Ba kirga kwanaki yakeyi ba yanzun, saboda wani irin tsayi da suke mishi wajen wucewa. Rayuwar ma gabaki daya bayajin dadinta, saboda cikin watanni ukun nan ta kowacce fuska rayuwar ta hade mishi waje daya. Su Anna basuce suna fushi da shi kai tsaye ba, amman bayan gaisuwa babu wata magana mai tsayi da take hada su, bai samu fuska har a wajen Appa da zai roki su sake zuwar mishi wajen Hindu ba. Hatta AbdulHafiz har yanzun bai huce da shi ba, ko yayi kokarin fada mishi damuwar shi baya saurare, satin daya wuce ma kai tsaye AbdulHafiz din. . .
I love to read the book