Iyakacin abinda ya rubuta kenan, wanda yasa Nasara sakin wayar a kasa ta tarwatse. Cikin karaji tace "SIYAMA! Me nake shirin gani haka?
Karya yake bazai taba musulunta sabida ke ba, kin yi masa kadan, kin yi tsararo. Kafin ya gan ki ya ga dubun ki, saidai su su bar nasu addinin ba dai shi ya bar nasa a kan su ba. Kuma barin nasu addinin baya sakawa ya aure su. Me yasa kika kula shi? Na dauka tun a shekarun baya mun rufe chapter din Hamzah? Na dauka kin gama cinye jarrabawar ki a kan sa?
Kada soyayyar dake. . .