Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Lailerh Mansoor by Maimoona Abdallah

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

This book is solely for my biggest supporter, my overall, my sisi from another mom, halak malak, Maman biyu na, Khadeeja nerh! I love you and I cherish you a lot – one love dear one love.

I dedicate this page to my sweetheart, favourite sis Hauwa’u (Walida), masoyiya, Ya Allah ya mi ki albarka Ya baki Muhammad.

*****

Kaduna, Nigeria

Madaidaicin tsakar gida ne dake d’auke da rijiya daga gefe, sai kitchen Dake rufe daga can hannun dama, daga gefen kitchen d’in akwai d’an dakali da aka zagaye da plaster inda ya kasance gurin wanke-wanke da few plates da pots a wajen wad’anda ba’a wanke ba, sai bayan gida Dake rufe Shima daga hannun hagu, d’an k’aramin falo ne da d’akuna guda biyu falle d’addaya a cikin k’ofa d’aya Dake tsakar gid’an, gidan fes- fes Babu alamar datti ko d’igo.

Wata kyakkyawar macece ta fito daga d’aya daga cikin d’akuna guda biyun, matar doguwa ce dirarriya sosai Mai hasken fata, irin hasken y’an Ethiopia d’innan, a k’alla zatayi shekara 33 zuwa 35 haka, tana Sanye da Riga da zani da ya yi wa fatarta kyau sosai duk da ba wani Mai nauyin kud’i bane, bak’in hijabin jikinta ta gyarawa zama tana k’arasowa falon, ta Sami guri kan d’aya daga cikin kujeru uku da ke gyararren falon Dake k’amshin turaren wuta, cas’bah d’in hannunta ta ajiye akan hannun kujeran tare da mik’e kafafunta, masu d’auke da dogayen yatsunta masu kyau, tana tunanin shin ina Lailerh? It’s already 6:00pm tasan duk inda take tana hanyar gida, tun k’arfe 5:30 ya kamata ta iso gida, wayar ta dake kan kujerar ta janyo da niyyar kiran layinta, sallamar da taji daga tsakar gida yasa ta sauk’e ajiyar zuciya tare da ajiye wayar a hannun kujera tana amsa sallamar tare da kallon k’ofar falon da kyakkyawar murmushi a kan fuskarta, yaye labulen falon aka yi ta shigo d’auke da wata sallamar kyakkyawar fuskarta a had’e.

Babu yabo babu fallasa, k’ura mata ido ammi ta yi ganin yadda take takowa a sanyaye kamar wadda k’wai ya fashe wa a ciki, dogon hijab maroon colour ne a jikinta da ya rufe har k’afafunta, socks d’in dake k’afafunta kad’ai ake iya hangowa, hannayenta duka suna cikin hijab d’in, sai Kuma kyakkyawar fuskarta Dake d’auke da dara-daran idanunta da suka d’an canja launi saboda gajiya, sosai take kama da Ammi tsayin, dirarren jikin, kyawawan idanuwan da suke Nan farare tass, k’wayar idon Kuma bak’i sid’ik. ga gashin gira bak’i cikakke da ya ƙarawa fuskar k’awa, d’an k’aramin Baki kamar cokali bazai shiga ba gashi nan pink yirr dashi, da dogon hanci daya dace da zagayayyiyar fuskarta, duk irin na Amminta, zuba mata ido Ammi tayi tana kallonta, komai nata Lailerh ta d’auko yatsun k’afafunta da na hannunta sune kad’ai irin na mahaifinta Wanda suna cikin abinda suka Fi birgeta a wajen Mansoor d’in, har ta k’araso ta zauna tana kallon Ammin tare da kwab’e fuska ganin Ammin tayi nisa a tunani, kwanciya tayi akan cinyarta tare da mik’ar da k’afafunta a kan hannun three seater d’in da Ammi ke Kai tana fad’in “washhh! Ammi na gaji wayyo Allahna, k’afafuna jinsu nake kamar ba nawa ba” sai a lokacin Ammi ta dubi kanta Dake kan cinyar ta, tire kan tayi daga k’afafunta tana fad’in “nikam d’agani wa ya aike ki trekking tun daga shagon naku?

