Tana Kasa Tana Dabo
Sameer babu abinda yake yi face sheƙe ayarsa da matan banza, duk kuwa da yana matuƙar son matarsa Farida. Tsammanin tana yin abin da yake yi ya sa shi fara zarrginta, hakan ya fara kawo musu tangarɗa a zaman aurensu. Baƙin kishi da rashin yarda da matar tasa ne ya kai shi ga kai ƙaninsa Bello mahallaka ba tare da ya sani ba.
Kowa Ya Debo Da Zafi
Neman ‘yancin rayuwa tare da samun jin daɗin duniya ya sa wasu matasa su shida barin ƙasarsu zuwa wata. Ninaah , Ibina, Zuzuuh, Fu’ad, Ammar da Haris, sun bar ƙasar Nijeriya inda suka tafi ƙasar Umbull domin yin rayuwa mai ‘yanci cikin jin daɗi da annushuwa. Sai dai tun a ranar da suka sauka a ƙasar suka fara da na sani sakamon wata mummunar cuta da ta kama biyu daga cikinsu inda ta mayar da su wasu irin dodanni masu cin naman mutane. Shin ko za su koma gida lafiya?
Kaddarata Ce
Kyakkyawar budurwa Suhaila ta tsinci kanta a wani irin hali mawuyaci, duk saurayin da ya furta mata kalmar ‘so’ mutuwa yake yi. Sulaiman, Shamsu, Abdulƙadir, Mashkur da kuma Dr. Adnan duk sun mutu a yanayi kusan iri ɗaya bayan sun furta mata kalmar so. Kafin mutuwar Adnan, ya faɗa mata cewa ya gano dalilin da ya sa samari ke mutuwa idan suka bayyana mata soyayya, sai dai bai kai ga sanar da ita dalilin ba ya mutu. Ana cikin haka ne kuma sai ga wani saurayin da ke yi mata ƙarin karatu ya mutu, ba a gama wannan ba kuma wani ya ce yana so a yi musu aure cikin kwana ɗaya.
Kaddarar So
Lalaah da Lilaah ‘yan’uwa ne na jini kuma dukkansu sun kamu da ƙaunar Doctor Arman Harun Maleek, sai dai ita Lilaah kullum cikin maƙale masa take yi, yayin da shi kuma ya fi raja’a wajen Lalaah. Burin Hajiya Zulaihat shi ne Bilkees ta auri Arman, amma ita ba ta son shi, Aunty Shuwa kuma tana ƙoƙarin kawo Salma ‘yar ƙawarta gidan domin ita ma ta samu shiga wurin Arman ɗin domin su samu dukiya mai tarin yawa.
A gefe kuma Inna Saude ce ke fafatawa da ɗiyarta Mufida wadda ta fetsare, ko gidan ma sai ta ga dama take kwana. Yayin da ‘yar riƙon da aka kawo mata mai suna Maryam ke fuskantar waƙi’a iri-iri.
Wace ce za ta auri Arman?
Rumfar Kasuwa
Alhaji Isah mutum ne da ke ƙoƙarin sauke nauyin gidansa daidai gwargwado a koyaushe. Sai dai hakan bai sa matarsa ta gode wa Allah ba, domin kuwa tana yi wa ‘yarsa awara tana siyarwa bai sani ba. Maryam kuwa tsula tsiyarta take yi yadda ta ga dama matuƙar za ta siyar da kayan siyarwarta, duk kuwa da irin nasihar da ‘yar uwarta take yawan yi mata.
Sanadin Kenan
Engineer Ma’arouf Ji-Ƙas zaɓaɓɓen gwamna ne, yana da ‘ya guda ɗaya mai suna Amina wacce ke fama da ciwon shanyewar ɓarin jiki. Bayan ya lura da cewa matarsa Lailah ba za ta iya kula mishi da ‘yarsa ba sai ya nemi likitar da za ta zo har gida ta kula da ita. A sanadiyar haka ne ya haɗu da Dr. Amina, ko yaya haɗuwar za ta kasance?
Duniyata
Irfaan da mahaifinsa jami’an ‘Yan sanda ne. Ƙaddarar rayuwa ta kai su Saulawa inda ya haɗu da Ihsan, wadda ta tsaya mishi a rai ba tare da wani dalili ba. Rashin yin soyayya balle ma batun aure ya sa iyayen Irfaan ke tunanin ko Aljana ce ta aure shi.
