Tafi-tafiya, rayuwa tana ta juyawa. Ta mayar da hankalinta kan karatunta. Babu abinda tafi muradi a lokacin, kamar taga cewa ta kammala karatunta. Idan ta gama ne ta karbi takardun shaidar kammala karatunta, akwai wasu kadarorinta da a lokacin tasan Hajiya Hadiza zata damka mata su. Ba zata kara bukatar komi ba, zata tattara ta bar musu gidan da rayuwarsu.
Zata ninkaya a cikin duniya, koda kuwa zata je har bangon duniyar ne domin ta nemo mahaifiyarta ta koma wajenta da zama.
Tasan wadannan kadarorin da kudaden dake kulle a cikin bankinta, zasu ishesu su rayu ita da mahaifiyarta. . .
Kauthar shiru Allah yasa lfy
Amma naji rasuwar Anty Ummy sosai wallahi kuma na tausayawa Kauthar da AbdulMalik. Lallai su kadai suka dace da juna
Jeeddah don Allah muna jira, shiru kake ji Allah dai Yasa lafiya #tagumi+zamanjira
Thank you dear
To… Yadda wannan aure dae zai kaya, sai yadda jidda tace lol
gaskiya yahadu littafin