Ai nasan tun da naga kin Kai 6:00 nasan da k’afa kika dawo, ki tashi ki cire hijab d’in da socks ki je kiyi wanka kizo kici abinci kafin magrib zakiji d’ad’in jikinki” mik’ewa tayi zaune a hankali, ta tsugunna tare da zare socks d’in k’afafunta, kyawawan yatsunta suka bayyana jerraru wasu unique yatsu take da masu matuk’ar tsari da suka dace da y’ar k’aramar k’afarta, zare hijab d’in tayi tare da bak’in hulan kanta, kwancataccen gashinta da ya kwanta har gaban goshinta ya but gefen fuskarta har Kusan chin d’inta ya bayyana, Ammi ta bita da kallo, yarinyar har Mamaki take bawa Ammi she’s just 17 Amma Babu wani k’ira na ƴ’a mace da Bai cika ba a jikin Lailerh,k’irjinta a cike kamar zai fasa rigarta, ga wani flat tommy da take dashi kamar bata tab’a zuba abinci a ciki ba, and a tiny waist sai Kuma wani mad curvy hips kamar wadda tayi ciko, shiyasa ba kasafai ta fiye barinta fita Babu hijab a jikinta ba, yawancin kayanta dogayen riguna ne sakakku, gyaran murya Ammi tayi ganin tana k’ok’arin fita tsakar gida, juyowa lailerh tayi ta dubi Ammi Dan tasan da ita take dats Ammi’s way of calling her sometimes “zo ki kwashe hijab da socks d’in ki Kai d’aki first, ki cire kayan kizo kiyi wankan” da “to.”

Kawai ta amsa kafin ta k’araso ta d’au hijab d’in da socks d’in ta wuce d’ayan d’akin dake jikin wanda Ammi ta fito d’azu ta na yatsina fuska jin yadda tafin k’afarta ke mata ciwo, d’an k’aramin d’aki ne dake d’auke da d’an k’aramin gado irin na y’an boarding d’in nan mai kyau, sai y’ar k’aramar drawer mai marfi biyu a d’akin, ledan tsakar d’akin ya tsufa Amma ba sosai ba, sif d’in ta bud’e ta ajiye ninkakken hijab d’in kafin ta janyo zanin wankanta daga kan k’ofa ta zare kayan jikinta ta d’aura zanin ta ninke kayan da ta cire d’in ta ajiye a kan gado, kafin ta fito falo, har lokacin Ammi na zaune a falon, fita tayi tsakar gida ta bud’e k’aramin kitchen d’in ganin babban tukunya akan murhu yasa ta juya ta koma band’aki wankakken bokitin wanka ta d’auko tazo ta sauk’e tukunyar ta juye ruwan cikin Bucket d’in ta d’auka ta wuce band’aki, wanka tayi sosai ta ji d’ad’in jikinta zafin ruwan ya taimaka sosai wajen warware mata gajiyar da ta d’ibo daga shagon d’inkin nasu ta had’a da alwala, kafin ta bud’e bayin ta fito, da gudu ta k’araso falonsu saboda sanyin magriba da ya ratsa ta. d’aki tayi da sauri tsantsar sanyin da take ji har hak’waranta na had’uwa, manta ta d’auka ta shafa tana rawar sanyi bayan ta goge jikinta, tayi sauri ta zura doguwar rigar da ta ciro daga sif d’in tana Jin yadda sanyin ke raguwa a jikinta, bata son sanyi sosai gata da Jin sanyi, turarenta ta fesa a hankali kafin ta d’au wani hijab d’in ta fito falo.

Ganin Ammi bata Nan yasa ta wuce d’akin Ammin, a zaune ta ganta a kan gadonta tana maimaita Kiran sallah da akeyi a masallacin unguwan da suke ji rau kamar a gidan ake Kiran sallah. A hankali ta jingina da bango tana maimaitawa itama har aka gama Kiran sallah sukayi addu’a kafin Ammi ta dubeta, “kinyi wankan?” “Eh Ammi” “to kije kiyi sallah sai kici abinci idan kinyi isha’i sai ki kwanta, sannu.”

