Kasancewar gidan cike yake da mutane, don ranar za a kawo lefe yasa duk suka bar gidan. Mamdud da Labeeb gidanshi suka nufa tare.
Suna shiga Labeeb ya shige ɗaki ya kwanta yana jin kamar an markaɗashi saboda gajiya. Sauran sati biyu kenan bikin Zainab don yau ma aka kawo lefe.
Amma gaba ɗaya tun farkon watan babu wanda ya zauna a cikinsu, a je nan a je can. Bai taɓa sanin haka hidimar biki take ba sai yanzun.
Da ya tambayi Mummy kome yasa nashi bikin ba ai hidima haka ba. Dariya ta yi. . .