Skip to content
Part 4 of 9 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

Kasancewar ta kwanta da wuri ya sanya tana asuba ta kasa komawa bacci, zaman lazimi tayi da ta idar kuma tayi tilawa san da ta kammala har 6 tayi ruwan d’umi da zuma ta sha kafin  ta shirya cikin wata farar top da ash d’in track suit, bak’in joggers ta sanya tana tufke gashinta ta rufe shi cikin bak’ar hula. Jogging take son fita don saurin gajiyar nan da take yi tasan ba komai bane face rashin motsa jikin da ta kwana biyu bata yi ba, har nauyi-nauyi takejin jikinta na mata.

Fitowa tayi zuwa room d’in Hajjah a dadduma ta tarda ta, zama tayi gabanta cikin sanyin murya tana gaisheta da ka amsa mata ba tare da ta bud’e baki ba. Sanin in tana lazumi bata son magana ya sanyata nufar k’ofa tana ce mata ta fita motsa jiki, tana fita ta ciro iPod d’in ta ta mak’ala a kunne tana sanya wak’a a wayarta ruwa mara sanyi ta d’auka a kitchen kafin ta fita.

Tun daga gate ta fara jogging taje farkon street d’in ta dawo zuwa k’arshe, ta sake komawa farko daga nan kuma ta mik’i main titi kamar zata fita daga estate d’in. A hanya tana ta had’uwa da d’aid’aikun ‘yan familyn da suma suke fitowa motsa jiki, gaisawa sukeyi kowa ya cigaba da abunda ya fito bata had’u da su Suleim da Zulfaa ba saboda su d’in basa fita motsa jiki har sukan tsokaneta da cewa wai ita d’in da bata da kauri ne take fita motsa jiki to me take son ragewa bata kula su don tasan amfanin motsa jiki ba sai ga mai k’iba ba. Aa kowa ma yana da kyau ya dinga koda 15 minutes walk ne saboda ayi maintaining homeostasis.

A dai-dai Yerwa court ta hango su sanye da armless shirts da dogayen wanduna, basketball suke bugawa cikeda k’warewa yayinda kowannensu ya jik’e jargab da zuwa su uku ne Farhaan Aliyu Yerwa, ElSadeeq Yusuf Yerwa sai kuma Burhaan Abdullah Yerwa wainda suke kusan kai d’aya duk cikinsu Burhaan ne babba don ya girmewa ElSadeeq da kusan 5 months while ElSadeeq d’in ya bawa Farhaan 3 months Sannan ElSadeeq d’in ya fisu haske sosai while Burhaan is bit tall and well built than them.

Tsayawa tayi ta na kallonsu a zahiri a bad’ini kuma Burhaan take kallo yayinda har k’asan ranta son shi yake d’ad’a hank’oro da hauhawa, a jikinshi yaji ana kallonshi waigowa yayi yaganta tsaki yaja a zuciyarshi a zahiri kuma cira idanunshi yayi yana k’wace k’wallon daga hannun Farhaan cike da zafin nama ya daka tsalle yana cilla k’wallon a kwando.

Gwalo yayi musu yana d’aga hannunshi alamar ”I gat it”, yanda yayin kuwa ya k’ara masa kyau a idanunta he looks so adorable kamar ta sace shi. Yippee ta furta da k’arfi ba tareda ta sani ba hakan nee ya ankarar da su Farhaan d’in isowarta wurin, waigowa sukayi a tare banda Burhaan.

Farhaan ne yace ” wai ke har yanzu baki hak’ura da motsa jiki ba ko?, can’t you see that you are  getting slimmer as days goes by?” Ya k’arashe yana isowa gabanta ya rik’e siririn hannunta dake nan as soft as a baby’s, k’wace hannun tayi a shagwab’e tace ” I’m not complaining ai ” ta k’arashe da murgud’a baki.

