Skip to content
Part 31 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Da daddare kuwa food flaks din mu nake dauka in kai wurin da ake kwashe tuwon dare a zuba mana namu in yi musu sannu da aiki in dauka in kawo mana in zuba mana manshanu da yaji muci ba tunda ya hana ni cin abincin hadaka da su ba, ban dai kara tsinkewa na lamarin gidan yawa na kara tsorata da zaman gidan yawa ba irin ranar da aka wayi gari a gidan ana tuhumar Ade ‘yar dakin Yaya Furera wai tayi gulma.

Ade kuwa kishiyar, Ruwailah ce ranar ne na gane su matan gidan ba shugabancin matan sasansu suke yi ba, a’a group ne kawai daga kowane sassa kake in kana so zaka shiga kan hakan ne ma nake ganin tamkar gaba dayansu kowacce kokari take ta janye ni in shiga nata group din.

Ni kuwa kashedin da Ado ya yi min da kuma ganin abinda ya faru a ranar don ma anyi sa’a Yaya Baidu yana gida, shi ne ya fito yayi tsawar da kowacce ta shiga taitayinta da ba a san abin da zai faru ba, yasa na kara tsorata na kara kama kaina.

Sannu a hankali ma sai na daina zuwa karbo mana tuwon daren, ina yi mana namu saboda kullum Ado yana yi min maganar ke ba taya su aikin komai ki ke yi ba, amma sai kin je kin karbo musu tuwon su, in nayi abincin daren dai ban sawa kowa, amma na rana gabadaya tsofaffin gidan nake sanya musu, su kuma yaran matan wacce ta aiko danta ko tazo ta ce in zuba mata in zuba mata, wacce bata aiko ba shi kenan. Don abin da ya ce kenan, sai ko yaran gida da na gama suna wurina.

Yarda da bin ka’idojin Ado da nayi sai suka yi dalilin da na samu wata irin rayuwa a tare dashi wacce ta fahintar dani cewar ita mace ba wai tarin dukiya ko wani kyale-kyale ne yake samar mata farin ciki da kwanciyar har kalin rayuwarta ba, a’a mijinta kawai.

Kullum ni da Ado a cikin tarairayar juna muke, yana gudun bacin raina ina gudun nashi, yana tattalin farin cikina kamar yanda nima nake tattalin nashi, duk da matsanancin aikin da yake fama da shi a gonakin shi ramar shi tayi matukar raguwa, saboda yana da kwanciyar hankali a gida ina kuma tarairayarshi da abinci mai kyau.

Rannan muna daki da daddare ni da shi, hadari ne ya taso a gari ganga-ganga, tuni na fara sabawa da irin wannan hadarin mai yawan iska da rugugi gami da tsawa, shafa maina nake yi ban fasa ba, na ce mishi kai-kawo hadarin nan ba irin namu ba ne na can.

Idon shi yana lumshe ba tare da ya yarda ya bude su ba, ya ce min eh ai ko ruwan ma ba daya ba ne, in kin lura ai mun baro can ne damuna ta riga ta kankama sai muka zo nan muka tarar lokacin ake shuka.

Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi idon naka yana ciwo ne? Bai yarda ya bude suba ya ce min to ko ba sa ciwo Humairah tunda ki ka zauna kika bar kirji a waje ai dole in yi maza in rufe su in dai ba so ki ke in kasa cika alkawarin da nayi miki na cewar shekaran jiya waccan da wacce ta wuce da jiya da yau da gobe duk za su zamo ranakun hutu ne a gare ki ba, don ki san in aka yi min alheri nima na iya irin nawa alherin.

Na yi murmushi na ce eh, gaskiya ne kar ka bude kai dai to dan bani hannunka in sa shi yayi min wani aiki.

Ba tare da ya bude ba yayi maza ya miko hannun yana laluben in da nake tare da fadin ungo shi Humairah ungo hannun nawa karbe shi ki Sanya shi hidimar da ki ke ganin ta dace da shi ina kama hannun nashi na ji Ado ya yi wani irin ajiyar zuciya mai sanyi ban sake ganin yanda aka yi ba sai ganina nayi a gefen shi a kwance ya zagaye ni da hannayen shi duka biyu tare da yi min tambayar.

“Kin san wani abu ne Humaira?” Bai jira na ba shi amsar na sani ko ban sani ba, sai ya soma rattabo min bayaninshi, ke din mai alheri ce, alherinki kuma yawa ne da shi saboda kina da kirki ga ki da abin arziki iri-irni, in ki ka ga dama sai ki sa mutum ya rinka ganin tanfar babu ma wanda ya kai ki abin arziki, balle ya iya fin ki.

Ban kula zancen na Ado ba, iya ka dai nasan in dai barin shi ya yi yanda yake so shi ne kirki, ko alheri to na yi mishi.

Muna cikin irin wannan zaman mai dadi ni da shi wara magana ta taso a cikin gida, Ruwaila ce take yawan yi min magana akan kankane ni da Ado yake yi, yana hana ni mu’amalla da kowa cutata yake so yayi dama haka tsofaffin maza suke yi ma matansu, don su hana su fahimtar komai.