Bakon Yanayi
Munawwa da Munara yan tagwaye ne masu kama daya. Yana da wuya ake iya bambance su, to amma wannan kamar a ido kawai ta tsaya domin kuwa halayyansu sunyi hanun riga. Wannan banbanci nasu ya jawo saurayin daya daga cikin su ya zo musu da wani Sabon Yanayi na jarraba soyayyarsu. Shin yaya zata kaya? Shin mai saurayi zata ci gaba da samun soyayyar saurayinta ko ko labarin zai canja?
Na Cancanta
Sumayya Abdullah Khalil mace ce mai hakuri da tarbiyya daidai gwargwado. Talakawa ne su, wannan ya sa a dangi ake ƙyamar su, ake gudun su kuma ba a son ganin su. Domin da an gansu za a fara tunanin wani abu suka zo nema. Babban abin da ya fi ci wa Sumayya tuwo a ƙwarya shi ne irin yadda dangi ke zargin halin da suke ciki ya ta’allaƙa ne da ‘ƙashin tsiya’ irin na mahaifiyarsu.
Daurin Huhun Goro
Halin yunwa, talauci da kuma matsatsin rayuwa da ake ciki ne suka tunzura Tabawa har ta kai ga tana bin layi da lunguna tana zagin shugabanni, ‘yan siya da kuma ‘yan kasuwa. Domin ita a ganinta, duk su ne sanadin faruwar hakan a cikin al’umma. Ta kuma ƙudiri aniyar kawo sauyi game da wannan lamari.
Abbakar
Abbakar Malami ne da ke koyarwa a jama’ar B.U.K. Allah ya jarrabe shi da matsanancin son wata ɗalibarsa mai suna Ummulkhairi, sai dai ya kasa faɗa mata. Kwatsam watarana sai ya gano cewa ashe matar aure ce, har ma tana da ciki. A gefe kuma ga ƙawarta Aisha da take matuƙar son Abbakar ɗin.
Kushewar Badi
Tsawon shekaru Almustapha da matarsa Lajja suna tare, suna matukar so da kaunar junansu, so irin na don Allah. Abubuwa biyu ne kadai ke damunsu a rayuwa; rashin haihuwa, da kuma wani al’amari mai firgitarwa da ke tare da Lajjar. Kwatsam! Wata rana tsaka a cikin ire-iren ranekun babi-babi na rayuwarsu, wani mutum mai suna Alhaji Hammad ya bayyana tare da shaidun cewar Lajja fa matarsa ce. Hujjojin da ya kawo sun tabbatar da abin da ya fada haka yake. Don haka alkali ta karbe Lajjar daga hannun Almustapha aka ba Alhaji Hammad. Shekara daya da faruwar wannan abu Allah ya yi wa Lajja haihuwa. To a wannan lokaci ne kuma wasu hujjojin suka kuma bayyana, kuma suka tabbatar wa duniya Lajja ba matar Alhaji Hammad ba ce! To matar wane ne?
Mutuwar Tsaye
Dr. Deeni ƙwararren likita ne a ɓangaren jinyar cututtukan da suka shafi mata kawai. Rana ɗaya kawai ya tsinci kansa da cutar makanta wadda ta zo mishi a yanayi na bazata. Matarshi Deena, wadda ke ɗauke da tsohon ciki ta fi kowa shiga tashin hankali, domin kuwa mahaifiyarta ba son aurenta da shi take yi ba. A gefe kuma ga mahaifiyar su Deeni wacce ita ma ke fama da tata lalurar. Shin za su faɗa mata ne ko kuma za su ɓote? Yaya makomar aikin Deeni? Kuma yaya makomar aurensu da Deena?
Abnur
Hankalin mahaifin Kamal ya yi matuƙar tashi bisa ganin budurwa a ƙofar gidanshi tun da sanyin asuba. Kamal ne ya yi ta maza ya shigar da ita wurin mahaifiyarsa domin ta yi Sallah. Abin da ba su sani ba shi ne, irin mummunan halin da wannan budurwa ke ciki ya girmi tunaninsu.
Wani Rabon
Maryam, wacce aka fi sani da Faheema ta nutsa cikin duniyar farinciki sakamakon ganin zuwan ranar aurenta da Mas’ud. Kwatsam sai ya kira ta a waya yana shaida mata cewa ba zai iya aurenta ba. Ganin cewa wannan ba shi ne na farko ba da aka fasa ɗaura aurenta, hakan ya sa ta sha alwashin daina soyayya gaba ɗaya, duk kuwa da cewa samarin ba su daina kunno kai ba.
