Skip to content
Part 11 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Shiru bai taba mishi yawa ba, lokutta da yawa ma yana jin yayi mishi kadan, ko shi kadai ne zaune a bangaren su cikin gida, sai ya dinga jin hayaniya a cikin shirun dakin, karar agogo, fanka ko AC din cikin dakin, ko wani kwaro da ba zai ce ga inda yake ba, hakan kawai na hana shi sukuni, shisa ya siyi abin toshe kunne, yana da su wajen kala hudu. Su kansu basa taimaka mishi, idan yasa duk kananun hayaniyar sai ta daina isa cikin kunnuwan shi, sai kuma ya dinga jin surutun da yake wanzuwa tsakanin kwakwalwar shi da zuciyar shi.

Yana rasa a cikin mutane shi din wanne iri ne? Ya kanyi tunanin ko irin shi guda nawa ne, ko ya suke ji da hayaniyar da take cikin yau da kullum? Musamman idan ya hasaso kasancewar su cikin halin rashi, babu wadatar da zasu samu wajen kebewa su kadai. Amman yau shirun da yake cikin motar yayi mishi yawa, ba dan gilasan suna kulle ba, idan shi kadai ne zai dinga jin karar sauran motoci harda ma kukan tashi motar. Sai dai duk lokacin da zai zamana shi da Madina ne a zaune cikin mota, ko kuma tana gefen shi baya jin kowacce irin hayaniya.

Asalima banda muryarta da dariyarta babu wani abu da yake isowa kunnen shi, ko bata magana kamar ganinta na saka komai yin shiru ne. Sai dai yau shirun nata yayi mishi yawa, tunda ta fito ta gaishe da shi ta koma cikin mota ta kwanta kamar marar lafiya, har suka fita daga layin suka hau titi ko motsi baiga tayi ba, lokaci zuwa lokaci yana kallonta. Matsalar bai iya hira ba, bai taba fara hira da wani ba, ko a cikin yan gidan su kuwa, banda gaisuwa sai dai in kaine ka tambaye shi wani abin, ya rasa me ya kamata yace mata.

“Lokacin damuna ne ake noma tumatiri ko?”

Tambayar ta kubce mishi tana saka Madina juyo da kanta tana kallon shi na wasu dakika cike da mamaki, shima dan raba idon shi yayi daga titi yana kallon ta.

“Shine abinda ya fara zuwa kai na…”

Ya fadi yana maida hankalin shi kan titi, wata irin dariya Madina ta kwashe da ita.

“Da gaske Hamma?”

Ta tambaya, kafadu yadan daga yana rausayar mata da kai.

“Kinki mun hira… Bansan me zance ba.”

Yayi maganar da dukkan gaskiyar shi, hannu takai ta gyara gilashin fuskarta tana sauke numfashi, har lokacin da murmushi a fuskarta. Kawai ba zata ce ga asalin abinda yake damunta ba duk satin. Ta san zazzabi, da shine zata gane, babu inda take ji yana mata ciwo, kawai tana jin kamar dai akwai wani abu da babu a cikin rayuwarta a satin.

“Bajjo zai yi aure.”

Daada ta fada mata, ta zabi ta fada mata lokacin da ta cika bakinta da ruwa tana shirin hadiye wa, ta kuwa sarke tana tarin da ta kusan shafe mintina biyar bai tsagaita mata ba, idanuwanta duk sun tara hawayen wahala.

“Cikin satin nan idan Allah ya bamu aron rai.”

Daadar ta sake fadi, ko da taso yin wata tambaya bata san ta inda zata fara ba, tambayoyin nata da yawa, wata na danne wata haka suka dinga tasowa cikin kanta. A lokaci daya kuma tana nemar ma maganar wajen zama a tare da ita cike da son gane me hakan yake nufi da tata rayuwar ko wata dangantaka da take tsakanin auren na shi da ita. Shisa sai komai yayi mata yawa, abu daya ne take jin zata iya cewa, kamar Nawfal din bai kyauta mata ba, kamar daga bakin shi ya kamata ta fara ji. Kamar ya kamata ace tasan maganar.

“Kunyi shakuwar da zai gaya miki zaiyi aure ne?”