Harararta yayi yana cewa ” why will you complain?, ko fa kinyi ba riba dole kiyi hak’uri ba k’ibar zakiyi ba”. Turo baki tayi tace ” oho dai a hakan ake gani a rikice kuma ba samu zaayi ba, I know what’s paining you sorry ehn”, juyawa tayi tana gaishe su duk suka amsa da sakin fuska banda Burhaan.

Yayinda shikuma Farhaan ya cigaba da tsokanarshi yace ” ai kema kin sani yarinya,,,,yawwa Lele zo kiji! Guys ina zuwa” Ya k’arashe maganar yana  fitowa yayi daga court d’in, a d’an tsorace ta sa k’afa zata gudu tunaninta ko wayo zai mata. Cafko hannunta yayi yana cewa ” ke matsoraciya, magana fa zamuyi.”

Ajiyar zuciya ta sauke tana tsayawa har tayi k’ok’arin zame hannunta sai dai waigawar da tayi taga dukansu kallonta sukeyi ne yasa ta k’yaleshi don so take shi ma Burhaan d’in yaji kishi.

Shiko kauda kan shi yayi ba tareda yaji ko d’ar ba hasalima yafi bada cewa shima Farhaan d’in sonta yakeyi, mace d’ayace yake kishin yaga an tab’a ta which is none other than Suleim ko Farhaan kuwa da suka fito ciki d’aya kishinshi yake ji akanta balle random family guys. Tsayawa da wasan sukayi zama yayi ya nemi ruwa yana mai goge zufan da ya wanke masa fuska.

Tafiya suka fara towards the direction d’in gidan Hajjah, sai da suka d’anyi nisa ne ta k’wace hannunta tana cewa ” kace zamuyi magana, amma ka matse min hannu kana cin zalina.” Tsayawa yayi yaci serious yana cewa ” it’s about my friend Khaleel, He’s been pestering me about you jiya da kin ganshi a office d’inki ni na hana shi saboda dai i don’t know whether you are single or in a relationship.”

Yanda yai maganar sai da k’irjinta ya buga, she’s single yet taken saboda tana hangen future’n ta da Burhaan. On the other side kuma Khaleel is a nice guy kana shi ma kyakkyawa ne dai-dai misali kuma yana ji da lokacinshi amma kuma ba zata iya accepting soyayyar shi ba, don in tai haka kamar ta gina katanga mai fad’i ne tsakaninta da Burhaan which will definitely be the last thing she could think of.

Ajiyar zuciya ta sauke cikeda rashin madafa tace ” I’m in a relationship, ka bashi hak’uri kawai.” Kallonta yakeyi kawai don bai wani yarda da abunda tace ba she’s in a relationship amma ko Zulfaa bata sani ba?

Don jiyan nan sunyi magana da ita akan Khaleel d’in bata ce tana da saurayi ba sai ma murnan da tayi harda cewa ” finally,,,Lele zata fara soyayya” kai to ai har ElSadeeq ma ya san da maganar kuma bai ce tana da tsayayye ba  to me hakan ke nufi?, ko dai Khaleel d’in ne bata so? Well that’s understandable ko dai ya bawa Khaleel d’in number ta in yaso suyi magana ne?

Cewa yayi ” wow who’s the lucky guy then?”, girgiza kai tayi tace ” soon zaku ganshi.” Kallonta yayi studying her da kyau sai dai kuma facial expressions d’inta ya b’oye komai hakan yasa he couldn’t point a finger to what’s going through her mind, but zuciyarshi yafi bashi cewa “she’s not saying the truth” murmushi yayi mata yace ” Masha Allah, Allah ya tabbatar da mafi alkhairi a tsakaninku barin koma ki gaida Hajjah kafin mu shigo.” Ameen ta amsa har ranta tayi dad’in adduar da yayi mata, daga haka ta wuce shikuma ya koma inda ya baro su.

