You ware using your ear to hear, and i am using my heart…
No.181, Guzape, Abuja…
10:11pm
KULIYA POV.
I lost my way, somewhere in another galaxy
Too much to take, these memories end in tragedy
And all of these pleces , all of these faces, I didn’t wanna let you down
And all these mistakes of mine I can’t replace it, i gotta move on somehow…
Waƙar dake tashi kenan a falon gidan. Daga can ɓangaren da kujerun gidan kuma suke, Kuliya ne durƙushe a gaban Mishal, wadda ke zaune a kan kujera, ya kama ƙafarta ta dama yabna saka mata safa, saboda sanyin da ake a gari.
Safar ya gama saka mata, sannan ya kai hannunsa ya janyo hular sanyita dake gefen kujera, ya miƙe tsaye yana saka mata a kanta. Binsa kawai take da kallo, tana shawara da zuciyarta, kan ta yadda za ta ɓullo masa da maganar da suka yi da Adawiyya a yau. Zama ya yi a gafenta ya na cewa.
“Shikenan?”
Kanta ta gyaɗa masa tana gyara zamanta. Kallon da suke suka ci gaba da yi, kafin Kuliyan ya miƙe ya shiga kitchen ya aje plates ɗin da suka ci abinci. Har ya kamo hanya zai fito, sai kuma ya fasa ya koma dan ɗaukar ruwa.
Babban kuskuren da ya tafka kenan a ranar. Dan a sa’ilin da ya rufe murfin fridge ɗin, asa’ilin wani ɗan ƙarami, kuma mulmullallen ƙarfe, ya fito daga cikin bindigar da aka harba da ƙarfin tsiya, kuma bai tashi sauƙa a ko ina ba, sai a damtsen Kuliya na dama.
Wani irin shiga harbin ya masa, hakan ya sa shi sakin gorar ruwan dake hannunsa da sauri, sannan ya yi luuu zuwa baya ya na shirin faɗu, cikin dauriya da zafin nama ya kai hannunsa ya dafa island. Da ƙyar ya tsaya a kan ƙafafunsa ya na layi. Wani irin zugin azaba hannun nasa yake masa, hakan ya sa ya kalli hannun, bai tabbatar da abun da yake gani ba, sai da ya kai hannunsa ya kawar da ɗan guntun hannun T-shirt ɗin jikinsa, ya ga ramin da harbin da aka masa ya yi.
Ji ya yi jini na ɗibansa, tunawa da ya yi da Mishal dake falo ya sa shi cije leɓensa na ƙasa. Ya kai hannunsa na hagu ya riƙe damtsen nasa dake ta zubar jini, da ƙyar ya ja ƙafarsa zuwa falon, dan ya san ko ma su waye suka zo gidan dan shi suka zo, kuma idan aka jima kaɗan za su iya shigowa cikin gidan, wata ƙila su cutar masa da ita.
“Ab… Abu… Abu Aswad… La… lafiya…”
Mishal ta faɗi tana miƙewa tsayi, ganinsa cikin wani hali ba ƙaramin ruɗata ya yi ba, kamar an kunna famfo, haka hawaye ya shiga mata zuba, da sauri ta nufi inda yake tana kiran sunansa, duk ta birkice, ta rasa abin yi.
“Zo… Zo mu je ka zauna!”
Ta faɗi tana jan hannunsa na hagu dake kan damtsensa na dama. Da sauri ya riƙe nata hannun ya na girgiza mata kai cike da dauri, leɓensa ya ƙara datsewa. A sanda ya fara jan hannunta zuwa ɗakinsa. Kamar raƙumi da akala haka ta riƙa binsa har zuwa ɗakin nasa, duk kuwa da shi ɗin ba ya tafiya da kyau, ta lura ma da layi yake.
