Skip to content
Part 38 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Wanda zai yi mana amfani dukanmu, ki rinka zuwa kina samuna adalci muna hira da daddare in su Goggo sunyi bacci.

Na girgiza kai nuna alamar rashin yarda tare da fadin ba zan tun kafin in karasa maganar tawa ya katse ni da wata irin rantsuwa na kuma san ba dabi’arshi ba ne yin hakan.

To na rantse miki babu inda za ki in dai ba ki yarda da wannan ba gaba daya na fasa tafiyar ki zauna kawai tunda ni dama ba don ke na shiryata ba, don Gambo ce nasan yanzu haka tana son ganinki balle taji kin haihu.

Zata zo ta gan ki taga abin da ki ka haifa amma duk da haka nasan in nayi waya na ce mata tayi hakuri wani uzurin ya hana ki zuwa, ai zata hakura tunda ita ba irin ki ba ce, ace mata baka da ikon sarrafata.

Ba ka da halin ka ce mata ga yadda za’ayi ta ce maka to sai a’a? Sannan a rinka yimaka karyar ladabi da biyayya ta musu? A haka fa muke zaune ni da ke in kin yi min alherin kwana bakwai to sai kin yi dalilin bacin raina na kwanakin da ban san adadinsu ba.

Cikin zuciyata kalaman Gambo suka fado min game da muhimmancin mijinka yasan alherinka to ni yaushe ne Ado zai san alherina da kokarina akan shi ya rike wannan yabon guda daya a mafi yawancin lokaci yakan yabe ni ne a daidai lokacin da abin yabon ya faru.

Amma ‘yan mintoci kadan bayan nan da zan yi mishi wani kuskuren musamman ace kan abin da ya shafi kankanshi ne ba zai tuna kokarina na baya ba don haka naji hawaye sun fara zuba a idona a dalilin zuciyata ta kuntata na fara kukan kenan sai ga Goggo ta shigo.

Ni fa naji abinda ya ishe ni wai ina dalilin wannan kuka ne na iya shege? Kai Adamu yayi maza ya ce na’am Goggo ta ce na roke ka ka yi wa yarinyar nan abinda take so.

Ya ce mata to Goggo ya tashi ya fita ya bar mu ni da ita a dakin tana ta mita dama kin yi a hankali namiji ne in ki ka zauna ki ka yi jegonki na gaskiya ma ina ruwanki da shi yaushe za ki je kina daga ido kina kallonshi. Balle ki san abinda yake ciki ranki yana baci a banza, taja tsaki ta wuce ta fita taje sanya mana ruwan wankan yamma.

Mun kammala komai muna shirin kwanciya Goggo kam ma tuni take ta faman gyangyadi jira kawai take yi in gama baiwa Umamatu nono in mika mata ita suyi kwanciyarsu da tuni tayi barcinta, don tare suke kwana.

Muna cikin haka sai ga Ado ya shigo, Goggo sai da safe ta ce mishi to sai da safe, ta amsa daidai ta karbi yarinyar sunyi kwanciyar su.

Nan da nan ta soma minshari, ya mike tsaye yana kallona mu je ko? Nayi kamar ban ji shi ba, na ce muje ko? Ko kina son yi min wulakanci ne? Na mike tsaye na fita na nufi wurin namu gabana sai faduwa yake yi, shi kuma ya tsaya yana jawowa Goggo kofarta wacce dama ba sakata take Sanya mata ba.

Ina shiga dakin na shaki wani irin kamshi mai dadi ga kayaiyakin ciye-ciye iri-iri ya ajiye ga wasu dunkakkun zannuwan da ban san da su ba a gefe.

Yana shigowa yayi murmushi, kici wani abu mana ga kuma dinkunanki nan ki duba, na ce uh’uh ai ba dadewa zan yi ba.

Bai kalle ni ba ya ce min dama kin saki ranki don ba zan yarda da wannan dari-darin ba kin gane?

A kan dole na saki jikina da Ado na bar shi yayi abin da yaga dama, kuma wai maimakon yayi la’akari da halin da muke ciki na satan jiki muka yi na kawo mishi kaina bai damu be, bai yarda ya hakura dani ba sai wajen karfe biyu na dare.

Ya rako ni na dawo dakin Goggo na hau gado na kwanta yayi min sai da safe yaja kofar ya koma wurinshi don yin wanka tunda ni kanm na riga nayi nawa.