Halimatus Sa'adiya
Halima Jibril da yayanta Muttaƙa na fuskantar Ƙalubale mai girma a cikin gidansu, saboda maman su Hanifa ba ta da aikin yi face haɗa su da mahaifinsu, abin ma har ya kai ga duka. A gidan su ƙawarta da suka zama tamkar ‘yan biyu, wato Sadiya da ɗan’uwan mahaifinta Abba Ibrahim ne kaɗai Halima ke ɗan samun sauƙin rayuwa.
Danyar Guba
Salis, wanda ya kasance shashan namiji marar kishi, ya ba wa matarsa Nu’aymah damar yin kowace irin mu’amala da maza matuƙar za ta samo musu kuɗi. A irin wannan harkar da take yi ne ta haɗu da Masroor, matashin mai kuɗi. Duk da cewa sau da dama takan yi mamakin irin rashin kishin Salis, ruɗin duniya ya sa ba ta wani damuwa. Babban abin da ba su sani ba shi ne, ɗanyar guba suke ɗaura wa cokunansu, kuma ba za ta barsu ba har sai ta kai su ga halaka.
Silar Aurena
A Unguwar Dole, da ke ƙaramar hukumar Daura ta Katsina, Maryam na fuskantar ƙalubalen zamantakewar aure. Baba Hari ta gallabeta kuma ta sa ta a halin ƙaƙa-na-ka-yi ta hanyar cin fuska da musgunawa.
Shi kuwa Admiral Ibrahim Khalil, mummunar jarabawar rayuwa ya faɗa, yayin da ya kama matarsa dumu-dumu tana rawar Tiktok.
Kangin Rayuwa
A wani ƙauye mai suna Fachankan, da ke cikin Jahar Jigawa. An yi wani magidanci mai suna Alhaji Sani Mai Goro. Mai Goro na da mata uku da ‘ya’ya da dama. Su ma yaran da yawansu sun yi aure, hakan ya sa gidan ya zama a cike da jama’a. Ko da yake halayen mutanen wannan gida ya bambanta, Hajara ita ce ta zama makirar da ta zarce saura, domin ita har bin bokaye take yi don ganin ta ƙuntata wa kishiyarta A’i.
Bakin Fenti
Sakamakon faruwar wani abu muƙaddari a rayuwarta, matashiya Sajeederh ta shiga halin jimami da rashin makama saboda canji da ta samu. Hajiya Aisha, wadda ita ce mahaifiyar angon da za a yi haɗin auren shi da na Sajeederh kanta ta shiga wani hali sakamakon irin surutan da Hajiya Ruƙayya take yi mata. Wannan baƙin fenti ne ya sa har ‘yar’uwarta Amina ke yi mata gori.
Muryar Dalili
Kundin rubutattun waƙoƙin Muryar Dalili ya ƙunshi waƙoƙi ne masu yawa da suka taɓo fannonin rayuwa daban-daban cikin hikima da jan hankali domin masu karatu su amfana. Musamman wasu abubuwan da suka shafi zamantakewa da kuma yadda zamani ke tafiya.
Daga Karshe
Fatima budurwa ce ‘yar kimanin shekaru goma sha bakwai. Shiririta, rashin hankali da tsiwa bayyanannu ne daga cikin halayenta. Kowa na ƙorafi da ita game da wannan, domin ko waye mutum za ta iya ɗaga ido ta kalle ka ta faɗa maka duk maganar da ta ga dama. Kafiya, kuwa sai ka ce kuturu. Jamilu ɗan uwan mahaifiyar Fatima ne, kuma shi take so ta aura, Mustafa kuma malamin Fatima ne na Islamiyya. Jamilu ya daɗe yana son Fatima amma bai faɗa wa kowa ba, ita kuma ta ce wa Mustafa ya turo manyan gidansu neman aurenta.
Siddabaru
Ko da yake yasan ba a mutuwa a dawo, bayyanar hotunan gayyatar auren Maryam da ya gani a Facebook tare da cikakken sunanta da ya gani sun ƙara tabbatar wa da Isah cewa lallai akwai wani ɓoyayyen al’amari game da mutuwarta. Ita kuma Jalila ko ya za ta yi da irin halin ko in kula da mijinta ke nuna mata?
