

Be kai karshen maganar saba yaji kitt an kashe wayar, murmushi bobo ya saki kafun a hankali ya furta “ my big boss “

*****

Suna idar da sallar magreeb ko wannansu ya shirya cikin shigar kananan kaya, tun daga kan sumar kansu han zuwa ta kalmin kafarsu abun kallo ne sai suka fito sak larabawa musamman yadda gashin Kansu yake a murmurde gawani irin santsi da yake d’auka, babbar wayarsa ADEEL ya dauka ‘kirar iPhone 14 pro max yana matsowa kusa da Prince , “say cheeze “ atare suka kara kada baki wajan cewa “ cheeze “ kafun Adeel ya dauke su hoto, ba karamun kyau sukai cikin hotan ba, sai wani tsantsan kyau da ya kara yiwa hoton nasu armashi ko wannansu musamman yanda kalolin idanuwansu suka fito sosai.

Zai kara yi musu wani hoton Prince ya dakatar dashi.“ kasan yanxu yaya bobo zai iya canza shawara, ka ajje wannan hotan naka a gefe muna ‘bata lokaci” okay kawai Adil ya ce masa kafun su fito,lokacin bobo baya gida shiyasa Wajan uncle Dinsu kawai suka nufa sukai masa sallama , suna fito wa waje jerun motocin da zasu fita dasu ba’ka’ke sai faman kyalli da daukar ido suke , gabaki d’aya sojojin sanye suke cikin shigar suit ba’kake kowanansu a kwai bindiga a jikinsa, bakar bullet proof Armored Toyota Land Cruiser dake cikin Jerin motocin captain ya bud’e musu suka shiga kafun ya komawa driving seat , suma ragowar cikin motocin suka shiga cikin wani irin salon driving motocin nan suka soma tafiya a Jere akan babban titin New York .

Tafiyar 22 minutes sukai ya kawosu Babban shopping mall din Brookfield place ,’kayataccen shoppping mall me shegen kyau da tsada, tun daga wajan zaka gane ba karamun waje bane ga wasu matakan tsaro da aka saka ta ko ina a cikin mall din, ko ina ka waiga zaka ga wajan  tsit ba hayaniya musamman yanda fitulun Garin ya kara haska wajan kamar ba dare ba .suna shiga a Daidai parking space motocin sukai parking, kallan Tarin sojojin da suka fito daga cikin mota yayi kafun ya kalli captain “please captain mu kasu kashi hudu,” be kara zancan saba gabaki d’aya sojojin Suka raba kansu gida hudu , ko wannansu ya soma tafiya aka bar  captain tare dasu.

”Thank you “ Adil yace yana sakin masa murmushin sa da kullum baya ‘boyuwa , cikin wani side suka bi su uku da yafi ko ina shiru a cikin mall d’in, wani doguwar Elevator  suka hau kafun ya kai  su floor 11th dake can saman building din, idan mutum  ya sunkuyar da kansa tsaf yana ina hango abunda ake a kasansa , koda suka sauka akan lifter d’in sai da suka hau kan wani luxury escalator me kamar shape din circle.

Wari irin had’addan wajene ya bayyana a wajan me shegen kayatarwa , gabaki d’aya wajan shiru  kake ji babu hayaniyar komai sai daddadan kamshi da sanyin Ac da yake ratsa ko ina , babban wajan siyayya ne a wajan masu shegen tsad’a, kallansa Prince yayi “ Let’s have a little fun first (bari mu d’an ji dadi tukunna)”gyada masa kai Adil yayi , yanxu ma wani escalator din sukahau amaimakon yayi sama dasu sai suka hau barin da yake saukar dasu kasa, wata kofa suka nufe me girman gaske, anan ma wasu irin securities Suka gani tsatstsaye a Wajan , hannu d’aya  daga cikin security man din ya daga wa captain kafun gabaki d’aya ragowar su sara masa , wani dan button security din ya danna take a wajan kofar ta bude , babban wajan shakatawane na games me shegen girma , tundaga kan geometry dash ,getting over it with Bennett foddy, ninja gaiden ,sekiro:shadow die twice , da sauran games masu shegen dad’i cike a wajan mabanbanta, duk da yanda wajan ya cika da kayan games na manya , gabaki d’aya wajan baka jin hayaniyar komai sai d’an surutu kadan kadan da d’an ihu da yake fito wa , ba tare da damuwar komai ba su Adil suka fara kutsa kansu cikin babban wajan games d’in , kallan Prince Adil yayi.

“Yaya Prince let’s play Devil daggers please “, gyada masa kai Prince yayi , d’an tafiya kad’an sukai kafun suyi wata kwana yar kad’an , su na maso wajan inda game d’in da zasuyi yake suna kara jiyo sautin murya na kara tashi.

