Ya kai mintina sha biyar a ƙofar gidan su Yumna yana kiran wayarta bata ɗauka ba. Hankalinshi ya soma tashi.
Wata yarinya ya gani. Ya aiketa cikin gidan ta kira mishi ita. Sai ta dawo ta ce an ce bata gidan. Yasan ƙarya ne.
Wayar El ya kira. Not reachable.
"Damn..."
Ya faɗi yana mai saka hannunshi cikin sumar kanshi. Ya sake gwada lambar Yumna ɗin. Wannan karon ɗagawa ta yi.
"Kin san me kika yi kuwa? Kin san in na shigo cikin gidan nan abin ba zai kyau ba. Ki fito in kaiki gidan. . .