Alkalamin Kaddara
Altaaf Tafida ya daɗe da yin aure amma har yanzu bai samu haihuwa ba, gashi kuma Allah ya jarabce shi da son yara. Kwatsam watarana sai ƙaddara ta sa ya ci karo da wasu ‘yan biyu waɗanda ko tantama babu nashi ne, sai dai karɓarsu daidai yake da neman jaki mai ƙaho. Rafiq ya kasa fahimtar dalilin da ya sa ba ya iya tuƙi, alhali kuwa yana iya tuna lokutan da yake tuƙa kansa a mota, tashin hankalinsa ya hauhawa ne ya yin da ya fahimci sabuwar amaryarsa Tasneem ta zo gidan shi ba tare da budurcinta ba. Kafin kuma ya gama ji da wannan, sai ga wani sabon asirin da ka iya rusa komai na rayuwarsa ya fara fitowa fili.
Marubuci
Yayinda wani matashin marubuci ya saurari wata tattaunawa da aka yi da wani fitaccen jarumin fina-finai, hakan ya ƙara mishi ƙwarin gwiwar ci gaba da rubutu tare da zama tsanin samun nasararsa a harkar rubutu.
Asabe Reza
Hankalin fitacciyar Karuwa Asabe Reza ya tashi sakamakon cin amanar da ƙawarta Fakriyya ta yi mata na aure mata hamshaƙin masoyinta Hamoudi. Wannan ya sa ta sha alwashin tarwatsa musu farincikin da suke fatar samu.
Rabon A Yi
Farida, wadda aka fi sani da ‘Ferry’ ta yanke shawarar zuwa bikin babbar ƙawarta Jiddah, duk kuwa da cewa mijinta Mukhtar ya tabbatar mata da cewa baya so ta je. Hankalinta ya tashi sosai yayin da ta na gidan bikin aka ce an yi sata, ana cikin rigimar sata kuma aljanun wata suka tashi. Ga kuma Mukhtar yana kiranta a waya.
Fudayl
Abbu ya yi wa ‘yarsa Hamna Nuhu Alƙali aure da mijin da ko sunan shi ba ta iya riƙewa ba saboda ba auren soyayya ba ne. Amna za ta bi shawarar Ammi ta zauna da mijinta lafiya ne ko kuma za ta biyewa son zuciya da ra’ayinta?
Laifin Wa?
Ladidi matashiya ce mai ji da ƙuruciya, hakan ya sa ta faɗa harkar bin maza domin ta hucewa kanta haushin rashin ɗauke mata ɗawainiya da iyayenta suka kasa. Duk da cewa sun san irin abin da ɗiyarsu ke aikatawa, amma ba su da ta cewa. Saboda wani lokaci ma wurinta suke zuwa su yi ‘yar murya.
Kaddarar Mutum
Tun bayan mutuwar mahaifinta, wato Malam Tanimu, Asma’u da mahaifiyarta Inna Hauwa suka shiga cikin tsangwama a wurin mutanen ƙauyen Somayi. Hakan ko ya samo asali ne sabo da ta ƙi amincewa da batun auren duk samarin garin, musamman Muntari da yake ɗan Maigari. Ba zato ba tsammani kuma sai wani ya yi wa Asma’u fyaɗe har ta samu ciki. Wannan dalili ne ya tursasa mata barin ƙauyen ba don tana so ba. Ko za ta samu mafita a inda ta nufa?
Ba Kauyanci Ba Ne
Alhaji Abdulƙadir mutum ne ɗan zamani wanda kiyaye haƙƙoƙin addini bai dame shi ba, to amma ‘yarsa Salma da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu suna da kyawawan halaye kuma suna matuƙar kiyaye dokokin shari’ar Musulunci. Alhaji Sameer da Hajiya Samira suna da ɗa guda ɗaya da suka haifa mai suna Kamal. Duk iya ƙoƙarin da Alhaji Sameer yake yi na ganin Kamal ya shiryu, ita mahaifiyarsa gani take takura ce. Kamal ya kama hannun Salma a wurin wani taro inda ta wanke shi da mari. Sai daga baya yake jin ashe mahaifiyar Salma mahaifinsa ya fara so ya aura kafin mahaifiyarsa.
Munafukin Miji
Ridayya na matuƙar son mijinta Zameer. Ta mallaka mishi dukkan rayuwarta da duk wani abu da ta mallaka. Saboda shi ta rabu da iyayenta da ‘yan’uwanta. Sai dai shi kuma a nashi ɓangaren, Zameer cin amanarta yake yi, ha’intarta yake yi6, kuma amfani da ita kawai yake yi wajen cimma muradansa. Duk irin yadda Mardiyya ta so ta nuna wa Ridayya gaskiyar abinda mijinta ke yi ta kasa fahimta saboda makauniyar soyayyar da take yi mishi.