A Daidai inda game d’in da zasuyi suka tarar da wasu maza guda hudu, ko wannansu da wani irin shegen aski akansu da wasu manyan sar’ko’ki da suka rataya a jikinsu , daga gefen su kuma wasu karatan mazane guda uku ko wannansu fuskarsa ba fara’a , tsakanin Prince da Adil babu Wanda ya kalli inda suke har Suka ‘karasa inda captain yayi musu jagora har wajan da zasuyi playing games d’insu , d’aya daga cikin samarin nanne ya d’ura wani zagi cikin English language , kafun a kakkaice ya soma gama cikin yaran hausa da kallo idan ka kallesu bazaka taba cewa akwai mejin hausa ba sabida shigarsu, na gefensa ne ya d’auki kwalbar barasa yana kallan guy d’in da yayi magana “calm down Dizzy , kwantar da hankalinka , yanxu zamuyi maganin ‘yan iska ko wanane su dan ubansu, basusan ko su wanenen BAD BOYS ba da zasu takamana doka, ko basu san idan Bad boys suna zaune a waje ba a zama ba.”

A zuciye na ukunsu ya kalli d’aya daga cikin kartawan mazan nan yana nuna Adil “ je d’akko munshi yanxun nan”, na cikin hudun sune yayi kokarin dakatar dasu” no please kunsan game ne ya kawomu nan and nasan suma shine ya kawosu, let’s just enjoy and let them go, ku rabu dasu”, wani Wawan tsaki d’aya daga cikin guys d’in me suna Oskar yayi “ matsalata dakai sometimes ka fiya yawa , just wait and watch ka tsaya kayi kallo kawai”, ya karasa da yiwa d’aya daga cikin yaransu da su d’akko masu Adil, cikin cika umarni kuwa ya nufi inda suke, gabaki d’aya maganganun su akunnan Prince da yake sakin dariya shikad’ai azuxiyarsa.

“Wai a dakko musu Adil, zaku ci ubanku kuwa ,”yana cikin zancan zucinsa yaji wannan mutumin da aka aiko yayi sama da Adil, cikin fusata captain ya saka hannu zai dauko bindigarsa Prince ya damke masa hannu, da mamaki captain ya kallesa “ ka bari muga me zasuyi masa tukunna , karmu d’auki doka please “, captain zaiyi magana prince yayi saurin cewa it’s an order , mu bisu”, suna karasa wajan suka tarar da Adil zaune kan kujera gashin kansa ya kara kwantowa a kyakkyawar fuskarsa, gabaki d’ayansu binsu yayi da kallo d’aya bayan d’aya kafun cikin sakin murmushi ya furta “ if you don’t have anything to say am busy ( idan baku da wani abun fada, ni bani da lokaci”, Wanda aka kira da Oskar ne ya mike a yayyake yana shirin yiwa Adil masifa shima Adil din ya kallesa har yanxu da murmushi akan fuskarsa ,

“kana haukane? “, Little ,Prince ya kira sunansa tare da karaso wa inda yake “ let’s go bamu da time “ cikin jin zafinsu Dizzy yayi yunkurin taba rigar Prince, take a wajan Prince ya kwashesa da mari,” kanashan kwayane, ni zaka rike , or are you insane?” gabaki d’aya Prince ya Jera masa tanbayoyin , mutuwar tsaye su Oskar sukai suna bin Prince da yayi gangancin marin, a zuciye dizzy ya daga hannu zai mari Prince yaji an lankwasa hannun ya bada sautin’kass, cikin karar azaba Dizzy ya kalli Wanda yayi wasa wannan aikin , bakowa bane face captain da yake tsaye kam fuskarsa ba fara’a , d’aya daga cikin samarin ne mesu na EMESSI ne ya kalli yaransu.

“Ku karya munsu yanxun nan ku kawo mun su, shima be karasa zan cansaba yaji saukar mari akan fuskar sa , da karfi ya furta “Innalillahi “ Sabida yanda yaji saukar marin a kan fuskarsa, kara kallan Little Prince yayi “ let’s go” mikewa Adil yayi a zuciya Oskar da aka mara ya tunkude Adil yayi baya baya zai fadi, cikin wani zafin nawa Prince da captain suka tare sa Daidai lokacin da sauran sojojin su suka karaso, a zuciye suka nufi inda su oskar suke, basuyi aunewa kawai sukaji saukar duka ta ko ina a jikinsu hatta yaransu da suke tare da su, dakatar dasu captain yayi kafun ya karaso inda suke , gabaki d’aya an kunbura musu face, ko wannansu ya dukar da kansa katsa sabida wani azabar buguwa da Sukai, ko wannansu da kyar yake iya maida nunfashi, kallan yanda suke zazzaro idanuwa captain yayi “ ku yan iska ko, baku da mutunci yau zakuga yadda za a koya muku tarbiyya.“

