Zaid ya yi murmushi ya na aje mug ɗin hannunsa a kan wata chest drawer, sannan ya tsaya yana kallon kansa ta cikin mirrors ɗin dake zagaye da gym ɗin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana wani jujjuyawa. Kafin ya ɗaga hannayensa ya na auna girman muscle ɗinsa. Duk abun da yake Rabi na leƙensa ta ƙasan ƙafafunta.
Kamar da aka ce ya kalleta ta cikin mirrorn, karaf suka haɗa ido, da sauri Rabi ta waske ta ci gaba da cat cow pose ɗinta. Zaid ya kuma yin wani murmushin yana kama rigarsa ta ƙasa, sannan a. . .