Jogging d’in ta taci gaba har ta karaso gate d’in gida , turawa tayi ta shige tana shiga ta cire jacket d’in track suit d’in nata saboda muguwar zafin da ta fara ji babu kowa a harabar gidan don haka a tsanake ta wuce cikin parlorn dake mugun k’amshi lumshe idanunta tayi jin jikinta yana saki, d’akin ta ta nufa direct toilet ta wuce man zaitun ta fara had’awa da lalle ta shafe kanta dashi har scalp kafin ta sanya bonnet a kanta.

Ta shafe face d’in ta da face mask na snake na kamfanin Hemani, ruwan wanka ta had’a mai mugun k’amshi da d’umi ta shige ciki. Har cikin k’ashinta take jin ruwan ya na ratsawa, ta dad’e a ciki kafin ta wanke gashinta tayi wanka ta fito bata d’aura towel ba sai da ta kunna wata burner ta sanya turaren Halud a ciki ta tsaya a kai tana mai rufe jikinta da wata towel mai girma sai da ruwan jikinta ya tsane tsaf yayinda k’amshin ya samu wuri ya mannu a jikinta kana ta d’aura towel k’arami ta fito

Ko a gaban madubin ma ta jima mulka wannan mittssika wancan fesa wancan, Sannan tayi blowing gashinta ta bishi da kalolin mayukan gyaran kai tayi waxing sannan ta tufke shi in a ponytail bayan tayi spraying k’arshen da red hair dye. Murmushi tayi tana kallon kanta she looks quite adorable dukda bata yi kwalliya ba shiryawa tayi cikin wata mint colored Versace peplum gown bata rufe kanta ba ta fito lokacin 9 am tayi har rana ta fara fitowa.

D’akin Hajjah ta shiga ta tarda ta ta kabbara sallahr Duhaa hakan yasa ta koma baya, art room d’inta ta nufa don she too missed zane. Tsayawa tayi ta d’auki rigar aiki ta sanya kana ta fara abunda tafi k’aunar yi fiyeda komai, with passion and determination. Zanen abunda yazo kanta ta fara wato heart ta zana mai matuk’ar girma saidai ba irin yanda muke zanawa ba.

Aa wannan heart ce ta gaske zallahr tsokarta, a yanayin kamar an yanka ( dissection or cross section) cikin gwanancewa ta lank’wasa edge d’in irin bud’eta akayi sannan a ciki ga jijiyon kai jini da ma papillary muscles dake ciki, sai kuma daga right atrium ta zana ido mai matuk’ar kyau but full of blood haka jinin yana kwaranya har yana jik’a heart d’in ya kuma zubo k’asan zuciyar.

Gyaran zanen ta cigaba dayi tana mai k’ok’arin pouring heart d’in ta a zanen da takeyi don ji take tamfar ana sauke mata nauyin da zuciyarta takeyi a kanshi ne, a duniyar nan babu wanda yasan halinda take ciki sai ita d’in da mahaliccinta in ta bud’e baki kuma ba wanda yake sauraranta sai ma wallenta da ake gani akan ta zurma jiki cikin abunda ba zai tab’a fissheta ba.

But her board is always listening to her keenly  without questioning or judging her and her brushes and paints are doing more than justice in pouring out what’s in her mind, they are the friends she always longed for. Duk girman damuwarta daga alqurani sai brush d’in ta suke yaye mata su, bata cika zama da Ummu ba saboda rayuwarta rabi da kwata tayi tareda ita.

Kana tana tsoron bud’e love life d’inta gareta ba wai tana tsoron Ummun bane Aa bata son ta sanyata a damuwa ne, don muddun taji ba zata samu sukuni ba musamman da ya zama k’oshin wuya take fama da (wato son maso wani) Hajjah ce kawai ta san me take ciki itama dai-dai da rana d’aya bata tab’a supporting d’in ta ba kullum cikin dakushe mata burin takeyi hakan ya sanyata yin gaba-gad’i ta sanar masa soyayyarta da har yanzu kuma bata nadamar hakan…

Tayi nisa a tunaninta har bata san shigowar shi cikin d’akin ba sai ji tayi an dafata da hanzari ta waigo, a d’an tsorace don ita d’in matsoraciya ce. Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa ‘ Hey there ‘, kallonta yayi cikeda nazari ba tun yau ba ya tabbatar tana da damuwa amma bata tab’a sanar masa ba kuma bata  tab’a ba shi k’ofar hakan bama .