Ba shiri guy din dazu yayi saurin riko kafar captain “ we’re very sorry sir”kafun captain yayi magana Prince yayi saurin yin magana “zakuga sorry lokacin da aka ce kuyi wa kaza aski, ku yan iska , iskancinku har nan ko”murmushi Adil ya saki” no yaya Prince , kamar idan sun bada hakuri its okay”. Cikin wani dan iskan murmushi Prince ya kalli dizzy da har yanxu kansa yake a sunkuye sai faman sakin nishi yake , “ku Bashi hakuri”, gabaki d’aya kuwa hada baki sukai wajan cewa sorry bansa Dizzy da yake a zuciye, nuna msu kofa Prince yayi kafin ya kalli captain ,”wannan shine marakunyar , he can’t even apologize, kawai ku sashi a boot akaiwa simba shi”cikin murmushin da Adil ya furta “kasan lion din Big boss bashi da hakuri fa”, be karasa zancansaba a rude su dizzy suka dago tare da hada baki wajan furta “BIG BOSS?

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun “ gabaki d’ayansu zuface ta fara sakko musu duk da sanyin Acn da ke wajan, basusan ko wanene ba amma sun ‘ta’ba jin labarin yadda yasaka ogansu yiwa dan buri tsarki sannan yasa akayi masa kwalkwal, kamar zasuyi kuka suka fara bawa Adil hakuri hatta dizzy da yafi kowa rudewa, Prince shi abun dariya ma ya bashi Ganin yadda suka rude lokaci guda, shikam Adil murmushi ya sakar musu.

“You can go”, ai bashiri suka arta a guje hatta takalminsa d’aya sai da oskar ya manta, ana kiransa yazo ya d’auka amma ko juyowa bayi ba.”yaya Prince ka tsorata sufa “cewar Adil , gashin kansa kadan Prince ya kama” Sabida ina cikin good mood ne amma da a boot za a sasu akai wa yaya bobo bankararrun Kaji “kallansa Adil yayi be san lokacin da ya furta.

“Yaya sometimes fa kai mugune wasa wasa “yar karamar dariya Prince ya saki “ zanyi maganinka idan mun koma , yanxu time d’inmu ya tafi a kan wayancan shashashan, let’s play kafun muga yaya bobo a nan wajan.” Hakance kuwa ta faru game d’in Devil dragger sukayi kafun su ‘kara yin wani game d’in ganin babu lokaci ne yasa suka fito dga wajan game d’in, ta escalator Suka sauka , Daidai wajan siyayyar kaya Adil ya hango wata P_cap blue colour , nuna wa Prince yayi suka ‘karasa wajan, 5 p_caps Adil yadauka, Green, blue, red, black, white sai abubuwan ci da suka iya kusan Leda Hudu kafun su bar Brookfield palace.

11 saura suka shigo ciki gida , masu tsaran da suka gani daban ne ya tabbatar musu da dawowar Bobo, hakanne kuwa dan suka shigowa main gate suka tarar dashi a tsaye ya dukar da kai, yana ganin shigowarsu ya juya cikin takun manyan sojoji ya nufi part d’insa, suma suna fitowa 2 leda din kayan ciye ciyen da suka ibo suka bawa su captain na su, kafun suma su shiga cikin main falour, bakowa a wajan sai james dake tsaye bakin dinning, shaf shaf suka ci abincin su kafun su mikawa James kayan da suka siyo suma suka nufi dakinsu. Gabaki d’aya wanka Sukai kafun su bi ayarin gado.

2:30am aka turo kofar dakin nasu, shima sanye yake cikin kayan bacci coffee colour masu shegen taushi,wayarshi dake kare a kunnansa ya haska ,Daidai inda Little yake , kafin ya saita Daidai in Prince yake akwance shima ,cikin wani daddadan cool voice kamar ba asan yin magana aka furta “ okay, Take care “, kai Bobo ya dan jinjina duk da na cikin wayar baya ganinsa kafun ya kashe call d’in gabaki d’aya , kan gadon Little ya karasa kafun ya shafa kyakkyawar Sumarsa dara dan ruke masa fuska, addua ya tottofa masa kafun ya koma kan Prince shima , sai da ya tabbatar they’re safe kafun ya kashe musu fitular dakin ya barmusu dumm light me kamar light green. Akofar dakin suka ci karo da uncle Dinsu yana kokarin shiga dakin shima, ganin bobo ya fitone yasa ya fasa shiga,cikin kulawa uncle din ya kallesa “ kaima kaje ka huta, har yanxu baka kwanta ba.“

Kama hannunsa bobo yayi suka nufi part din uncle din, shima sai da ya kwantar dashi akan gado kafun ya furta “Good night uncle “, cikin kuwa uncle ya shafa kansa “Allah ya tashemu lapiya ya albarkace ku yarana “, a zuciya bobo ya amsa da Ameen kafun ya kashewa uncle din su light shima. Still be kwanta ba sai da ya tabbatar da lapiyan gidan dukda tsaran dake cikin gidan kafun shima ya nufi part d’insa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ibtissam 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×