“Zan yi anan” ta fad’a tana d’auko daddumar Ammi dake gefe ta shimfid’a, mik’ewa Ammi tayi ta fita Dan d’auro tata alwalar, ta dawo ta zura hijab itama ta shimfid’a wani daddumar ta tada sallah, bayan sun idar Ammi tayi shiru tana tasbihi, da sauri Lailerh ta kwanta akan k’afafun Ammi tana fad’in “Ammi Dan Allah karkice in tashi wallahi na gaji” murmushi tayi ta shafa kanta a hankali ba tare da tace komai ba, d’an d’agowa tayi ta Kalli Ammi ganin tayi murmushi ta sake gyara kwanciyarta a kan k’afarta tana fad’in “Ammi!, madam d’inmu tace wai zata yayemu saboda munfi kowa k’ok’ari a shagon, duk set d’inmu mun fisu k’warewa zata bamu certificate next week ni da fadeela” “haba?, Ma sha Allah, Allah ya temaka” Ammi ta fad’a tana cigaba da shafa kanta. Allah kuwa, Ammi kince Zaki saya min keken d’inki!” Ta fad’a tana kwab’e fuska “Eh zan saya Miki mana, next week zan karb’i adashe, sai in cigita kud’in keken in sha Allah dama na bada fiye da Rabi” da sauri ta tashi zaune tana washe Baki sai Kuma ta fad’a jikin Ammi tana dariya wasu hawaye suka zubo mata hannu ta sa ta share a hankali. “Ammi Ubangiji ya saka Miki da mafificin Alkhairi Ammina, I want you to be happy Ammi, I love you!, ke kad’ai nake da, Ammi idan nayi kud’i Zaki ji dad’i, zan saya Miki mota in kaiki saudiya ki,kinji, kinga yanzu ina da followers da yawa a page d’ina na Instagram, da sauransu, idan nayi blowing aka sanni manya suka fara bani d’inki zakiga yadda zanyi kud’i kema ki huta shiyasa nake ta damunki akan kekennan Kinga…” ” Shishh!! ya isa haka uwar surutu” Ammi ta fad’a tana d’agota daga jikinta ” je ki d’auko abincinki ki ci” “zanyi Isha tukunna Ammi bana Jin yunwa” jinjina mata Kai Ammi tayi tana cigaba da abinda takeyi,.

A hankali ta jingina da gadon Ammi ta fad’a duniyar tunani, tunda tayi paper dis year zata Maida hankali akan d’inkinta sosai since she got d talent, idan results ɗinsu ya fito kafin nan su san abinyi she really wantto study further Amma tasan Ammi bata da k’arfin sponsoring d’inta. Sunkuyar da kanta tayi sai Kuma ta d’ago da sauri ta dubi Ammi ” laa Ammi na manta” d’agowa Ammi tayi ta dubeta alamun tana jinta ” Ammi Uncle Idris fa ya sake kirana a waya jiya” ta fad’a tana langab’ar da Kai alamun rarrashi ” “uhm sai akayi Yaya?” “Ya ce wai idan bamuyi claiming scholarship d’inba I can loose it, Ammi please, please ki Yi hakuri ki yarda” ta fad’a hawaye na kawowa idanunta, kawar da kanta Ammi tayi daga kallonta kafin tayi k’wafa tana girgiza k’afa “hmmm yanzu ke a haukanki Lailerh sai in barki ki tafi wata k’asa can da Baki sani ba Baki da kowa a can, noo I can’t, u are all I have bazan bari kiyi nisa da ni ba, bana kokonto akanki Lailerh da tarbiyyar da na Baki but I don’t plan on allowing you kiyi nesa da ni noo” zata Kuma magana ta d’aga mata hannun “tashi kiyi sallah ana Kiran Isha” ta fad’a tare da mik’ewa ta kabbarta sallah, kukan da ke zuwa mata ta had’iye tare da mik’ewa ta fice daga d’akin ta rasa me yasa Ammi bata so taje wata k’asa karatu bayan opportunity ne da ba kowa yake samu ba ita ta samu kasancewarta best student of the year a makarantarsu yasa uncle Idris ya yi mata hanya dan baya so k’ok’arinta ya tafi a banza, yanzu ta samu da k’yar Amma da alama Ammi bazata tab’a yarda ba.