Ko ya tambaya amsa d’aya take bashi wato ba komai, har fushi ya tab’a yi akan hakan amma da kanshi ya sauko don ita d’in mai wayau ce ta kuma iya shanye damuwa ba tareda ta bari wani ya lura ba. Shi ma d’in don ya mata kyakkyawan sani ne da ba zai tab’a k’aras da damuwarta ba, har Suleim sai da ya tambaya ko Nadeefah d’in tana da wata matsala amma baiwar Allahn ta shaida masa k’alau take. (She promised komai rintsi ba zata tab’a gayawa wani halinda Lelen take ciki ba, shiyasa ma bata so ta tunkari Burhaan da maganar ba).

A hankali yace “are you okay Nadeefah?” kai ta gyad’a tana cigaba da abunda takeyi. Girgiza kai yayi yace ” no you are not, Nadeefah Yousuf !” Murmushi tayi jin yau harda kiranta da sunanta ba wai don basa kiran kansu ba sunayen yankan su bane wani lokacin ma complete name suke kira musamman a lokacin nishad’i.

Tace ” me ka gani Yaya Sadeeq?” Ya amsa da ”many things Lele, you are not yourself kamar akwai abunda yake damunki kina b’oyewa open up to me I’m your brother Nadeefah!” Murmushinta ta fad’ad’a jin yadda yayi maganar  cikeda damuwa, tabbas yayyinta suna sonta son da basa had’a shi da na kowa wanda ya samo asali da kasancewarta mace d’aya tilo a tsakar gidansu.

Sai dai ba zata iya shaida masa damuwarta ba, ta ya zata dubi tsabar idanun Abubakar Yusuf Yerwa ta shaida masa cewa ” Abokinka, our cousin Burhaan Abdullah take so”? Haba da kunya ai. A hankali cikeda k’arfin halin shanyewa tace ” I promise you babu abunda yake damu na, in da akwai ai da na shaida maka ko ka manta cewa Nadeefah bata b’oye maka damuwarta?”

Gyad’a kai yayi ba don ya yarda ba sai don yanda take insisting, amma ya k’udure shi da kanshi zai bincika he won’t give up har sai ya gano matsalar amma for now zai share.

Kallon d’akin yayi with so much adoration yace ” kullum sai k’ara k’warewa kikeyi a zane kamar bada hannu kikeyi ba,,,kuma har yau ank’i zana ni.”

Dariya ta sanya jin yanda ya k’arashe da shagwab’a tace ” ni na isa in k’i zana ka, kawai shiririta na sanyawa zanen sai na fara sai in tafi wani abun buh, I promise nan bada jimawa ba zan gama.” Cikin jin dad’i yace ” toh a bani in gani mana, in da gaske ne”, cewa tayi ” ank’i wayon sai na gama zaka gani” dariya yayi ya samu wuri ya zauna yana ciro wayarshi, pics  ya fara yi mata  tana jikin zanen da videos komawa tayi tayi retouching sannan tayi abunda tafi so wato inscription ta rubuta ” if hearts get eyes then I’m pretty sure that mine is shedding tears of blood and you are actually the reason why…..Aorta

“Da kalan salon bescript  na zallar calligraphy.

Duk yanda yaso ya karanta mai ta rubuta ya kasa, da ya tambayeta cewa tayi ” kawai quote ne ta rubuta” tab’e baki yayi don ya san artists da kichifi, yana zaune har ta kammala tare suka fito bayan ta kulle design d’in yau bata d’auki hoton ba don ElSadeeq ya gama mata komai kafin ma su fito yayi airdropping mata.