Wani abu da ya bata mamaki shi ne, ganin ya nufi closet ɗinsa da ita. Mamaki bai gama cinyeta ba har sai sanda ta ga ya danna wani switch da duk shigowarta wurin ba ta taɓa lura da shi ba. Ba tare da ɓata lokaci ba, lokar kayan dake wurin ta zuge zuwa gefe sannan ƙofa ta bayyana a gabansu. Hannunsa na hagu wanda ya yi kaca-kaca da jini ya kai ya tura ƙofar ta yi baya, sannan ya tura Mishal ɗin ciki, shi ma ya shiga. Ya na shiga ya rufo ƙofar, ya danna wani switch dake kusa da ƙofar, nan take lokar nan da ta yi gefe ta koma mazauninta na ainahi, kamar ma ba’a taɓa motsa ta ba.
Mishal ta ci gaba da bin wurin da kallo, ganin cewar ɗaki ne, har da gado a ciki, ga kuma wani work table dake ɗauke da computers da kuma tardu. Duk da tana cikin halin ruɗu, bai hanata jin mamaki na jan ƙafarta zuwa ƙasa ba, to shi wannan ɗakin ta wani ɓangare yake a gidan?, dan ita ko da wasa ba ta taɓa sanin cewa akwai wasu ɗakuna bayan waɗanan ukun da ta sani a gidan ba.
Jin abu ya faɗi yaraf a bayanta ya sa da sauri ta waigo. Idonta ya sauƙa a kan Kuliya dake yashe a ƙasa, hannunsa na hagu dafe da damtsensa na dama, wanda yake ta ɓuɓullar da jini.
Da gudu ta isa kansa tana kiran sunansa, a hankali ta kama kansa tana shirin zaunar da shi. Da ɗan sauran kuzarin da ya rage masa ya miƙe zaunen ya na jingina da bango. Mishal sai duba jikinsa take, kamar wadda aka cewa akwai wani switch da za ta danna a jikin nasa, wanda zai hana zubar jinin da yake. Gaba ɗaya ya haɗa gumi sharkaf, kasancewar babu wata isashiyyar iska a ɗakin, dan ita ba ta ga windo ko wata ƙofa bayan wadda suka shigo ba. Hular kanta ta cire ta na faɗin.
“Tsaya na saka maka wannan a wurin, may be zai hana jinin zuba”
Da ƙyar Kuliya ya iya sauƙe hannunsa na hagu daga kan raunin, sannan cikin sauri Mishal ta cikukuye hukarta pink color tana danawwa a wurin. Jin ya yi wani irin nishi ne ya sa ta fashe da kuka me sauti tana kallon fuskarsa, idanuwansa har sama suke, alamun dai ya na gaf da rufesu gaba ɗaya.
“Na shiga uku ni Hafsat, Abu Aswad kar ka mutu, dan Allah kar ka mutu ka barni, Abu Aswad ka min alƙawarin kasancewa tare da ni fa, kuma na san Anna ta faɗa maka cewar karya alƙawari ba kyau, kar ka karya alƙawari, Abu Aswad ka kasance tare da ni, Abu Aswad ɗina dan Allah!…”
Sambatu take tana ƙarawa, ita kanta ba ta jin ma tana cikin hayyacinta, hular kanta da ta cire ce tasa gashin kanta barbajewa a bayanta, ta koma kamarwata wadda sanyi ya taɓawa ƙwaƙwalwa.
“Kana ji ko?!”
Ta tambaya tana mammarin gefen fuskarsa, idonsa da ya lumshe ya buɗe a kanta.
“Kar ka mutu baka haɗu da Zaid ba!…”
Kuliya ya ja wani kalar numfashi yana buɗe idonsa da ƙyar, cikin wani irin sauti yace.
“A… Ina… Ki… Ki ka san… Za… Zaid?”
Ba dan babu sautin komai a ɗakin ba, da balalle ta ji abun da yake faɗi ba.
“Yau Anti Adawiyya ta zo makaranta ta same ni, shi ne take faɗamin cewar Zaid ne mijinta, kuma… Kuma da ma ina ganinsa a layin makaranta”
Kansa ya kawar gefe yana ƙoƙarin ƙwato numfashinsa da ya nufi wata duniyar.