Na fara bacci kenan, Goggo ta tashen a dalilin yarinya ta tashi na karbeta na bata nono.

Washegari da safe Ado ya shigo bayam munyi wanka daga ni har yarinyar Goggo tana wurin kosanta, zama yayi a bakin gadon yana wasa da kafar yarinyar dake faman shan nono.

Zan fita amma ba zan dawo da wuri ba in na dawo zan zo in sanar da ke don ki zo ki same ni, na ce mishi kai ya yi maza ya katse ni da kin koyi ce min to don ki rinka samun cikakken lada.

Da daddaren kuwa sai da ya dawo ya zo yaja ni muke je. Washegari ma haka tun ina tsoro sai kuma na saki raina, rannan ina tare da shi mun yi matukar sakin jiki mun shagala cikin al’amuranmu.

Gaskiyar magana ita ce daga ni har shi muna son juna, muna son kasancewa tare da juna, nakan dai jawa Ado raine kawai in yi mishi yanga saboda kawaici da kuma jan aji irin namu na mata.

Amma in ba haka ba kasancewa tare da shi yana sanya ni jin dadi, ya sanya ni farin ciki da nishadi, ya sanya ni in rinka ji da ganin tanfar bayan ni din to babu wata. Barin komai yake yi ya tarairaye ni ya gaya min kalmomi masu sanyaya rai da tofar da zuciya.

Ya maida kanshi zama tanfar wani dan yaro ko wani mara yawo a gabana, bai kuma gajiya kullum muka shiga cikin irin wannan halin zai nanata kalmarshi guda daya da ya saba gaya min ita ce ke din matata ce Humnairah.

Ke ce matata kar ki taba ganin nayi aure a wanilo kaci kiyi tunanin zan mallaka mata kaina kamar yadda nake mallaka miki ko zan zauna in yi mata shagwaba da sakarci irin wanda nake yi miki.

Muna cikin wannan halin ne kawai naji Goggo Ayalle tana kwala min kira a tsakar gida da iyakacin karfinta, a cikin kuwa wannan tsohon daren.

A kidime kwarai nayi maza na bude baki da nufin amsawa don in hutar da ita wage bakin da take yi tuna yi min irin wannan kiran a cikinwannan daren wanda nasan da wuya kwarai ace akwai wani cikin mutanen gidan nan da bai ji kiran da take yi min din ba, tunda dare ne, dare kuwa ba raina motsi yake yi ba.

Ado ya yi maza ya dora tafin hannun shi akan bakin nawa ya rufe da iyakacin karfinshi, don hana sautin maganar tawa fitowa sosai.

Ganin hakan ya sanya ni kokarin kwatar kaina a hannunshi, tunda shi da kanshi ya ji kiran da ake yi min daga inda muke din kuma muna jin muryar Umamatu da ke ta faman canyara kuka.

Amma hakan bai sanya shi ya hakura ba, sai da ya natsa don kan shi sannan ya kalie ni cikin wani yanayi da yafi kama da na tsananin gajiya.

A hankali ya bude baki yana yi min magana, ke ba ki da wayo ai shiru za ki yi abin ki sai ta gaji ta koma daki sai kiyi fitowarki, na ce mishi to.

Amma duk da haka jikina ya kai matuka wajen tsorata sai bari nake yi, ya zuba min ido yana kallona ke menene haka? Na fa zunubi muka yi ba ni mijinki ne ke matata ce.

Na ce mishi uhun, ai ni babu abin da yafi damuna da tsayuwar min a rai irin bazuwar maganara cikin gidannan da yanda za’ayi ta yadata ana cancanzata, cikin sauri ya ce min ke kar ki nemi ki maida mutane wadansu iri mana. Goggo Ayallen da girman shekarunta ne ki ke cewa za ta yada wannan maganar?

Kina so ki ce ita din bata san girma da lalurar aure ba ne? Nayi kamar in ce to ai a sanin girma da lalurar auren nata ne taja ta tsaya a tsakar gida a cikin tsohon daren nan ta wage bakinta tana kwalawa sunana kira tamkar wata yarinya yar karama.

Bayan kuma tasan karamin motsi ma dare bai raina shi ba, balle wannan ihun da ta rinka yi wanda ba mutanen da ke cikin gidan nan ne kadai za su jiwo ta ba, har makwabta sai sun ji.

