New VOA Staff
Nasara ta duba screen na kwamfutar kan cinyar ta sosai, sakon email ne wanda ta fidda rai da shi ta kuma manta da shi, tafi shekara da neman aiki da gidan Rediyon VOA sai yau Allah Subhana ya yiwa aikin fitowa, suna kiranta interview na gaggawa nan da kwanaki biyu masu zuwa.
Mikewa tayi bayan tayi printing din takardar akan takarda, ta samu maigidan ta Adamu a dakin barcin su. Bakin ta kamar ya yage don farin ciki. Fuska kamar gonar auduga don smiling.
"Imagine Baban Ahyaan sai yau aiki na da VOA ya. . .