Wata murya ta tambayeta, ta so tayi gardama, taso ta zayyano ma muryar shekarunta na kuruciya, lokuttan da Nawfal yake daukota akan bayan shi daga makarantar islamiyyar su zuwa gida kamar bata da wani nauyi, lokuttan da take jiran zuwan shi dan ta zayyana mishi duk wasu kananun bukatunta ya kuma cire kudin shi ya biya mata su. Sai ta tuna da shekaru biyun da suka ja layi a tsakanin su, abubuwa da yawa zasu iya fara a cikin awanni biyu, balle a tsallaka awannin da suke cikin ranakun da suka shude tare da shekara biyu.

“Ma shaa Allah. Allah ya tabbatar da alkhairi.”

Tace maimakon furta ko da daya daga cikin tambayoyin da take da su ne. Hidimar da ta fito da ita ta cigaba dayi, ba dai tasan dalilin Daada na binta da wani irin kallo mai cike da ma’anoni ba. Ba zatace tausayawa kawai ta gani a cikin kallon ba, kamar Daada na son sanar da ita auren Nawfal din yana da alaka da rayuwarta ne, ta kasa fahimtar kalaman da Daada ta zabi tabar su cikin idanuwanta maimakon ta furta mata su. A ranar da ta shiga dakin ta, bayan ta zauna ta dauki agogon Nawfal kamar yanda sabonta yake sai ta tsinci kanta da saukowa daga kan gado tana neman waje ta jefa agogon a ciki.

Har yau da take zaune a cikin motar Salim da yazo daukarta zuwa restaurant din da suka yanke hukunci zuwa yasu-yasu dan gudanar da yar walima ta taya Nawfal din murnar auren shi da aka daura a safiyar Asabar din ba zata ce ga dalilinta na adana agogon ba. Hannun Salim da taji a gefen kuncinta na sata saurin janye jikinta kamar wadda wuta ta taba, sake mika hannun shi yayi kamar bai ga yanda ta hade da murfin motar ba, ji yayi babu zazzabi a jikinta. Sannan ya janye hannun shi yana gyara zaman shi yana fadin, “Shirun ki yayi mun yawa.”

Numfashi ta sake saukewa a karo na biyu.

“Banda labari ne fa… Yau zan missing karatu a islamiyya, bana fashi in ba rashin lafiya ba sai bikin Adee, zasu ga banje ba yau ma kuma ban fada ba.”

Kai ya jinjina.

“Za su dake ki ne?”

Saboda tunanin wani zai taba lafiyarta na sa jikin shi daukar dumi da wani yanayi na bacin rai. “A’a, ba su cika dukan fashi ba inba kana yawan yi ba.”

Duk da haka hankalin shi ya ki kwanciya

“Kin tabbata?” Ya yi tambayar cikin harshen turanci .

“Na tabbata.”

Ta bashi amsa cikin harshen itama, yana shan wata kwana ya dan rage gudu alamar yana son samun damar da zai tsallaka titi ne, tana kuma iya ganin sunan restaurant din Tasty Corner. Sai da ya tsallaka ya samu waje yayi ajiye motar yana kashewa tukunna take kara ganin kyawun restaurant din tun kafin ma su shiga. Da yake banda makaranta babu inda take zuwa, sai nan cikin unguwar su, sai kuma gidan Julde da shima tana dadewa bataje ba. A garin Kano tsaf zaka siyar da ita. Babu inda ta sani, yanzun ne ma da Salim ke yawon dauko ta daga makaranta yakan biya wani wajen ya yi mata siyayya, har wani wajen saida litattafai sukaje da bata san a ina bane ba, amman ya yi mata kyau matuka.

Da kan shi ya zagaya ya bude mata murfin motar ta fito. Sai lokacin ya kalli kayan jikinta, jeans ne baki, kamar yanda ta saba ta nannade shi har kwaurinta ya dan fito, sai fararen kambas, riga ce ta sanyi mai dogon hannun da taja baya, itama farace kamar hijabin kanta. Ta dora wata farar hular sanyi a saman kanta. Murmushi ya yi yana tsayawa a gabanta yana kara mamakin gajartar Madina, da kadan kanta ya wuce cikin shi, kama hular ya yi yana cire ta daga kanta ya duba kamar mai son gano wani abu a jiki.