Shi Adamu ai ba yaro bane ga sa’o’inshi ne da ke garin nan suna shirin yin surukai, ko ma daukan jika kwanannan, don haka ga adashe nan na kafa ki zo ki shiga, na ce ai ba zai bar ni ba, ta gallà min harara “Ke ko iya zama da miji baki yi ba? Ai kamewa za ki yi daga gare shi ba a sakan mishi jiki haka sakakaka ba, in ki ka ga ya matsa sai kema ki bijiro mishi da taki bukatar.

Mu da muke da shashun kishiyoyi ma muke yin hakan muci nasara balle ke ke kadai? In ki ka saban mishi da yanda ku ke din nan ai wahala za ki sha tunda in ke kin yarda da hakan wata ba za ta yarda ba, kin kuma san ana yin kaka in ya saida amfanin gonarshi kishiya zai yiwo miki.”

Kirjina ya bada sautin rugugugu! ban sani ba ko itama ta gane tsananin tsoratar da nayi ne yasa ta yin murmushi, ta ce “Lah, to wannan ai ba wani abu ba ne, mu nan ai haka ake yi kaka tana yi in aka cika runbuna da hatsi, to abinda yai saura sai akai kasuwa a sayar sai ki ga an kawo miki wacce zaku ci hatsin tare shi kenan.”

Ta sake kallona ta ce min, to balle ko mijinki da wahalar damunar nan bata hana shi manne miki ba, ai kuwa kin san ya huta da kaka akwai magana, na kuma ji Yayanshi yana cewa yayi noma ba kadan ba, in kaga irin aikin da yake yi ma sai ka ga tanfar da gayya yake yi.

Sammako yake yi ya riga kowa tafiya, sannan duk a can ake baro shi, na ce mishi babu wata gayya so yake yi yayi gini ya kuma kara wani auren, ai kuwa dolen shi yayi aiki tukuru.” Na zuba mata ido kawai ina kallonta don kuwa ban taba jin maganar da ta dame ni ta daki zuciyata ba irin cewar wai Ado zai yi min kishiya, to ni kuwa kenan ribar me naci a biyo shin da nayi?

Ta sake kallona cikin natsuwa ta ce, yarinya kamar ki ya kyale ki kina yawo cikin wasu zulunbun dogayen riguna da tun suna baiwa mutane sha’awaa har sun daina sun maida ke kin zama tanfar wata tsohuwar Babarbariya.”

Kalaman na Ruwailah sun yi matukar yin tasiri a zuciyata, musamman da ta tabbatar min da cewar su al’adar mazansu ne ma in sun cika runbu da hatsi, to abinda ya saura in an kai shi kasuwa aure ake yi.

Don haka nan na kame sosai daga yawan sakewa Ado fuska, al’amura suka yi matukar sauyawa a tsakaninmu, da yazo zai taba ni sai in ce mishi cikina na ciwo, sai yayi maza ya kyale ni.

Rannan dai ta kure, mun kai wajen sati uku a haka tunda safe Ado yake yi min magana, rarrashina yake yi a dalilin bai son tilasta ni saboda abin da ya taba faruwa a tsakaninmu, ganin da nayi ya matsu kwarai mu fahirnci juna ya sani bijiro mishi da maganar adashen da ake yi a gidan, wanda ni kadai ce bana yi.

Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, “To kina da sana’a ne Humairah? Adashe ai na mutane masu sana’a ne, ke ba ki da sana’a ni ba wani abu nake yi ba in ban da maganar gonar nan, gona kuma ci mun kudi take yi bata fara bani ba, yanzu ne nake neman aikin koyarwa tunda na gaya miki na mika takarduna ba kuma zan yi wani aiki da bai wuce koyarwa ba a yanzu, saboda ina son in jarraba yin noma sosai.

Ni yanzu fatana da addu’a ta bai wuce mu kai lokacin da za a yi girbi asirinmu bai tonu ba. Na rantse miki Humairah rutin asirin Ubangiji ne kawai yake tafiyar mana da al’amuran sai ma ganin kamar zata kure sai kuma in ga wata hanyar tazo ai, wani lokacin ma ba da gangan nake kwashe miki kudinki ina bar miki nera hamsin ba, Kurewa take yi. Kiyi hakuri kin gane? Nasan kina hakuri dani, amma ki kara maimakon in ji wannan rarrashi da bayanin da yayi min, na riga naji zuga zugan da aka yi min cewar su din ma’ana, ‘maza’ ba ayi musu sassauci mai yawa sai su raina mutum.

Don haka sai na kara daure fuska na kara bata rai na ce, to sai muyi hakuri duka, na kawar da fuskata gefe.

Abin da kawai na fada kenan, sai ya fahimci abinda da nake nufi, muyi hakuri duka? Na ce, eh, me kenan hakan yake nufi? Na sake bata rai na ce, ko ma menene? Ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, waye ya koya miki wannan iskancin ?