Yasmeenah
Gagarumar matsala ce ta yi wa wasu masoya dirar mikiya a washe-garin ɗaurin aurensu sakamakon canjawar da halittar amaryar ta yi, ta yadda ita kanta ta kasa yarda da cewa ita ce ko ba ita ba ce.
Kisan Boko
Kyawun fuska da kyawun dirin jiki tare da dakakkiyar niyyar ganin ta yi karatun boko mai zurfi ne suka sa ake yi wa Sa’adatu inkiya da ‘Yar Boko. Tabbas ta yi bokon, domin har ta kai ga samun digiri na biyu. Ga gida da aiki duk ta mallaka. Babban tashin hankalinta shi ne rashin samun mijin aure. Ƙawayenta da yawa tuni sun tara ‘ya’ya, samarinta duk sun kama kansu, ga shi ita kuma auren take so.
Shameekh
Shameekh na cikin wani irin yanayi. Shi da Jidderh suna soyayya mai inganci da aminci, kuma suna fatan kasancewa tare, a gefe guda kuma ga Safwan ya nace wa Jidderh duk kuwa da cewa ba ta son shi. A ɗaya ɓangaren kuma Sofiya ce ta ƙwallafa ranta a kan Shameekh, kuma har ta sha alwashin illata duk wani wanda ya yi yunƙurin shiga tsakaninsu. Har da cewa sai ta hallaka Jidderh ko da ita ma za a kashe ta, in ya so kowa ya rasa.
Tsinuwar Uwa
Yayin da samarin wata unguwa suka yi cincirindo don ganin ba a binne wata sabuwar gawa da ta mutu a maƙabartarsu ba, hakan sai ya zamo sanadin haɗuwar gangami na ban mamaki. ‘Yan’uwan wannan gawa sun ƙi yarda ko wanka a yi mata balle a kai ta ga kabari, ga samarin unguwa sun yi caaa don ganin ba ai hakan ba. Bayan an saka ta a kabari da ƙyar har an fara zuba ƙasa, kwatsam sai gani aka yi ta miƙe. Ashe ba ta mutu ba.
Wace ce ita? Kuma me ya sa ake gudun ta? Mene ne labarinta?
Shirin Allah
Wanda Allah Ya so da shiriya, babu wanda ya isa ya sauya shi. Duk da irin ƙalubale na rayuwa da Hamida ta fuskanta har zuwa aurenta da Abdurrashid, da kuma harin da babban amininsa Usman kai mata tare da nuna sha’awarsa akanta basu canza ta ba. Shin ko Hamida za ta ba wa Usman dama wajen saɓa wa Allah, me zai faru idan Abdurrashid ya gane Usman na neman matarsa?
Bakar Tafiya
Basma, Jafar, Salma, Rabson Guy da Biba sun shirya tsaf domin yin wata doguwar tafiya, sai dai kafin su isa inda suka nufa dole sai sun bi wata shu’umar hanya wadda ta ratsa ta cikin wani baƙin daji da ake yi wa laƙabi da ‘Kai Ka Zo.’ Kowa a cikinsu tana da babban dalilin da ya sa zai yi wannan tafiya. Sai dai tun kafin a yi nisa kowannensu ya fara da na sanin yin tafiyar a lokacin da kwatsam direbansu ya mutu ba tare da sun san dalili ba.
Our Friendship
When Zainab caught her best friend Sa’ada with her husband naked on their matrimonial bed, a ruckus ensured which ended the marriage shortly after. But is that really the solution she sought? Are things going to happen the way Sa’ada planned?
Wane Ne Ni?
Ba zato ba tsammani Ahmad ya farka ya ganshi a gadon asibiti ba tare da ya san yadda aka yi ya zo wurin ba. Ba ma wannan ba, ya kasa tuna hatta sunansa da kuma ko shi waye. Bayan Dr. Aminu ya yi masa wasu ‘yan gwaje-gwaje sai aka gano cewa ya kamu da cutar mantuwa ne. Kwatsam sai ga wata mai suna Hafsat ta yi wa rayuwar shi shigar ba zato, sai dai likita kuma ya ce ita ɗin ba gaskiya bace, kawai tunaninsa yake hasaso mishi hakan. Shin ko Ahmad zai yarda da wannan batun?
Sakacina Ko Halin Maza?