Sai kuma na ce uhun, bari dai ma kawai in kama bakina in yi shiru, kar in jawowa kaina wata magana tsakanina da shi a wannan lokacin da na san ba karamin abu zan fuskanta a cikin gida ba, in fadi wata magana ya ce na yi wa matar Baban shi rashin kunya.

Rako ni yayi nayi wanka yana tsaye yana jiran fitowata sannan ya tasa ni a gaba ya kai ni har kofar dakin Goggo Ayalle. Ya kalle ni cikin natsuwa da murya mai sanyi ya ce min shiga kiyı kwanciyarki na sake daga ido na kalle shi.

Fuskata ta bayyanar da alamar tsoro yayin da zuciyata ke ta faman harbawa da sauri ya sake kallona fuskarshi ta bayyanar da murmushi mai yawa daina jin tsoro Humairah.

Ai ni mijinki ne ba wurin wani kika je ba kin amsa umarnina ne na kuma gode miki iyakar abinda Goggo zata yi in ma ranta ya baci ta ce ki koma dakinki gobe shi kenan, amma ba za ta je tana yáda wannan maganar ba.

Ai ita babba ce, in kuwa haka zata yi to ai ai yafi min na riga na gaji da wankan naki, kin gane? Na gyada kai nuna alamar eh, don ni kam ko bude bakin nawa in yi magana bana iyawa, saboda kaduwar da nake yi.

To shiga mana, na kalle shi cikin natsuwa a hankali cikin muryar da tafi kama da rada na ce mishi, to jeka ka kwanta zan shiga.

Ya ce uh’uh ai ba zan bar ki cikin daren nan a waje ba in haka yasa na tura kofar a hankali na shiga. Cikin sa’a gaba daya dakin a duhu yake nayi matukar jin dadin hakan don haka na lallaba a hankali na dale kan gadona, ina shirin kwanciya kenan sai kawai naga Goggo ta hasko ni da tochlight dinta.

Ashe wai duk abin nan da ake yi duk da

dadewar da nayi ban baro wurin Ado ba, duk da ita yarinyar tuni ta hakura da kukan nata ta koma baccinta.

Ita Goggo bata hakura ta kwanta ba, tana nan zaune dingir a tsakar dakinta bata ma yarda ta hau gado ba, don kar tayi gyan-gyadi da bacci zai dauke ta har in shiga bata sani ba.

Don haka tayi zaman dirshan a tsakar daki tana Jiran sai taga zuwana wai ita nan a dole sai taga KWALUWAR DAKA’.

“Ina ki ka fito? Ruwan me ke diga a jikinki? Jegon kenan? Dama damuwarki kenan yasa kika yi ta tasa yaron nan a gaba da koke-koke? Haba ni fa kuka na soma yi wa Goggo kuka kuma mai tsanani, saboda tambayoyin nata sun yi min tsanani da yawa.

Kukanki din banza da na woff? Ina…daga waje Ado yayi gyaran murya mai karfi, wai dai don Goggo tasan shi din bai yi nisa ba yana wurin ko zata yi hakuri ta bar maganar tata.

Ban sani ba ko bata gane abinda gyaran muryar tashi ke nufi ba ne ya hana ta saurarawa ta ci gaba da fadin ina amfanin ace mace ita ce fitinanniya?

Namiji bai damu ba sai ke ce Uh’uh Goggo, uh’uh Goggo, abinda ya ci gaba da fadi kenan don kara yi wa Goggo Ayalle kashedin maganar tata, yayin da ni kuma gabana ke ta faman harbawa saboda tsoron kar ya ce zai tanka mata.

Gaba daya fatana da burina bai wuce ya bar wurin tsayuwar tashi yayi tafiyarshi wurinshi, ba tare da ya bude baki ya ce mata komai ba.

Saboda nasan yin maganan nashi ba zai taba haifar mana da da mai ido ba, kin barin maganar da Goggon tayi shi ne ya hassalar da Ado har yayi dalilin da ya toro kanshi cikin dakin ya ce mata ba ita ba ce Gogggo ni ne, ba ita ba ce kyale ta kawai ni ne.

Abinda kawai naji Ado ya gayawa Goggo Ayalle kenan sai kawai naga ta fashe da kuka tare da salati mai tsananin karfi.

Mu tafi littafi na hudu don jin yadda za a kare.

<< Mijin Ta Ce 37Mijin Ta Ce 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×