Murmushin dai ya kasa barin fuskar shi har lokacin, gyara hular yayi a cikin hannun shi yana dorawa saman kanta kafin ya gyara mata ita saman kanta, ganin yanda take kallon shi yasa shi amfani da dan yatsa ya tura mata gilashin da yasan gab take da dago nata hannun ta gyara mishi zama.

“You look like a Mug.”

Salim yace muryar shi dauke da wani irin yanayi da yake jin fitowar shi daga zuciyar shi, kai Madina take girgiza mishi tana kokarin danne dariyar da take son yi saboda hada tsayinta da kofi da ya yi.

“Ba zaka fara kirana da Mug ba Hamma.”

Girar shi daya ya daga mata. “Gargadi ne?”

Kai ta girgiza da sauri tana saka shi lumshe idanuwan shi yana bude su a kanta.

“Mug, it’s then… Muje.

Juyawa tayi kuwa, wani murmushin na kara kwace ma Salim, da gaske tayi kama da yan kofinan nan masu kyau da ake zuba coffee a ciki, masu murfin da marassa murfi, amman masu kyan cikin haka yake ganin tsayinta a gaban shi

“Mug”

Ya furta dai-dai kunnuwan shi da murmushi a labban shi, har takai kofar wajen ta juyo tana kallon shi da tunanin abinda ya tsayar da shi. Taku biyar ya yi ya karasa inda take suna shiga tare, can wani teburi da yake karshen wajen ya hango su Khalid, sai kuma hannuwan Adee duka biyun da take daga musu kamar yace bai gansu ba. Baima san me yasa mijinta ya bar ta fitowa ba duka sati daya da aure. Dariya take tana sake daga musu hannuwa. Dakuwa Salim ya yi mata daga inda yake yana kallo ta sake kwashewa da dariya kamar wadda ya bawa kyauta.

Suna karasawa tana tashi daga wajen da take zaune ta kama hannun Salim din da yake kokarin kwacewa yana daure fuska, “Wallahi nayi kewar ku sosai.”

Ji tayi kamar tayi wata bakwai bata gansu ba, “Sake ni dalla.”

Tabe baki Adee tayi, matsalar Salim ba’a mishi gwaninta, tana zame hannuwanta daga nashi ya daga ya dillar mata bakin da ta tabe mishi.

“Dan kinyi aure zaki mun rashin kunya.”

Dafe labbanta tayi babu shiri, “Ouchh… Hamma.”

Kallon da yayi mata yasa ta koma ta zauna, kujera yaja shima ya zauna yana dan kara janta gaba, kafin ya kalli agogon hannun shi, “Minti talatin…”

Ya fadi yana kallon su, yana da hidimar da zaiyi, ko bashi da ita baida hirar da zai yi da su, hayaniyar zata dame shi. Gara yaci abinci ya bar su suyi hirar su cikin nutsuwa. Kallon juna Khalid da Nawfal suka yi, dan sunyi gulmar shi, babu ma wanda ya kawo zaiyi minti talatin din duk a cikinsu.

“Ni nace maka Hamma ba zai minti biyar a wajen nan ba,” cewar Khalid.

“In za’a iya mishi takeaway din duk abinda yake so a kasa da minti biyar ba zai kai ba.”

Nawfal ya kara, basu taba tunanin zai zauna a waje irin haka yaci abinci ba

“Nasan kunyi gulmata.”

Ya fadi kasan makoshi yana duba menu din da waiter din wajen ya kawo mishi bayan ya dan daga hannu cikin alamar kira, dankali da kaza ya zaba sai bakin lemo yana kallon Madina da tunda ta zauna idanuwanta na kan Nawfal, bata ganshi ba tun da akayi mata zancen bikin, bai kwana a gidan Daada ba, sanda yazo tana makaranta sai dai inta dawo Daada tace mata Nawfal ya zo. Yanzun da ta ganshi kawai sai take jin kamar abin wasanta da ta dade tare da shine aka fisge daga hannun ta.

Kai tsaye ba zata ce ranta ya baci ba, amman kuma bata farin cikin da kwacen, wani yanayi ne a tsakanin abu biyun da bata san wacce kalma zatayi amfani da ita wajen fassara shi ba.