Nayi kamar ban ji shi ba, ya ce to ai da sai ki gaya mata naki mijin ba irin nata ba ne. na ce uhn, na mike da nufin fita in bar mishi dakin, sai kawai naji ya kamo hannuna ya murde da karfi, sai da na kwallara kara mai tsanani, amma bai sake ni ba.

Ai babu in da za ki tafi sai kin gaya min wacece take koya miki wannan iya shegen? Ruwailah ko? Sai naci abu kazanta, in bata yi hankali da ni ba, ha’a me tayi maka zaka zage ta?

Kau na ji, ya wanke ni da wani irin wawan mari, nayi maza nasa daya hannun na dafe wurin, ai in ba ki gaya min wacce tasa ki kiyi min wannan wulakancin ba, za kiyi mamakin abin da zai faru yau.”

Na soma mutsu-mutsun kwatar hannuna naga hakan ba zai yiwu ba wahala kawai nake karawa kaina bai kuma kula kukan da nake yi ba, balle ya damu da cewar rana ce mutanen gida zasu iya jin abin da muke ciki.

Wulakanci irin wanda Ado yayi min rannan bai kwatantuwa, murde ni yayi ya yi abin da yaga ya yi mishi daidai sannan yasa kai ya fita ya bar gidan da azahar tayi ma ya sake dawowa, babu kuma wata mu’amulla ta rarrashi ko sassauci a tsakani na rasa in da sa kaina in ji dadi, ga shi kuma bsbu halin in kai kara in maganar ta fto ban san me zai faru ba.

Ba kuma zan iya gayawa Gambo ba in ce tayi mishi magana, nasan zai iya gaya mata abin da ya hada mu, na kuma san zata yi fushi mai yawa don na saba jin ta tana cewa dabi’ar matsiyatan mata kenan su ne wadanda ba za su gaya wa mazansu bukatunsu ba, sai a lokacin da suka ga sun matsu da su.

Don haka na lallaba na samu Ado ina kuka na ce mishi kayi hakuri Kawu ka daina irin wannan mu’amullar dani.

Ya dago ido ya kalle ni ban san yadda aka yi ba, tausayina ya kama shi cikin natsuwa ya ce min ya wuce amma ki gaya mata tayi hankali da ni ko wacece? In ita bata sani ba ke kin sani cewar Mama ita ce mafi darajar mutum yau a wurina tunda bani da uwa ba ni da uba su Baba Tanimu ne iyayena.

Ita ta rike tayi min gatan da nayi karatu na koyi al’amura masu yawa na rayuwa, amma sa nayi jaruntakar rabuwa da ita don in zauna dake ya sake zuba min ido yana yi min kallo mai tsanani, shi ne za’a saki kiyi min abinda ki ka san zanyi bakin ciki?

In ana son cutar da ni sai a hada kai da ke? Yanzu in an san ina sonki sai ayi amfani da ke? Ni in ina da hali sai kinyi adashe? Me zan yi da kudin? Hankalina yayi matukar tashi jin kalaman Ado nayi matukar jin kunya da Nadama na abin da nayi mishin kuka sosai na soma yi ina bashi hakuri don kuwa na san ba karamar wauta nayi ba dana ji irin wannan zugan na kuma yarda nayi amfani da ita.

Na dade sosai ban iya sakin jikina sosai da Ado ba saboda naji kunyar abinda nayi mishin ba kadan ba duk dai shi din bai sake yi min wata magana ba ko kuma nuna min wani abu.

Ana cikin haka rannan ya dawo da rana, wasu takardu ya ciro a aljihunshi ya miko min, nasa hannu biyu na karba ina dubawa tun kafin in kai ga gama karantawa ya ce min naje nan Government Day Secondary School Dabai nayi magana da Princepal din ya yarda za ki soa zuwa satin nan.

Kije kiyi karatu ki samu takardar ki yafi min wunin da za ki rinka yi a gida bana nan ana koya miki abin da ba zai min daidai ba, da na bari ne sai badi don in ga na soma yin wani abu, to amma sai na tuna kuma ai ‘Though Times Never Last but though people do.”

A haka na soma zuwa makarantar (S.S. 2) aka sanya ni, babu kuma abin da Adon bai saya min ba na karatuna, tun daga uniform, sandal, safa, har zuwa littattafai na karatu. In nayi shiri zan tafi in sanya dogon hijabina akan uniform din sai na shiga cikin makaranta in cire in shiga aji in mun taso ma in mayar.

Tunda na shiga makaranta na soma koyon jarumtaka kan al’amura masu yawa nayi matukar rage baccina, kullum na kan tashi ne da wuri in yi mana abin karyawa da abincin da zamu dawo muci da rana, in zuba a cikin food flask kafin in yi wanke-wanke, in yi wanki in yi shara in yi wanka.

Karfe bakwai nayi kuma zan sanya kayana in dora hijabina in je in gaida su Baba da su Goggo, da sauran mutanen gida, in fita waje in samu Ado yana jiran fitowata bayan ya rurrufe mana wurinmu mu jera mu tafi sai yaga shigata makaranta sai ya wuce gonarshi.

<< Mijin Ta Ce 30Mijin Ta Ce 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×