Gadonta ta fad’a ba tare da tayi sallarba tana sauke ajiyar zuciya. tasan Ammi bata da laifi, Ammi bata da kowa sai ita itama batada kowa sai Amminta but she’s doing this for them both meyasa Ammi bazata Gane ba? A haka wani barci yayi awon gaba da ita tana sauk’e ajiyar zuciya. Cikin bacci taji ana matsa mata k’afafunta, a hankali ta gyara kwanciyarta dan d’ad’in da abin yake mata, Bud’e idanunta tayi a hankali ganin Ammi yasa tayi saurin tashi zaune. kallonta Ammi tayi ta tsuke fuska “tashi kije ki d’auko abincinki kizo ki ci” “to” ta fad’a tana sauk’a daga kan gadon ta wuce ta fita, Ammi ta bita da kallo kafin ta mik’e ta wuce d’akin ta. abincin ta d’auko taci kad’an Dan bata wani Jin yunwa, ta rufe ta fito ta d’auraye bakinta ta ajiye kulan a kitchen, har zata wuce d’aki ta dawo ta kwashe kwanuka da pots d’in da Basu da yawa daga wajen wanke wanke ta shigar kitchen ta rufe kitchen d’in buta ta d’auka ta d’auro wani alwalan kafin ta wuce d’aki, sai da tayi Isha kafin ta zare kayan jikinta ta saka wani dogon Riga Mai laushi Wanda dashi take bacci ta hau gadon da addu’ar bacci a bakinta, ko minti biyar bata k’ara ba bacci yayi awun gaba da ita. Sai da Ammi ta lek’o ganin tayi bacci yasa ta kashe mata wuta tare da rufo mata k’ofar ita ma ta wuce d’akinta.

Washe gari da asuba Ammi ta tasheta sai da sukayi sallah, sukayi azkar har gari yayi haske kafin ta mik’e bayan ta gaishe da Ammi ta amsa, tsintsiya ta d’auka ta share ko ina har tsakar gida tasss, ta tattaro wanke-wanken ta wanke wajen ta ja ruwa a rijiya ta wanke ba yi kafin ta hura wuta ta d’aura ruwan zafi, bayan yayi zafi ta d’au flask ta zuba ta sake Maida wani wuta ta Kai flask din falon dake ta k’amshin turaren wuta da ta saka, ta ajiye ta koma ta d’auko cups guda biyu da spoons ta ajiye ta wuce d’akin Ammi, Madara, sugar da Milo da Ammi ke Siya tana ajiyewa ta d’auko ta ajiye kafin ta Bud’e jakar Ammi duk tana kallonta 200 ta d’auka ta fita ta siyo bread, sai da suka karya kafin ta juye ruwan zafin ta d’aura wani, Ammi ta fara wanka kafin ita ma ta juye tayi, kafin ta fito har Ammi ta shirya fess ta Sako hijab d’inta tana zaune a falo, a gurguje ta wuce d’aki ta shirya, Riga da skirt ta saka ta gyara gashinta da ya d’an wargaje tayi ponytail da shi ta sake d’unkule shi ta saka hula a kanta, ta taje giranta ta gyara shi,chapet ta safa a pink tiny lips, sanin halin Ammi yasa ta zumbud’a hijab Black colour har ƙasa da ya haska fuskarta sosai ta tsuguna ta saka socks kafin ta fito.

A tare suka fito kasancewar Ammi tana aikin koyarwa a wani primary school, though ba wani albashi Mai yawa bane but da shi suke ci da Sha da rufa ma Kai asiri, ga Kuma Lailerh tana d’inki dudda ba’a yaye su ba tukun Amma mutane sun gwammace su bata d’inki akan Madam d’in ma Dan ita nata talent ne kawai duk yadda ta Maka d’inki dole ka soshi tun ma kan ta k’ware haka her hands are just gifted, sai da Ammi ta sauk’e ta a shagonsu bayan ta k’ara ja mata kunne akan nutsuwa kame kai kafin ta wuce school itama tana Jin y’ar tata d’aya tal a ranta.

Maimoon

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×