Juwairiyya yarinya ce mai matuƙar kamun kai. Sai dai halin da suke ciki na talauci na neman yi wa mutuncin nata barazana. Ga kuma ƙanin mahaifinta Baba Sani da ya kafa mata ƙahon zuƙa ba tare da wani takamaiman dalili ba.
Bakar Kaddara
Wasu lokutan ba sai ka aikata mummunan aiki ba kafin baƙar ƙaddara ta afko maka. A wasu lokutan kuma, halayen mutane ne ke kaisu ga faɗawa cikin bala’i.
Kauthar
Kauthar na cikin wani hali na ruɗani, domin kuwa mahaifinta ya yanke shawarar aurar da ita ga Abdulmalik Kwangila bayan sati biyu da kammala jarabawarta. Inda tashin hankalin yake shi ne, Abdulmalik mijin yar’uwarta ne kuma babbar ƙawarta, aminiyar da suke ƙaunar junansu tamkar ciki ɗaya suka fito. Yaya Faheemah wadda aka fi sani da Anty Ummi za ta ɗauki wannan labari na auren babbar ƙawarta da mijinta?
Launin So
Umma Maryam da yaranta uku, Samir, Abba da Samira suna cikin wani irin mawuyacin hali mai ban tausayi sakamakon talaucin da suke ciki wanda ya jawo musu ƙunci a cikin rayuwarsu. Sai sun yi bara ma suke samun abin da za su ci kuma a bola sukan zauna a mafi yawancin lokaci. Duk da cewa Alhaji Mas’ud ya basu wurin zama a cikin gidansa, shi da matarsa Hajiya Kilishi da babu irin karar tsanar da ba su ɗora musu ba. A cikin wannan yanayi ne kuma kwatsam sai Samir ya kamu da tsananin son Zuhra, shalelen Alhaji Mas’ud. Shin ko za ta karɓi soyayyar tashi?
Ma'aurata
Habibu mijin Ruƙayya ne, kullum cikin yi mishi masifa take saboda in ya fita gida ba ya dawowa sai dare sosai, hakan kuwa ya faru ne saboda ƙazantarta da rashin girki da gyaran jiki, wani lokaci ma hana shi haƙƙinsa take yi ta ce sai ya biya. Fahad shi ma ba ya wani zaman gida, kuma a buge yake dawowa Fatima, wani lokaci ma ya haɗa mata da duka da zagi. Shin ko za su samu mafita?
Nima Matarsa Ce
Taufiq ya shiga gagarumar damuwa sakamakon irin bita-da-ƙullin surikarsa wato Hajiya Murjanatu. Tun da ya nuna yana son ‘yarta Mujaheeda, shikenan ta shiga kawo tsirfa iri-iri duk don ta ga an fasa, domin a cewarta bai dace ya auri ɗiyarta ba. Shi kuma yana son Mujaheed, ita ma kuma tana sonsa. Anya kuwa ko da sun yi auren Hajiya Murjanatu za ta bar su su zauna lafiya?
Birnin Sahara
Haidar ya farka daga suman da bai san ya yi ba, yayin da ya tsinci kanshi a wani babban birni da duniya kaf ba ta san da wanzuwarsa ba. Abin ya bashi mamaki ƙwarai da gaske da ya ga tsohuwar budurwar da yake so Nadiya ita ce ke mulkin wannan birnin. Sai dai mamakin shi ya ƙara nunkuwa ne bayan ya fahimci cewa yana da alaƙa ta asali da wannan birni, kuma ya zama wajibi a gare shi ya tsallake wasu matakai domin ya zamo sarkin wannan birni matuƙar yana so ya ceci rayuwar ‘yan uwansa.
Matar Bahaushe
Ruqayya Manaf ƊanGambo ‘yar majalisar wakilai ce mai tausayi da ganin ta taimaki al’umma. Captain Anwar Sarari da Honorable Bamanga Jafaru, na daga cikin mazajen da ke mararin ganin sun mallake ta a matsayin matar aure. Sai dai kuma, tuni ta daɗe da yi wa mazan duniya gaba ɗaya kuɗin goro, hakan ya sa ba ta da lokacin su.
Addininmu
Abduljabbar wanda aka fi sani da AJ, matashi ne ɗan talaka jikan talakawa, sai dai kuma ya ƙwallafa wa ransa zama hamshaƙin mai kuɗi. A dalilin hakane yake yaudarar budurwarsa Zahra tana sato kuɗin iyayenta tana kawo mishi. Abdallah shi kuma ya tubure fafur kan cewa shi fa ƙanwarsa Maryam ba za ta auri ɗan bidi’a ba. Zainab Ambato kuma na shirin yin fito-na-fito da wani matashin mai wa’azi da ke sukarta.