“Zaid ya gudu… Gu… Guduwa aka ce ya y… yi”
Da sauri Mishal ta share hawayenta, hakan ya sa gefen fuskarta ɓaci da jinsa. Ta gyara zama ta shiga ba shi labarin da ta sani a kan Zaid ɗin. Duk kuwa da ba ta da tabbacin yana fahimta. Sai de kuma yana fahimtar, dan babu abu ɗaya da ta faɗa wanda bai samu mukkulin kansa ya buɗe ƙofa ya shiga ba, ya ji komai, kuma ya haddace komai. Kallonta yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa gaba ɗaya.
“Hafsat! Ballale… Na… Na kai gobe ba… Amma idan… Idan kin haɗu… Haɗu da Zaid, ki ce… Ki ce masa ina kewarsa… Sa… Sannan… Sannan kuma ba duk tswon wannan lokacin, ban manta da shi ba… Ki kuma faɗa masa cewar… Cewar ke matata ce, ya kula min dake!”
Mishal ta ƙarawa kukanta sauti tana kamo hannunsa.
“Aliyu Dan Allah ka dena faɗin haka… Na rantse za ka rayu, Allah na tare da mu… Yanzu Aliyu idan ka mutu ina zan sa kain?… Aliyu ba ni fa da kowa sai kai. Kai ne kawai ka rage min, dan Allah kai ma ka zauna, kar ka mutu ka barni kamar Babana da Mamana da kuma yayana, a ƙalla de ya kamata ace na samu ko da mutum ɗaya ne a cikinku!”
Tausayinta ya ƙara kama raunanniyar zuciyar Kuliya, hakan ya sa shi ɗagowa da hannunsa na hagu dake ɓace da jini, ya kama gefen fuskarta, hannun nasa gaba ɗaya karkarwa yake, hawaye na fita daga idonsa, wanda ya haɗe da zufar da yake.
Matsowa ya yi da fuskarta dab da tasa, har tana iya jiyo yanda numfashisa ke fita a gurɓace, saboda hancinta da ya kara da nasa, hakan ya sa Mishal lumshe ido tana buɗe wani sabon babin na kuka.
“Idan na mutu kar ki yi kuka, na san ma Zaid ba zai bari ki yi kukan ba, amma zan yi kewarki, Allah ya haɗani da ke a aljanna!…”
Da sauri Mishal ta kai hannayenta kan fuskarsa tana girgiza masa kai.
“Dan Allah kar ka tafi… Allah ina sonka… Wallahi ina sonka”
Cikin wani irin ƙarfin hali ya mata murmushi. Da gaske yake faɗa mata cewar ba ya jin zai iya kaiwa safiyar gobe, ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa da ita, haka kuma ba ya jin zai ƙara buɗar idonsa ya ganta kusa da shi. Wasiyya ce yake bata, dan wata ƙila bai sani ba, ko wanna ne kaɗai lokacin da Allah ya ara masa dan ya yi magana da ita ta ƙarshe.
“Silly girl… Ki me… Me da hankali kan karatunki, ki zama yarinyar kirki, idan kuma Allah ya sa akwai rabo tsakanina da ke, Allah ya raya mana shi, dan ina zaton kamar na baki baby shekaran jiya, ki kula da shi pleace”
Duk da halin da yake ciki sai da ya bawa Mishal haushi, ana ga yaƙi shi ya na ga ƙura, ɗan ƙaramin mari ta masa a kuncinsa, hakan ya sa ya buɗe idonsa da ya lumshe.
“I love you Teddy Bear… Mishallyn Aliyu…!”
Da sauri ta haɗe bakinta da nasa ta shiga kissing. Kafin a hankali ta saki bakinsa tan kallon idonsa.
“I love youuuuu too Abu Aswad!”
Murmushi ya mata, yana ɗaga hannunsa ya shafa kanta. Nan take kuma jikinsa ya saki, hannun nasa ya dawo ƙasa yaraf, fuskarsa dake hannunta ta ƙara nauyi, idonsa ya rufe ruf.