“Madina…” Salim ya kira a hankali yana dan daga mata Menu din da yake hannun shi bayan ta kalle shi

“Abinda duk aka baka.” Ta ce cikin sanyin murya, su Nawfal ya kalla, kowa ya fara jero abinda za’a kawo mishi.

“Madina yaushe zaki zo gidana? Kinsan ina fushi daman, baki je kaini ba, na kula ai.”

Murmushi Madina tayi, har ranta tayi niyyar zuwa kai Adee din tunda harda Daada, a wajen motocin daukar amaryar taji an riko mata hannu ana janta, kafafuwan shi ta fara kallo ta gane waye,

“Hamma…”

Ta kira, bai amsata ba ya cigaba da janta har suka inda motar shi take ya bude murfin yana sakin hannunta, yanayin fuskar shi yasa ta shiga batare da tayi musu ba, ya ja motar da bai tsayar ba sai a kofar gidan Daada, nan suka yi zaman su a ciki suna hira, ko tace tana mishi surutun da yake amsawa dai-dai. Har fita suka kara yi ya siyo musu tsire mai yawa da lemo.

“Zan zo, Hamma zai kawo ni. Kibari kunshin ki ya karasa gogewa, sai ki kira Daada kinga idan nazo sai in miki sabo.”

Kai Adee ta jinjina.

“Kin kusa ki wanke laifin ki.”

Yar dariya tayi tana kallon Nawfal.

“Hamma Ango.”

Hararta yayi. “Yanzun ne zaki kula ni? Bana so.”

Hannuwanta ta hade waje daya cikin ban hakuri. “Ance angwaye basa fushi fa ko Hamma Khalid?”

Dariya Khalid ya yi.

“Ni zan shiga fadan ku? Ku shirya ku ware ni yanda kuka saba? Babu ruwana, sai dai babban Yayaa.”

Ya karasa maganar cikin sigar tsokana. Wani kallon kashedi Salim ya watsa mishi yana saka shi gyara murya.

“Idan na taso saina mare ka”

Salim ya fadi yana sa Adee kwashewa da dariya.

“Me nayi ni kuma?”

Ko da ba’a fara kawo musu abincin su ba yasan ba amsa zai samu ba. Hira ce ta barke tsakanin Nawfal, Khalid da Adee, Salim abincin shi yake ci duk da maganganun su da yake ji har cikin kwakwalwar shi, Madina ma abincin take ci tana tsintar dankalin dai-dai. Salim na kallonta ta gefen idanuwan shi, dan ture plate din shi yayi yana jan nata bai damu da kallon mamakin da take mishi ba, wuka ya dauka yana yayyanka mata cinya guda biyu kanana yanda zata iya dauka kafin ya tura mata plate din batare da yace komai ba yaci gaba da cin abincin shi.

Lemon da yake gabanta ma shi ya bude yana zuba mata a kofi ya tura mata kusa da ita. Da ya gama cin nashi abincin ma ita yake kallo. Lokaci zuwa lokaci takan dago su hada ido, ta saba ciye-ciye a gaban shi, tasan dai idan ta ajiye cokalin magana zai mata tunda ba wani ci tayi ba, ita kuma tana turawa ne badan tana gane dandanon abincin a bakinta ba, sai da taci kusan rabin naman da yayayyanka mata tukunna ta ajiye cokalin a ciki tana dan ture plate din. Ganin girar da Salim ya daga mata cike da alamar tambaya ya sata fadin,

“Na koshi Allah, tuwo Daada tayi mana.”

Baice komai ba ya mike yana karasawa inda zai biya kudin ya kuma bama Madina damar yi musu sallama, idan ya barta zasu mayar da ita gida ya sani, bai san ko tana so ta zauna ba, ba tambayar ta zaiyi ba. Yanda suka zo tare haka zasu koma tare, saboda hakan yake jinyi badon yana da wani kwakkwaran dalili ba.

“Allah yasa alkhairi Hamma, Allah ya kawo zuri’a dayyi ba.”

Madina ta fadi tana rasa dalilin da yasa take jin wani iri. “Zan zo anjima.”

Nawfal ya amsa, kai ta jinjina mishi tana mikewa, Khalid ne ya kalle ta da fadin,

“Ki bari mu tafi gabaki daya mana, ba sai mu sauke ki ba.”

Kai ta girgiza mishi.

“Hamma zai ce a’a.”