Mutum Da Kaddararsa
Bilkisu matashiyar mace ce mai ƙarancin shekaru, sai dai ƙaddarar rayuwa ta sa zaman aure ya gagare ta. Da farko ta auri Aminu wanda suka samu ɗaa guda ɗaya da shi wato Amir. Bayan sun rabu ne sai ta auri Malam inda suke zaune tare da uwargidarsa Hajja. Kisisinar amaryar Malam ne tai ta jawo musu damuwa har aurenta ya mutu a karo na biyu. Bayan ta koma gidan gwaggo Maryam ne masoya biyu suka fito neman aurenta. Hassan mai shagon siyar da kayayyaki da kuma Ɗan Majalisa Hashim Bello. Kowa na mata kwaɗayin auren Ɗan Majalisa, sai dai ita kuma tunaninta daban.
Mai Daki
Hauwa’u Idris ɗaliba ce mai matuƙar ƙoƙari a fannin karatu. Babban burinta shi ne ta zama malamar jinya yayin da ta kammala karatu. Sai dai kash! Mahaifinta ba shi da ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar karatun nata. Hakan ya sa ko da Ishak ya zo neman aurenta kuma ya tabbatar musu da zai barta ta ci gaba da karatu, sai nan da nan suka amince. Abin da ba su sani ba shi ne, Ishak bai da niyyar barin Hauwa’u ta ci gaba da karatu.
Labarinmu
Aleya Saleem ɗaliba ce mai ƙoƙarin gaske. Hakan ya sa Professor Asma’u Sani ta ke yi musu lesson tare da taimaka musu ta fannin karatu domin su samu damar cinye gasar da makarantar Dr. Shaheed ke sa wa a duk shekara. Babbar matsalar Aleya ita ce, mahaifinta na so ya haɗa ta aure da Suhail saboda kuɗin da suke da shi. Ita kuwa Professor Asma’u Sani ta kasa samun nutsuwa ne sakamakon ganin ɗanta wanda rabon da ta ganinsa tun yana ɗan shekaru goma a duniya, yanzu ga shi har ya zama saurayi ɗan kimanin shekaru talatin. Shin ko zai karɓeta a matsayin uwa?
Boyayyen Sirri
A tsawon ‘yar ƙaramar rayuwarta da bata wuce shekaru goma sha shida ba, Eraj ta kasa fahimtar dalilin da yasa ita da mahaifiyarta suke zama a cikin daji tare da dabbobi ba da mutane ‘yan’uwansu ba, ta kuma rasa dalilin da ya sa ya mahaifiyartata ba ta son amsa mata duk wata tambaya da ta shafi danginsu da ‘yan’uwansu. Komai ya canza ne daga ranar da Eraj ta fahimci cewa ita jinin sarauta ce daga tsatson Masarautar Umuapala Royal Kingdom.
Ummu Radiyya
Abakar da matarsa Ummu Radiyya sun gamu tashin hankali mai girma sakamakon kama haya da suka yi a gidan Hajiya Iyami, inda ta hana su cin amarci ta hanyar yin asirin zama mage har zuwa ranar da Abubakar ya buge ta a kai. Gari na wayewa aka kai ta asibiti shi kuma aka ɗaure shi. Shin ko Ummu Radiyya za ta samu mafita a cikin wannan sarƙaƙiya da ta tsinci kanta a ciki?
Jiddo
“Ammey yunwa za ta kashe mu, Ammey wai da gaske Baba Malam shi ne Babanmu?”
Kalaman Zainab kenan, yarinya ‘yar kimanin shekaru takwas da ta taso ta ga yadda ita da iyayenta suke rayuwa cikin mawuyacin hali. Malam Suwiɗi ɗan tsibbu, ya kasance baƙin mugu kuma azzalumi, shi ya sa iyalansa suka zamo abin tausayi a idon duniya. Yayan Jiddo ya so ya raba auren amma ita da kanta ta ce tana son shi. Hakan ya sa mutane da yawa ke cewa ba haka ya barta ba.
