MAMA POV
“Mlm so nake a lalata mata basirar rubuta littafin data fara. Ina so asa mata rashin kwanciyar hankali tare da farkai masu ban tsoro, ta yadda bata da wata natsuwar rubutun bare harta k’irkiri wani labari”
Mlm dake kallonta da jajayen idonsa, ya saki wani murmushi yana cewa “wani hanzari ba gudu ba Hajara”
“Ina jinka Mlm”
“Akwai wata k’awarki Asiya hakane?”
“Kware kuwa Mlm Asiya k’awarta ce Unguwa d’aya ma muka taso da ita ai”
“Yawwa to zata kawo miki ziyara a yau d’in nan. Zata zo da wani fahimmin zance, duk yadda zakiyi kiyi domin aba Asiya aurar Salma. Indai kina son ganin bayan Salma, to ki tabbatar Abbansu Maryam ya amince da abunda Asiya tazo dashi”
“Mlm na kasa fahimtarka fa?”
Murmushin gefen baki ya sake saki kamin ya d’akko wata kwarya cike da ruwa ya nuna cikinta, yana cewa “ki kalla tsakiyar kwaryar nan”
Da sauri Mama ta kai dubanta a cikin kwaryar abunda ta gani ne ya bata mamaki.
Da d’an mamaki take kallon Mlm.
Mlm ya ce “miye kika gani ciki?”
“To Mlm mutum na gani, kwance bashi da lafiya, kamar mai shirin komawa maciji, jifa fatar jikinsa yacce take komawa tana sabulewa kamarta aljanin maciji, masu komawa mutane, irin wadda nake kallo a cikin fina-finan India”
“To kinga wannan mutunin shine za’a aurama Salma shi, zata zauna da mahaukaci har rayuwarta ta lalace, bata tsinana komai a duniya ba, tazo a wahale zata koma a wahale”.
Wata shewa Mama ta saki harda su bud’a tsabar dad’i.
Ta k’ara duba cikin kwaryar tana cewa “ai Mlm dole ma Abbansu Maryam ya amince da wannan batu. Abu d’aya zaka min kasa shi ya amince kawai idan na masa zancan, karma yayi min gaddama”.
Mlm ya d’akko wani k’ulli ya mik’a ma Mama yana cewa “kinga wannan?, ki tabbatar kin sa masa a abinci yaci, kamin ki kai masa maganar, na tabbatar zai amsa bai shirya ba. Sana ita kuma zamu sa mata rashin natsuwar zuciya bata da lokacin ma rubuta wani littafi”
“Idan kamin haka Mlm ka gama min komai ai”
Mama ta fad’a tana bud’e jakarta ta fiddo da wasu kud’i, tana dank’ama Mlm sai washe baki yake.
*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*
“Hajiya yau ne fa na tura labarina na gasar Hikayata, kimin addu’a”
“D’iyar albarka Allah ya bada sa’a kinji”
“Amin Hajiyata”
Cewar Salma tana kallon Hajiya da murmushi kwance akan fuskarta.
Ahmad ne yayi sallama ya shigo hannunsa rik’e da wata leda.
Zama yayi kan d’aya daga cikin kujerun parlon yana kallon Salma dake mik’a masa gaisuwa, ya amsa yana cewa “Salma kina shan magungunan ki kuwa?”
Murmushi ta saki tana jin dad’in yadda Yayan nata yake bata kulawa sosai. Ta ce “eh man Y Ahmad Ina sha”
“To amma naga kwayar idonki ta canza kala tana son komawa d’orawa?”
“To nima ban sani ba, amma dai duk ina sha akan lokaci yadda ya dace”
“Abinci fa kina kiyaye cinsa?, kin san fa ba kowane abinci ne ya kamata ki rink’a ci ba?”
Hajiya ce tayi gyaran murya tana cewa “Ahmad kenan, kaima kasan ba komai take samu ta ci yadda ya dace ba, kai dai kawai Allah yasa mu dace ya bata lafiya kuma”
Shima ajiyar zuciya ya sauk’e yana mik’a ma Salma ledar hannunsa ya ce “anshi wannan ki samu kici, ki ajema Ismail sauran”
Da murmushi sallama ta amsa tana godiya.
Tashi yayi ya fice daga d’akin.
Bayan fitarsa Salma ta bud’a ledar tana kallon abunda Yayan nata ya sayo mata. Su kankana ne dasu Ayaba, da dai sauransu.
