Skip to content
Part 19 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Sallamar da Halimah tayi yasa ni saurin dawowa daga tunanin da na shiga yi na yi saurin dagowa na kalleta gami da amsa sallamar,Haliman duk ta rame sai naji tausayinka nake ba wai nawa ba,’daurin qirji ne jikinta har wani rawar sanyi take yi bata kai ga qarasa bushewa ba da ka ga alamunta daga wankan ta fito kuwa.

Fa’da’da fara’arta tayi tana qoqarin zama gefen gado.
“Mutanan Katsina ashe kina Shirin dawowa ko maganar ba mu yi ba jiya.”

Na dubeta yadda take maganar da take qoqarin dauko Mai saman drower ‘din da ke gefen gadon.

“Halima ba wannan ba, ashe ba kida lafiya haka Sam baki bani labari ba,kuma kinsan zazzabin naki ki kaje ki tsalo wankanki kina ta rawar jiki.”

Murmushi tayi.

“Kyale zancen nan dan,Sumayya ina shafa mai na nemi kaya nasa shikenan,Umma tana kada nayi wanka ina zazzabi Ina ganin batanan naje nayo shi saina fara tashi ai Ina tsami,naji sauqi kwana 2 ne da fara zazzabin nawa.”

Tausayinta naji ya sake kamani.

“Halimah rigima kenan.”

“Ni dai naji bani labari naga jakarki kuma,baki je gida ba ya akayi ne?,duk naji ma jikina ya qara sanyi Sumayyah mai ya faru?”

Hawaye na goge kawai,banasan tadawa Halima hankali amma ya zanyi fa’dar shine zai kwantar mata da hankali, nasan ta da abu ka’dan ke sata damuwa.
“Halimah, su Mama sun koma Gwarzo,ina dawowa yanzu na samu labari”

Dan Allah Sumayya bani labari sosai yadda zan gane na fahimceki sosai,yadda ta buqata na cigaba da bata labarin komai da ya faru yadda ta buqata Halima ba qawar da zan ‘boyewa damuwata bace ba na cigaba da maganar.

“Har yanzu Halimah nakasa fahimtar ta ina na cancanta ‘din nan,na yarda da maganar Abbah Hashim ba nida wani cancanta saboda yadda rayuwar take tafiyar mana mu talakawa ne abincin yau da gobe yana gagararmu,Yaya Samir bai dace da ni ba ma,bana tunanin Hamid zai dace dani.”

“Sumayyah kin cancanta da komai ke ‘din abar a sadaukar da komai ce a tsira da rayuwa saboda samunki,fatan alkhairi ko wanne second da mintina nake ma qawar qwarai,ki goge hawayenki Sumayyah,akwai ranar da kowa da kowa zai fahimceku da rayuwarku,ranar wa’danda suka kasa kasancewa da ku harku ci alfarmusu sune zasu zo suna ci ki yarda ubangiji yana juya lamuransa cikin qanqanin lokaci,ki miqa lamuranki da naku gaba ‘daya bisa ga ubangiji.”

Kuka na fashe dashi jin kalmomin da Halimah ke anfani dasu wajen ban haquri gareni da lallashina,bisa ga dole na haqura ganin zan qara ‘dagawa Halima hankali ganin bata jin da’din jikinta.

Kaya Halima ta nema ta saka doguwar riga ta yadin material mai kauri kyawunta ya qara fitowa,Haliman kyakkyawa ce sosai,dan hasashena har nakejin ma ta zartani fara ce,mara girman jiki,rigar ta yi mata kyau dukda ba tsayawa tayi kwalliya ba.

“Bari na zubo miki abinci nasan kinsha yunwa,dan Allah ki bar damuwar haka inajinta nima sainaji kamar ni ce” da wannan zancen ta miqe ni Kuma na bita da kallo ba jimawa ta dawa ‘dakin,da plat cike da abinci ta ajiye gabana jallop ‘din shinkaface tana qanshin kifi.

“Ba zafi dai kinji yi haquri haka,nasan zaki iya ci ko,bari na bawa Faisal ya siyo miki ruwa”,Faisal ta qwalawa Kira sai gashi ya shigo ‘dakin

“Gani Yaya Halimah”

“Yanzu Sumayya ma tazo mutuniyar taka ko ruwa baka siyo mata kai Faisal anya kuwa ,ko ba danni ba Ahmad fa abokin kane”

Kai ya sosa “Yaya ai babu ku’din ne,kinga ma na manta Haris ya fa’da min su Ahmad sun koma garinsu,da baki da lafiya ba muyi zancen ba”

“Haka nake samu labari,ka ansa wajen Yaya Baffa kace inji ni, za’a siyawa Sumayya ruwa,nasan su Yaya Hakim sun fita ko?”

