Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Kalaman Soyayya by Xayyeesharthul-Humaerath

Ina ji a jikina cewa duk ranar da na daina sonka to numfashina ne ya zo karshe.

Ka sani ka kara sani, in har zan yi numfashi to sonka na cikin raina ko ince rayuwata ma gabadaya.

Indai ana so bayan rai, tabbas zan ci gaba da sonka har bayan raina.

Shin ko ka san mahimmacin murmishinka gareni kuwa? Tamkar yiwa makaho addu’ar budewar ido ne.

Ban ce ni kadai za ka so ba, amman ina da tabbacin zan yi kokarin cike duk wani gurbi da ke zuciyarka ta hanyar da ba za ka taba so ko tunanin kulla alaka da wata ‘ya mace ba.

Ina son ka tamkar raina!

Burina ko bayan bana duniya, ina fatan ka so ni misalin son da nake maka.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×