Sosai Hajiya tayi murna dan ya kamata Salmar ta rink’a shan abubuwa irinsu dama.
Sallamar da ake rafkawa a tsakar gidan ce, sawa Maryam fitowa daga d’akinsu.
Ganin k’awar Mama Asiya ce yasa ta cewa “Inna Asiya sannu da zuwa, ai ko yanzu Mamar ta dawo daga unguwa, Allah yasa zaki tadda ita, bari na kira miki ita, tana d’akin Abba”
“Yawwa y’ar albarka kira min ita, akwai magana yau ai”,
Bata tsaya jiran jin sauran abunda Asiyar ke cewa ba tayi gaba ta shiga d’akin Abban.
Zaune ta iske Mama sai wani iyaye take ma Abba yana biye mata.
Ganin Maryam ta shigo d’akin yasa Mama dubanta tana jiran jin miya kawota?.
Maryam ta ce “dama Mama Inna Asiya ce tazo “,
“Kai ai ko nasan da zuwanta, bari jeki gani nan zuwa”,
Maryam na fita Mama ta dawo da dubanta wajan Abba tana cewa “kaji abunda nake gaya maka ko?, dama na ce ma zata sake dawowa ne, domin tana so ayi abun da wuri”
Abba ya nisa ya ce “kin ce yaron bashi da lafiya zata je kula dashi ne, za’a d’aura auran domin gudun faruwar wani Abu?, to amma a can zatayi karatu ne ko kuwa?”,
Kallon takaici Mama ke aikama Abba, yadda yake shirin mata musu, duk da ta basa abinci da abunda Malaminta ya bata, kuma ya ci, dan yana kanci ma.
Ta ce “eh man zasu sata mana, babu abunda zata nema ta rasa. Ai kaga gara ma taje can tayi mai dalili, kai ka huta da kashe kud’inka akanta. Kuma tazo karatun ta kasayi kayi asarar kud’i akanta, tunda kasan ai ba k’ok’ari gareta ba, asarar kud’i kawai zakai, gara can taje tayi karatun acan”
“Kuma fa hakane Hajara. Ai kawai na amince, ko gobe suka zo za’a iya d’aura auran babu wata damuwa”
Wani almurin murmushi ta saki. Tana cewa “yawwa Abbansu Maryam shi yasa fa nake k’ara sonka, akwai saurin fahimtar mutum. Bari naje wajan Asiyar na sanar da ita abunda ake ciki”
Tana gama maganar ta fice daga d’akin.
“Ahh ahh Asiya yada zama waje kuma?, ga d’aki”
Cewar Mama data fito daga d’akin Abba, ta iske Asiya zaune a waje.
Asiya ta ce “wallahi kawai zama nayi nida Maryam muna d’an tab’a fira, ina Khadija ne ni kam?, ban ganta ba”
Mama ta ce “wallahi Khadija sun fita ita da wadda zata aura sunje wata sayayya ne”
“Ahh kai Masha Allah, kice an samo mana siriki kenan?”
“Ai kuwa dai, na nunawa a sa’a kuwa”
“Ayyiririiii, kice mun kusa zuwa aikin hajji?”.
Dariya Mama ta saki tana kamo hannun Asiya suka shige d’aki Mama na cewa “ai kuwa dai, gamu can a k’asa mai tsarki”
Zama Asiya tayi tana cire gyalanta ta k’ara natsuwa ta ce “kinga akwai fa magana a bakina sosai”,
Dariya Mama ta saki tana cewa “tunkan kizo na riga da na gama da matsalar, domin nasan zancan daya kawo ki”
Cike da d’unbin mamaki Asiya ke duban Mama, ta kasa hakuri ta ce “kamarya ban fahimta ba?”
“Hmmm Asiya kenan, Malami na nasa yayi min duba, har ya sanar dani zuwanki, da abunda zaki zo min dashi, tunkan kizo, na riga da na sanar da Abbansu Maryam, akan wannan zancan, kuma na gama shawo kansa, kawai abunda zance miki shine su turo ayi auran kawai”
Rik’e baki kawai Asiya tayi tana kallon K’awar tata, shaid’aniya uwar shaid’anu. Yo idan ba shaid’aniya ba, waye zai haka?.
Kamo hannunta Mama tayi tana fiskewa ta ce “ke karkiyi wani mamaki fa, kamar kin manta wace ni?”.
Ture komai Asiya tayi tana cewa “tunda kin gama da wannan, kema tukaicinki babba ne, idan abun ya kasance”
“Baki da damuwa komai zai kasance yadda muke so”.