Daga can wajen gidan kuma, bayan da ‘yan ta’addan da suka zo ɗaukar fansa suka gama dube-dubensu a cikin gidan ba su ga kowa ba, sai suka yanke shawarar kiran ogansu dan su sanar masa da su fa basu ga kowa ba. Ogan yace su bar gidan kawai tun da har sun ce sun harbe shi, ko haka ma suka barshi ai shikenan, sun ɗau fansar abin da ya musu, na kama babban ogansu da ya yi.
ZAID POV.
Da misalin ƙarfe 12:40am, ya fice daga gidansa, yayin da ya bar Rabi kwance tana bacci, shi ba zai iya jira har zuwa gobe da safe ba, dan tun bayan da ta kawo masa maganar Aliyu na raye ya shiga mata tambayoyi a kan Aliyun. Amma sai ta ce masa ita ba ta san komai a kansa ba bayan inkiyarsa, wato Kuliya, sannan kuma ta san cewa ma’aikacin DSS ne. Yanzu haka tafiyar da yake a motar, tunani, ruɗani, jimami da mamaki su ne suka cika kansa taf. Ya rasa ma wani kalar yanayi yake ciki, amma idan ya duba wani ɓangaren sai ya ga cewar kamar mamakin da yake ciki ya fi yawa. Dan ya na mamaki mutuƙa, na yanda Aliyun ya iya tserewa wutar da ta kama a gidan marayu, sai kuma mamakin sanin cewa shi ma SS ne, su na aiki a hukuma ɗaya, amma ba su san juna ba. Sai kuma wani murmushi ya suɓuce masa, tunawa da ya yi da alƙawarin da suke yawan ɗaukawa juna, na idan sun girma aikin SS shi ne za su yi. Wato bai manta ba kenan, tun da ga shi ya cika alƙawari.
Hannunsa ya kai ya ɗauki wayarsa, a sanda yake faka motar a gefen hanya. Cikin jerin gwanon lambobin dake wayarsa, ya nemo ta RAM, tare da aika masa kira. Kusan ringing uku ta yi ba tare da an ɗaga ba, har ransa ya soma ɓaci, dan ya san halin RAM ɗin, shi a rayuwarsa sam bai iya zama da waya ba, wayat ma sam ba ta gabansa, mutumin da sai ya yi sati ba tare da ya san inda wayar tasa take ba.
Sai a kira na biyar sannan ya ɗaga. Cikin magagin bacci ya soma gaida Zaid ɗin, ya amsashi a dake.
“Ina san ka buɗe bayanan ma’aikatan hukumarmu, ka duba min wani wai shi ALIYU ZAID, inkiyarsa KULIYA!”
Umarnin ya biyo baya. Daga ɗayan ɓangaren Ram ya miƙe tsaye daga kan gadonsa yana fita daga ɗakinsa, gudun kada ya tashi matarsa a bacci, ya koma falo ya zauna, har zuwa lokacin wayar na kare a kunnensa. Sai da ya murza idonsa kusan sau biyu, kafin ya sosa wuyansa, dai-dai kan wani tatto dake rubuce a wuyan nasa.
“Sir a yanzu ba zai iyu na duba bayanan ba, sai de na datsi na’urar, amma ni zan iya baka amsa!”
Daga ɗayan ɓangaren Zaid ya gyara zamansa ya na ɗaga kafaɗa.
“Umhumm, Ina jinka”
Ram ya ɗauko numfashi, sannan ya dire, dan kuwa ya san abun da zai aikata a yanzun, saɓawa ƙa’idar aikinsa ne, ba’a yarda su bawa juna sirrin wasu jami’an ba, amma kuma dole ne ya yi hakan, dan yana da tabbacin temako ne zai yi.
“Tun shekaru biyar baya na fara aiki da kai Sir, haka ne?”
Zaid ya gyaɗa kansa, a idonsa yake hango haɗuwarsu ta farko da Ram ɗin.
“Haka ne”
Ya faɗi cikin tabbatarwa.
