Tuna Baya (Rayuwar Dawud)
Da zai iya ɗora kalmar 'Perfect' zai kira ahalin shi da haka. Tun tasowarshi bai san wani tashin hankali ba balle ɓacin rai.
Ba masu kuɗi bane su. Sai dai suna da rufin asiri dai dai gwargwado. Don babu abinda suka nema suka rasa ta ɓangaren abinci, sutura da makaranta me kyau dai dai ƙarfin Abbansu.
Yakan yi mamaki in ya ji an ce mata da miji na faɗa. Don bai taɓa gani a nasu gidan ba. Maman shi Aisha da suke kira da Ummi mata ce mai hakuri. . .