Sai da ta gama ringing number din Hamid da na Kira harta katse ba'a 'daga ba tunanina 'daya biyu ya bani ko dai baya 'daga baqon number ko baya kusa da ita.
Wayar na cigaba da dannawa, ina jin mamaki wai wannan wayar ce ta haura hamsin ta tafi 'daruruwa, kuma an kashesu ba'aji wani 'dar ba,ni Kam da ku'din aka bani ai ba ni ba, harsu Halima da Batul sai sun san Ina da ku'din, amma ga abunda yakamata suyimin da ku'din su 'bige da siyamin waya ba zance ban gode ba dai. . .