Ya ‘daga kai”Eh sun fita sai dai inji ki ‘din kuwa Baffa ba mutunci abin shi bai ciyuwa,kema bansan yaushe kuka jone ba,ko dan kinyi zazzabi ne”

Dariya Haliman tayi”Wato Baffa ai shikenan wuce ni ka siyomin abinda na aikeka”

“Dan fa Yaya Sumayya zani duka 2years Kika bani kike wani bani command haka”

Sai lokacin Faisal ya wuce ,Halima ta juyo
“Kingani ko Faisal ya rainani wai shekara biyu na bashi,gaba ma zai ce ya girmeni ne yaga yayi tsawan qafa”

Dariya nayi “irinsu kenan su Ahmad ai yanzu wasu tunaninsu ma shine yayana sai anzo anji yana Yaya,ake tantancewa,yana fa’din ma ya kusa daina cemin Yaya mama tace shima an kusa daina ce masa Yaya”

“Ai kuwa shikenan”

Ina cin abinci muna ta’ba firarmu ta school dai dama tafi yawa kafin na tsokanowa Halima zancen Aliyunta

“Yawwa Halimah ya Aliyun naki”

Tsaki ta jamin”kyale wannan a gefe ina da abinyi”

Dariya ta bani”tofa ko dai hyperlove ya kamaki ba ni da labari”

Kai ta girgiza”Ko ‘daya dama dai bana jin da’di mu kyale batun shi,damuwar ki tafi maganarshi, muhimmanci,yanzu nasan rayuwar da zaku fuskanta idan Kuma koma,kina bani labarin Hajiya maman Abbah”

Nima ‘din sai lokacin na sake tuno wancen rayuwar tamu ta baya gabana fa’duwa ma yayi

Halimah ta dubeni “kinyi shiru kawai da ku’din da Yaya Samir ya baki ki bawa Abbah ku kama haya ko da irin kalar wannan gidanne da kuka kama anan,ni wayarma ki sai data indai zatayi ku’di to me zakiyi da ita din,da ace kin dawo da wuri kafin ranar da mai zaisa ku tashi kuma,nasan dai a gida za’a sha labarin Samir ya baki wasu ku’da’de dai,da ku ‘batar a banza gwara kuyi abinda ya dace dasu”

Ni mamakin tunanin Halima nayi,da ni banyi shi ba
“Hakane Halima,sai yanzu nayi wannan tunanin,wayar ma saidata za’a yi ,tunda da kwalinta Abbah yaja jari da ku’din su kam dama ‘yan uwan Abbah ai sun iya qananun maganganu”

“Yawwa Sumayya,ai Aunty Asma’u ma naji ance taje gwarzo ‘din ai”

Shiru nayi kawai da zancen nata, dan da Aunty Asma’u a cikin ‘yan uwan Abbah gwara babu har gwara ma Abbah Hashim ‘din saboda shi namijine, amma ita ‘din mace ce bata fahimci ciwon mu ba, Faisal ya kawomin ruwa harda lemo na Pepsi nayi godiya,Faisal yana jaddada a rage masa Dan saida yasha wahala har bakin titi wajen siyowa,ko da iyayen Halima suka dawo suka sameni ba abunda suka nunamin,da dare Halimah ta tsokano min firar Hamid,sai lokacin nake hango ya zaiji idan ya samu bana nan ‘din ya zasu qare da shirmen Abbah Hashim,ni sai lokacin naga alamun hauka a tare dashi banda haka ina Sumayya ta koma Fatima kuma, hassadar tashi tama koma hauka,saina ke jin tausayin Abbah da alamun qiyayyarshi a tun farko da ‘yan uwanshi shiyasa Basu qaunar cigabanshi,amma Abbah nasan ‘yan uwanshi shi ko, kullum da ko yaushe suna ranshi da tunaninshi,na rasa yadda zan ‘bullowa lamarin duba da ni ‘din ba wai babba bace tunanin nawa ya kasa tsawan da Zan gama fahimtar Mai ya dace da rayuwata amma nasan addu’a itace mafita…

<< Na Cancanta 18Na Cancanta 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×