Sa'adda ya fito daga wanka yana jin wayarshi na ringing bai bi ta kanta ba. Yasan su Asad ne za su azalzale shi. Shikuma sai ya gama shirin shi. Wani sama-sama yake jin shi. Ga wani sanyi da ke ratsa shi da bai da alaƙa da AC ɗin da ke kunne.
Nishaɗi yake ji da ya jima bai ji irin shi ba. Ya kasa daina murmushi har ya gama murza wa jikinshi mai. Nan da awanni da basu shige biyu ba Zulfa za ta dawo ƙarƙashin kulawarshi.
Ba zai iya misalta yanayin da. . .