Dakuna mata fuska Khalid ya yi.

“Ka kyaleta Khalid, kiyi tafiyar ki Madina, saina kira Daada…”

Numfashi ta dan sauke bata ma amsa ba ta juya.

“Kai ina ruwan ka? Baka ga tare suka zo ba?”

Ruwa Nawfal ya kurba ya hadiye sannan yace,

“Ni kadai naga Hamma ya yankawa Madina nama?”

Dariya Khalid ya yi, “Wallahi kiris in shake da taliya… Anya Hamma?”

Kai Adee ta girgiza, “Kuna da bala’in gulma yaran nan, ina ruwan ku? Sai na fada mishi.”

A tare suka kalle ta, dan kasa tayi da murya kamar tana tsoron Salim din zaiji ta

“Amman da gaske me yake faruwa ne?”

Kallon ‘maganar da nake yi kenan ai’ Khalid ya yi. Hirar suka dan karayi kafin su saki zancen suna kama wani tunda sun san koma mene ne ba zai wuce su ba, suna zaune zai zagayo kowa ma ya gani.

*****

“Yanzun wanne mai hankali ne ya dauki yarinya ya ba Bajjo?”

Saratu ta fada tana tabe baki.

“Mai irin hankalin wanda ya daukeki ya bani.”

Julde ya amsa ta, amsar kuma tayi mata zafi.

“Ubana kenan?”

Bai ce komai ba, sakon ya isa baya bukatar jan magana kuma.

“Idan wulakanci abinyi ne ka cigaba da wulakantani Julde, Allah ya baka sa’a, hirar arziki ma ba zan taba samu inyi da kai ba saika gasa mun Magana.”

Shirun dai shi ya kara yi mata yana cigaba da neman kayan da yake son sakewa dan ya fita yabar mata gidan ma gabaki daya, a gajiye ya dawo daga Abuja tunda a can ya kwana aka daura aure da safe ya tsaya wata hidima da ta shafi kasuwan cin shi tukunna ya juyo.

“Kuma sanda na aure ka aika girmi Bajjo, shekarar ka wajen ashirin da biyar.”

Gani tayi da gaske bashi da niyyar amsata, wasu hawaye taji masu zafi sun taru cikin idanuwanta. Duk kawayen ta haka suke cewa tayi sa’a, mijinta ga arziki ga kyau.

“Ko yanzun mijinki yaso zai auri budurwa wallahi da zata bi kyawun shi”

Wata kawarta ta taba fada, dan yanzun ma sun raba jaha, daina sakar mata fuska tayi tun da aurenta ya mutu, saboda matar ba karamar gogaggiya bace ba. Ko da aurenta ma duk yanda kuke karka fara yaba kyawun mijinta yanzun zata daina sauke girarta a gabanka. Wani irin kishin shi takeyi na ban mamaki, shisa duk idan taga zai fita haka take jin kamar baza’a waye safiyar ranar da ita ba saboda bacin rai. Da mutanen da suke mata kallon tana zaune a wannan tankamemen gidan tana kuma auren namiji kamar Julde sun san me take hadiya da ta daina basu sha’awa.

Ita a bakin yaran da ta haifa da cikinta ma bata ji zancen cewa Nawfal zaiyi aure ba. Yara kamar ba daga jikinta suka fito ba, yanda suke nanike ma Nawfal din yana bata takaici. Sai jiya da Julden zai tafi Abuja yace mata, “Gobe da safe za’a daura auren Bajjo.”

Tambayar duk da tayi mishi kuma bata samu amsa ba. Haka ya tsallake ta ya wuce, son da take mishi ne abinda ya sata yi mishi addu’ar dawowa lafiya. Sai Adee ta kira, itace take fada mata kowa zai aura da inda suka hadu. Duk da bangare mafi rinjaye a zuciyarta na tare da bakin cikin kalar matar da ya samu, sauran karamin kashin yaji dadi da kuma fatan su karata can, ta rike shi karya dawo. Kar ya sake waiwayo su, inda yake ya zauna kamar Bukari, danma yanzun zamani ya canza ko ba’a ga fuskar juna ba za’aji muryoyi, da tace aji shi dif, ayi zaman makokin da babu gawa idan anyi cigiya an gaji.

