Hadari Gabas
Ƙaramar yarinya ce da ƙalubalen rayuwa ya sauya akalar ƙaddarar rayuwarta, daga mai tafiya da ƙafafu biyu zuwa mai ƙafafu huɗu. Baiwar rubutu ta bayyana a gareta a daidai gaɓar da take tsakiyar alhinin rabuwa da iyayenta da suka shuɗe a ranar da ta rasa ƙafafunta. Ƙanin mahaifinta wanda ke riƙe da ita shi ya fara zama barazana ga cikar burinta na zama Marubuciya. A daidai lokacin da ta duƙufa domin tattara bayanan da za su bata daman ɗora alƙalaminta a wata gasar rubutu ta ci karo da gingimemen dutsen da ya fara barazanar danneta, sirrin da aka bi dare da rana aka lulluɓe hasken alkaminta ya bankaɗo shi. A nan ta fahimci dalilin zamanta a keken guragu da musabbabin raba iyayenta da numfashinsu.
Wata Shari'ar
Shari’ar da aka yi mini tsakanina da Idris a kotu, ba ta isa ta wanke mini mummunan tabon da ya bar mini ba. Domin ya lulluÉ“e ni da bargon makirci, ya kuma haÉ—a da kashe mini rayuwa ta hanyar ruguza mafarkina na zama uwa.