Dariya suka saki a tare harda tab’a hannu.
*Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria*
Waya ce manne a kunnan Momy suna waya da Asiya.
Daga cikin wayar Asiya ta ce “Hajiya an gama komai fa, yanzu haka wakilanku kawai zaku turo a d’aura auran, ku tafi da amarya”
“Da kyau, haka nake sonji. Zan turo miki naira million biyar, ki d’auki naira million biyu, kiba wacce tayi hanyar abun ya yiwu, naira million d’aya, shi kuma Abban yarinyar ki basa cik’on naira million biyun”
Wata shewa had’e bud’a Asiya ta saki tana cewa “saike Hajiyarmu, uwar gida, a gidan Alhaji Bin Muhammad daga ke ba k’ari, Allah dai ya biya”.
Dariya kawai Momy ta saki tana kashe wayar. Ba’a jima ba kuwa saiga message na account number na Asiyar. Nan take ta tura mata kud’in gaba d’aya.
Zaune take a gaban Daddy bayan ta gama koro masa jawabin abunda take so ayi.
“Daddyn Salman, ina ganin yarinyar ita ce ta dace da zama da Salman, domin yarinyar tana da hankali da tunani, zata zauna dashi tsakani da Allah badan komai nasa na duniya ba, domin duk sauran da yake aura duk dan kud’insa ko kyansa ke rud’arsu”.
Daddy ya aje wani biro dake hannunsa yana rubutu a wasu takardu ya ce “kina ganin ita yarinyar ba’a danne mata hak’k’inta ba?, kin sanfa yadda rayuwar yaron nan take ciki”
Kamo hannun Daddy Momy tayi cike da kissa ta ce “ba wani danne hak’k’inta da akai. Hasalinma taimakonta akai, saboda ita kanta tasan ko a hanya bata isa ganin Salman ba, yaro mai kud’i ga kyau ga nasaba, komai ya had’a, kawai wannan ciwon ne ke basa matsala a rayuwa, kuma da sannu komai zai shige, idan komai ya wuce ita ce da riba nake gani ai”
Wani murmushin jin dad’i Daddy yayi, yaji dad’in yadda ta fahimtar dashi, kuma ya fahimta sosai. Inda daga k’arshe ya ce “to ita yarinyar y’ar ina ce?, yaushe kuma kike ganin za’aje domin tabbayo auran nata?”
“Y’ar Hadejia ce, kuma tabbayo aure duk bai taso ba, d’aurasa kawai za’ai, domin duk na gama da wannan, yanzu haka Abban yarinyar yasan da maganar, ku kawai yake jira”
“Ai shikenan tunda abu yazo gidan sauk’i. Zanje da kaina tare da wasu manya dana aminta dasu a d’auro auran zuwa gobe insha Allahu”.
Cike da farin ciki Momy ta baro part d’in Daddy. Tafe take tana maganar zuci.
“Hmm Alhaji kenan, kaifa gani kake kamar son d’anka nake ko?, ina duk duniya ba abunda na tsana yanzu kamar shegen yaron can naka, amma da sannu zan kawo k’arshensa”.
*NANAH* POV
Wani irin sansanin y’an Ta’adda ne su Auta suka tsinci kansu ciki. Auta ba abunda yake sai kuka yanata neman inda zai hangi Nanah.
An zube su wani waje duk ciyayi ga rana ta kwanyare.
Kowa ka gani wajan sab’anin y’an Ta’addar cike suke da tashin hankali.
Kamar ance Auta ya waiga ya hango Nanah dake d’aure a jikin wata bishiya har yanzu a sume take bata farka ba. Gashin kanta ya sakko ya rufe mata fuska.
Da gudu Auta ya nufi inda take, yana aikin kiran sunanta.
Wani d’an Ta’adda ne ya matso ya kwasa masa tsawa, yana cewa “kaiii ina zaka je haka?, koma inda kake kar yanzu na fasa maka kai da wannan Bindigar”
A tsorace ce Auta ya ke duban D’an Ta’addar. Amma duk da haka tsaye yake inda Nanah take ya rik’e tsintsiyar hannunta sai jijjigata yake.
A hankali Nanah ta fara motsa hannun nata, kamin komai nata ya fara dawowa dai-dai, dashi-dashi take ganin mutane, hatta muryar Auta sama-sama take iya jiyota, kamin ta ware idonta akan Auta.
Auta ko jin Nanah na motsa hannunta yasa shi sakin murmushin k’arfin hali yana sake kiran sunanta.