A zaune suka tarda Hajjah tana kallo, da sauri Lele ta fad’a jikinta tana zuba shagwab’a cikeda kulawa ta biye mata tana shafa kanta tace ” ke dai baki son d’ankwali…yau ba zaku je office bane hala?” Ita fa sai yanzu ta tuna ba d’ankwali a kanta tace ”

Hajjah na manta shi a d’aki,,,,,zan fita yanzu ma breakfast zanyi in wuce.”

Shiko cewa yayi ” zan fita da sai after 2, wani site zanje duba aikin sanda aka fara bana nan” tace ” tohm ku tashi kuje dining breakfast yana jiranku ni kam azumi nakeyi” Ita fa ta sha’afa cewa yau Thursday da ta tashi da azumin ita ma a tare suka tashi ko a dining d’in ma halinta tayi na tsakurar abinci omelette d’in ne ma taci sai fries nan ta bar musu peppersoup d’insu ba tare da ta wani ci da yawa ba.

Shigewa d’aki tayi ta fito da cream colored veil haka bag da flat shoe duka na Vinci bata sanya hula ba sai dai ta nad’e gashin ta kuma yi rolling yanda baa ganin gashin nata sai ta gaba wanda dama ko ta sanya hula bai rufe shi. Sallama tayi musu tai wucewarta inda suka rakata da idanu da addua, fitarta ne Sadeeq d’in ya fara tambayar Hajjah ko akwai matsalar dake damun Lelen amsar d’aya ce dai babu wata matsala. Hakan yasa ya bar maganar a wurin suka dasa wata hirar na bak’in yau.

Yau ma she’s so committed don daga wannan sai wannan hakan itama an mata lalle a hannu kawai, duk da dai ta san yau sai ta bani da mitan Hajjah akan lalle a hannu ko k’afar budurwa bata tanka ta don ita bata ga dalilin hana ta lalle ba haka kawai sai kace a can. Ita kad’ai take ta mita a ranta, ko da rana sauka tayi a Yerwa closet tayi lunch tare dasu Zulfaa sai after 3 ta koma office d’in nata.

Bata yarda ta kai ko Magrib ba, haka ta shaidawa maaikatan wurin kar a wuce 7pm baa rufe ba don bata son yawan overtime d’in da suke kwanannan tunda dai baya cikin agreement d’in da suke dashi da maaikata sai dai in lalurar hakan ya gifta. Wanda bata san yafi yi ma maaikatan dad’i ba, don ba k’aramin samun return sukeyi mai tsoka ba kasancewar payment d’in by hour sukeyi.

5:30 ta sauko k’asa cikin tafiyarta na cat walking, a tare suka sauko da Suleim wacce take bata labarin maganar da sukayi da ElSadeeq akan kai maganar su ga Baba Tijjani don so yakeyi a meeting d’in watan nan da zaayi nan da 2 days a gabatar da neman aure in so samu ne ma a sanya bikinsu. Murna ta tayata har zuciyarta, sun dad’e suna maganar kafin kowacce ta shige motarta zuwa gida.

Shigowarta layin ne ta ga gidan da yake farko a rukunin gidajen an bud’e gate d’in shi , a mamakance ta tsayar da motarta don ta tabbatar dai masu gidan ba sa nan in kuma kaga an bud’e shi to sun dawo ne. Zaro idanu tayi sai kuma ta sanya dariya tace ” what a surprise?!, wato ni aka shammata”, da sauri ta juya akalar motarta tayi honk mai gadi ya lek’o ganin wacce ke honk d’in ne ya sanya shi washe baki tare da wangale mata gate d’in ta shigar da motarta ko sauraran mai gadi dake jero kirari bata yi ba ta nufi parlor tana k’walla kiran “Ummulkhairi” kamar wata yarinyar goye…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nisfu Deeniy 3Nisfu Deeniy 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×