Ya zamana sunan shi ma zaiyi ma kowa nauyin ambato kamar yanda na mahaifin shi yayi. Wannan shine fatanta, Nawfal ya yi ma rayuwar ta da ta ahalinta nisa.

Wannan karin ma kaddara ce ta riga fata.

Kaddarar da take bibbiyar mutanen da ta kira ahalin ta da Nawfal din da ta zabi ta ware a cikin su.

Bata sani ba. Bata san shi din haske bane a tare da su.

Bata san shi zai zame musu katanga a lokacin da tarihi ya maimaita kan shi ba.

“Sai da safe.”

Julde ya fadi yana nufar kofa, hannu tasa tana share hawayen da ya zubo mata. Yana fita yaja mata kofar, a jagule yake jin zuciyar shi harya fice daga gidan, inda ya tsaya ya siyi lemon zaki yaji wani yace,

“Mero!”

Sai da zuciyar shi ta nemi fitowa daga kirjin shi saboda tsallen da yaji tayi, da sauri ya waiga yana ganin yarinyar da bata wuce sa’ar Adeen shi ba da take tattare kwanoninta da alama abinci ta gama siyarwa a wajen, lumshe idanuwan shi yayi ya bude su.

“Maigida ga canjin ka.”

Mai lemon ya fadi, karba Julde yayi ya karasa motar shi ya zauna a ciki yana dora kanshi da abin tukin, har lokacin numfashi yake fitarwa cikin kokarin dai-dai ta bugun da zuciyar shi.

“Naji maganganu kala-kala akan ka, wanda duk yake tunanin ya isa dani yace mun kar in aure ka… Ya zanyi da zuciyata Julde? Ya zan fito musu da ita su fahimci hakuri da kai baya cikin zabin da nake da shi?”

Kalaman Mero suka dawo mishi kamar tana cikin motar a tare da shi, sake runtsa idanuwan shi ya yi.

“Na yadda kowanne rai da nashi kaddarar, kai ne kaddara ta Julde…”

Ya rasa yanda lokaci zai zama mai adalci kuma marar adalci a lokaci daya, yanda yake wucewa batare da ya jira kowa ba shine babban adalcin shi, amman yanda idan ya wuce baya dawowa kowa a wajen Julde hakan rashin adalci ne, ya zaiyi da kadan daga cikin kurakuren da yake jin zaiso ya sake samun aron lokaci dan ya sauya zabukan da yayi? Yau bama wani waje yake son komawa ba, rana daya ce, dakika ne kayadaddu a cikin ranar da zai sauya amsar da ya bama Mero, so yake ya kalleta ya fada mata ita ce kaddarar shi bashi bane kaddararta.

“Mero tayi aure”

Labarin ya riske shi shekaru hudu bayan rabuwar su, labarin da saida yayi yar karamar jinya a kan shi, hangota da wani, hango rayuwar da tayi da shi tana yinta tare da wani ba zai daina kassara zuciyar shi ba. Shi kadai yake dawainiya da ita a ran shi, ita ta shafe babin shi daga rayuwarta harta bude wani sabon shafin tare da wani. Bai tambayi a ina ko wa ta aura ba, abubuwan da yake gujema cikin sanin masu yawa ne. Da duk rana da yanda yake jin kusancin ta a zuciyar shi yana kuma jin nisanta da rayuwar shi.

Da ya san kaddara ta adana musu shafin sake haduwa a titi daya da ya sauya tunani

In da yasan haduwar da zasu sake yi da Mero zata tono mishi abubuwan da za’a hada da rayuwar shi ta baya da ta yanzun a waje daya daya duba zabukan da yake da su.

Dago kan shi yayi yana sauke wani irin numfashi ya tayar da motar fitilar ta na haske wajen har yana shirin kashe mishi idanuwan daya dan jima da su a runtse, sai da yasa hannu ya murza idanun, duk da haka ji yake hasken kamar yayi mishi yawa.

Da yasan duhun da yake bibiyar shi watakila da ya nemi duk wani haske da zai iya kafin lokaci ya kure mishi.

Kaddara.

Kaddarar dai…

Ya baro tushen shi saboda ita.

Tana biye da shi har wajen da yake tunanin ya boye mata.

<< Rai Da Kaddara 10Rai Da Kaddara 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×