“Bayan shekara uku da fara aiki da kai, sai aka haɗani aiki da wani me kamarka, dan kuwa ba zan kirashi da kai kai tsaye ba, saboda akwai wasu banbaci biyu tare da ku. Wannan banbanci shi ne yasa na gane cewa, ku mutane biyu ne mabanbanta. Shi wannan wanda aka haɗani aikin da shi, sunansa ALIYU ZAID BICHI, inkiyarsa KULIYA. Confusing ɗin da kuka saka ni a ciki ya sa na fara bincike a kan rayuwar ko wannenku ba tare da sanin kowa ba. Kuma cikin ikon Allah sai na gano komai a kanku, sai de kuma na gano cewar ba ku san da zaman juna ba, kai kana zargin cewa Aliyu ya mutu, shi kuma an sanar da shi cewar ka gudu. A lokacin sai na samu Sir Andi, na masa bayanin abun da na gano, shi ne ya gargaɗeni da kada na kuskura na ɗaga zancen, na barku a haka, domin kuwa sanin junanku zai iya haifarwa da ɗaya daga cikinki matsala a aikinku. Sai na yarda da abun da ya faɗi, hakan tasa na yi shiru da bakina. Amma tun da har ka tambayeni a yau, na ji cewar ba zan iya ɓoye maka ba!”
Shuuuuuu! Wata iska ta shiga wucewa ta gefen kunnen Zaid da ba wayar, hannunsa na hagu dunƙuke a kan bakinsa. Wai shi kam meke damunsa ne yau?. Ji yake kamar duk abun da yake faruwa a mafarki ne, kamar idan wani ya zungureshi zai farka ya ga cewar ba gaskiya ba ne. Ashe kenan duk tsawon wannan shekarun Aliyunsa na raye?. Miyau ya haɗiye da ƙyar, yana laluben muryasa a maƙogwaransa.
“Ina ne address ɗin gidansa?”
Da gudu motar Zaid ta shigo layin gidan Aliyu, Allah-Allah yake ya isa gidan, dan zuciyarsa na faɗa masa kamar biyuninsa baya cikin ƙoshin lafiya. A dai-dai ƙofar gidan da Ram ya faɗa masa ya yi parking, bai ko kashe motar ba, ya fito da gudu ya shiga cikin gidan, da megadin y fara cinkaro, yashe a ƙasa,, hakan ya sa hankalinsa ninkuwa wurin tashi. Zuciyarsa ko kamar za ta fashe dan tsabar bugun da take da ƙarfi.
Cikin gidan ya kutsa, ya shuga dube-dube, amma be ga kowa a falo ba, ya shiga kitchen, babu kowa, ya fito ya nufi corridor ɗin dake ƙunshe da ɗakunan gidan, haka ya yi ta shiga ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, kafin ya samu nasarar gano ɗakin Kuliyan a cikin ɗakunan uku.
Ya bincika ko ina be ga kowa ba, kuma tun da ya ga me gadin gidan a sume, ya fuskanci cewar hari aka kawo musu, imma de sun tafi da su, shi da matarsa, ko kuma suna ɓoye a wani ɓangare na gidan. Tun da de har aka faɗa masa cewar Aliyun SS ne, to tabbas akwai maɓoya a cikin gidan, dan su ba sa zama haka kawai, hatta shi kansa akwai maɓoya a gidansa. To amma a ina ta gidan Aliyun take?.
Ya tambayi kansa, sa’ilin da yake dudduba ɗakin, wai ko Allah zaisa ya samu wata makama, amma haka ya hargutsa ɗakin, ba tare da ya samo komai ba. Har ya fara karaya, sai kuma idonsa ya sauƙa a kan ƙofar toilet, dan haka ya shiga ya dudduba nan ɗin ma. Amma bai samu komai ba, ya fito yana jin ƙirjinsa ya masa nauyi, kamar da aka ɗora masa wani gingimemen dutse a kan zuciyarsa, kamar da aka sa igiya aka ɗaure masa magudanar nunfashinsa haka yake ji, kansa ya masa nauyi, dan tarin abubuwan dak ciki za su iya sakawa ya tarwatse ma.