"'Eh! Nawa za'a ciro maka?"
Sai da ya zaro Atm ɗinsa daga cikin wallet ya miƙa ma jami'in.
"A ciro min dubu ɗari biyu, su cire cherges a cikin acc ɗin."
Ya faɗa musu pin ɗinshi sannan ya sake mayar da hankali kan Alhaji Lukhman, wanda har lokacin bai samu sararin ɗago da kanshi ba.
Ko da ya mayar da idanunshi kan Khamis da wani masifaffen haushinshi da yake ji, sai yaga idanunshi a buɗe, shi kaɗai yana ta ƴan harare-harare. Babu alamun damuwa da halin da aka fice da Firdausi ko. . .
Masha Allah….I’m learning a lot from this story
tea, sad more lesson from this story