Kallon Auta take kamar wacce ta samu tab’in hankali. Kamin komai a hankali ya fara dawo mata, duk abubuwan da suka wakana a daran jiya.
Tana gama tunanowa ta fashe da wani irin kuka mai k’arfi jikinta na rawa, ta kama leb’en bakinta ta cije tana durzar kuka. Ganin yadda take kuka yasa Auta ma fashewa da kuka.
Wani daga cikin y’an Ta’addar ne ya k’ara matsowa inda suke, bai tsaya wata-wata ba, ya damk’e gashin kan Nanah ya jashi zuwa baya da k’arfi, har saida ta saki wata k’arar azaba. Fuskarta ce ta bayyana.
Hawaye duk sun b’ata mata fuska. Cike da rashin imani yake kallonta ya ce “zakiyi mana shuru a wajan nan, ko sai na kashe wannan bakin naki, maima mutane kukan banza?”
Wani irin bak’in ciki ne ya rufe Nanah, data na dama wallahi saita kashe duk wani d’an Ta’adda dake wajan yanzu, to amma bata da damar hakan.
Sakinta yayi yana maido dubansa inda Auta yake.
Ya wani k’ankance ido ya ce “ni wai miye ma anfanin tahowa da wannan yaron?, ai da an rage masa wahalar duniya, an aikasa can kiyama”.
Zare ido Nanah tayi tana jin wani sabon tashin hankali na saukar mata.
Tafiya suka farayi suka bar wajan da Nanah take. Suna magana, ganin haka yasa Auta rungume Nanah dake d’aure kamar wata akuya.
Ba abunda y’an Ta’addar suke sai shan tab’a da giya. Ga y’an matan da suka dad’e da satowa suna faman dafa masu abinci, wasu ma sun maida su k’aruwan k’arfi da yaji, sun maida su kamar wasu matansu.
K’iri-k’iri sai kaga k’aton gardi, daya ji sha’awar mace, zai d’auki mace kamar kayan wanki yayi cikin wata rufma da ita, ya biya ma kansa buk’ata, ya kuma tashi ya zuge wandonsa. Yadda suke afka masu kamar wasu dabbobi.
Yadda Nanah ta lura da yawan matan wajan suna sato sune kawai dan su rink’a masu bauta, da biyan buk’atarsu kawai. Hakan yasa Nanah shiga wani sabon tashin hankali marar musaltuwa.
Motsi kad’an tana nanik’e da Auta, wadda ji take kamar ta mayar dashi ciki.
Wata irin yinwa ta fara addabar wa’inda suka sato, ciki harda Auta, ya fara kuka, yana gaya ma Nanah yinwa yake ji. Dan rabonsa da abinci tun jiya cikin dare gashi har gare ya waye rana na neman fad’uwa.
Wasu hawaye ne suka shiga zuboma Nanah na tausayin Auta, ita dan ita zata iya zama a haka, zata iya jurewa na d’an wani lokaci, kai zama ta iya hakura har zuwa wata safiyar. Shifa?, yaro ne.
Gashi anbi an wani d’aure mata hannu, tana son rarrashin Auta, tama rasa wacce kalma zata fara basa hakuri da ita.
Kukan da Auta yake ne ya fara isar y’an Ta’addar. Hakan yasa wadda Nanah bazata tab’a manta sunansa ba, Mai suna Tajo ya nufo inda suke.
Duk duniya idan akwai wadda ta tsana to bazai wace wannan Tajo ba, shine ya rabata da farin cikin rayuwarta, wato Innarta, shine ya ruguza masu rayuwa, shine ya rabasu da jigwan rayuwarsu. Da tana da dama saita kashe Tajo kamar yadda ya kashe Inna.
Da jajayen idonsa yake kallon su Nanah, ganin irin kallon da Nanah ke aika masa dashi, na tsananin tsana da fusata, yasa Tajo shekewa da wata dariya yana nuna Nanah da hannunsa.
Can ya tsagaita dariyar yana kallon Nanah da ba alamar tsoro yanzu a cikin idonta. Ya ce “keee uban mi yaron nan yake so ya ishemu da kuka?”.
Shuru tayi bata da niyar magana ga Auta daya k’ara balun d’in kukansa.
Haushi abun ya bama Tajo, hakan yasa ya d’auke Nanah da wani gigitaccan mari. Wadda yasa taga giftawar wasu taurari. Duk da haka taji zafin marin daya kai mata, amma tayi shuru tana kallonsa da jajeyen idonta da suka kad’a sukai jawur.
Ganin fa bazata tanka masa ba, yasa Tajo jawo Auta ya daka masa tsawa yana cewa “kaii kayi ma mutane shuru ko yanzu nasa wuk’a na yanka maka wuya wallahi”
Auta bai daina kuka ba, majina da hawaye duk sun b’ata masa fuska.
Wani dogon tsaki Tajo yaja yana shafa sumar kansa, ya d’an daga kansa sama, sak’on d’aya biyu……. Kawai ya kaima Auta wani bugu a saman kai, nan take Auta ya zube a sume.
Wani sab’on kuka ne ya kufce ma Nanah tana kiran sunan Auta iya k’arfinta, duk tunaninta ko mutuwa yayi.
Cikin muryar kuka take magana tana kallon Tajo cike da tsana ta ce “ku sani Allah bazai tab’a kyale ku ba, Allah saiya isar mana akan zaluncin da kuke mana. K’aramin yaro ma baku kyale ba, tsabar baku da imani, Allah ya isarmu wallahi bamu yafe ba”.
Dariya Tajo ya saki yana matsowa inda Nanah take, ya damko wuyanta yana cewa “au ashe kina magana y’an mata?, na d’auka ai kurma muka d’akko. Dama mu ai bamu ce ku yafe ba. Ya ishe mu da kukan banza ne, shine na sashi yin baccin dole, kin gane?, zai farka ai ba mutuwa yayi ba, amma ki sani ya sake mana irin haka, to zaibar duniya ne gaba d’aya. Ya kamata ki kula, bama son damuwa ne”.
Wani abu mai d’aci Nana ta had’iye a mak’oshinta tana bin Tajo da kallo. Ji take inama tana da dama data shak’e masa wuta shima harsai ya daina numfashi.
Cikin dare Nanah tajiyo kukan Auta daya farka, sanyin dake cikin dajin ne ya farkar dashi, ga kuma inda yake kwance tsinnaku duk sun cijeshi a jiki. Da sauri Nanah ta kira sunansa a hankali. Da lalube ya k’araso inda Nanah take, yana zuwa ta rufe masa baki da tafin hannunta data samu Tajo ya kwance mata shi, d’azo daya gama gaggaya mata magana.
A hankali Nanah ta ce “dan Allah Auta kayi shuru, kayi hakuri kaji?, zuwa safiya za’a baka wani abu kaci, kana kallo mutanan nan basu da imani fa, kana so ka mutu ne?”.
Da sauri Auta ya girgiza mata kai.
Ta ce “to yawwa ka daina kuka idan baka so kaji?”.
Ba yadda Auta yayi dole tasa yayi shuru ya mak’ale a jikin Nanah.
Suna haka, sukaji ihun wata matashiyar yarinya, daga jin yadda take ihun tana neman taimako, zaka san cewa so ake a keta mutumcinta ne.
Yadda Nanah ke jin yarinyar na cewa “wayyo Allah, ku taimaka min zai kashe ni, na shiga uku ina zan kai wannan mutunin, zai lalata min rayuwa dan Allah ku ceceni”.
Waro idonta Nanah tayi tana kallon wata ruffa da abun ke faruwa hasken fitila ta gani a wajan, ihun yarinyar na fitowa daga cikin rufar. Tana iya jiyo yadda suke kokowa da yarinyar, tana son kwance kanta. Tana jin shi kuma yadda yake ta kai mata maruka ba k’ak’k’autawa.
Allah sarki yarinyar duk da irin dukan da yake kai mata so kawai take ta kwaci kanta, sai kuka take tana kiran azo a taimaketa.
Ganinfa tana son b’ata masa lokaci, gashi duk ta ji masa ciwo yasa ya harzuk’a bai san sadda ya d’akko bindiga ba ya sakar mata harsashi.
A mugun rud’e Nanah ta toshe kunnuwanta had’e da k’ara rungume Auta daya fasa wata gigitacciyar k’ara yana sumewa a jikin Nanah, domin harga Allah ya mugun tsorota sosai. Nanah tama rasa wane hali take ciki, duk ta rud’e ta fice daga yaccinta. Ga Auta da bata jin motsinsa a jikinta, ga yarinyar da tana da tabbacin ita ce aka halba. Tana iya jiyo yadda D’an Ta’addar ke ta’asarsa saman kan yarinyar duk da halbinta da yayi, amma tsabar mugunta da rashin imani a haka ya afka mata…