Uwata Ce Sila
Ameera yarinya ce ‘yar kimanin shekaru goma sha shida. Kyakkyawar gaske ce ajin farko, sannan tana da ƙira da diri na gani na faɗa. Sai dai duk wannan kyawu nata ya tashi a banza, domin kuwa karuwanci take yi. Ƙanwar mahaifiyarta Zainab, Mom, da kawunta Bala babu irin ƙoƙarin da ba su yi ba wajen ganin sun ganar da ita illar hanyar da ta ɗauka, amma kullum idan sun yi mata magana sai ta ce musu Uwarta ce silar shigarta wannan rayuwar, kuma so take yi ta tara mata kuɗi masu yawa. Babban abin da ke ɗaure wa kowa kai shi ne, in an tambayi uwar ina dalilin faruwar hakan sai ta ce ita ma ba ta sani ba.
Halin Rayuwa
Maryam Abubakar ta ga rayuwa a wannan duniya. Duniyarta gaba ɗaya ta fara birkicewa ne tun tana ‘yar shekara tara a duniya. A wannan lokaci ne mahaifiyarta Ramatu ta rasu, ya zamana Baba Sumaye ce ke kula da ita kamar ita ta haife ta. Zaman kaɗaici kawai suke yi ita da mahaifinta.
To sai dai duk wannan ba komai bane a cikin wahalhalun rayuwarta face ‘wasa farin girki.’
Cikin Baure
Auren Asma’u da Abbas ya kusa, sai dai ko kaɗan ba ta son shi. Hankalinta na kan wani matashin mai kuɗi da ake kira Alhaji Nas, alhali kuwa shi bai san ma tana yi ba. A haka dai aka ɗaura auren ba don tana so ba. Kwaɗayin dukiyar Alhaji Nas da fafutukar ganin ta shiga rayuwar daula suka sa soyayya ta makantar da ita har sai da ta kashe aurenta ta fito domin ta auri Alhaji Nas. Burinta ya cika ta aure shi, sai dai irin halin da ta tsinci kanta a rayuwar zaman gidan ko a mafarki ba ta hango wa kanta hakan ba.
Soyayya Da Rayuwa
Safina da Nabila matan Hassan Hassan ne da Hussaini. Suna zaman lafiya tare da nuna wa juna tsantsar soyayya. Kwatsam rana guda sai Hassan da Hussaini ke faɗa wa matansu cewa za su ƙara aure nan da wata uku. Shin ko matan za su ɗauki wannan labari da sauƙi kuwa?
Aminaina Ko Ita?
Nafisa, kyakkyawar matashiya mai tashe da ji da kanta, ta ɗana wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ambasada Ahmad Ɗangiwa mai suna Haidar tarkon soyayyar ƙarya domin ta samu maƙudan kuɗaɗe a wurinsa. Abin da ba ta sani ba shi ne, rikicin da ke kewaye da ahalin su Haidar ya sha gaban tunaninta, domin kuwa akwai waɗanda suka fi ta son kuɗin da take hangen samu, kuma har kisa za su iya yi domin su cimma burinsu.
Abul-Khair
‘Yan biyu masu matuƙar kama da junansu wato Abul da Khair kyawawa ne na gaban kwatance. Saboda tsabar kamanninsu ma ba kowa ke iya bambance su ba. Sai dai kuma akwai wani ɓoyayyen lamari game da su. Shin ko wane irin lamari ne?
Akan So
Safiyya ta biyewa So da ya makantar da ita ta bi Fu’ad sun yi aure ana gab da yi mata aure da Ado. Wannan ya sa iyayenta suka tsame hannunsu daga komai nata. Shi ma Fu’ad ɗin hakan ce ta faru da shi. Sai dai tashin hankali ya fara ratsowa cikin zamantakewar tasu ne yayin da Fu’ad ya fara nuna ƙiyayyar shi da son haihuwa. Saboda hakan ne ma ya je asibiti aka kashe mishi ƙwayoyin haihuwar shi. Abin da bai sani ba shi ne, Allah Ya riga Ya ƙaddara rabo a tsakaninsu da Safiyya.
Ko Ruwa Na Gama Ba Ki
Kwaɗayin abin duniya ya sa ‘yar gidan Malam Amadu ba wa saurayi kanta har ya yi mata cikin shege. Gashi kuma mahaifinta shi ne limamin ƙauyensu, ciki kuma har ya kai kusan wata biyar ba tare da an ankare ba. Wannan dalili ne ya sa mahaifiyarta Asabe ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata.
Ina Matsalar Take?
Yayin da aka nemi Safwan sama ko ƙasa ba a gan shi ba har na tsawon wasu kwaki, sai mahaifiyarsa Amina ta matsa wa mahaifinsa game da nemo inda yake. Domin har ta fara fatan ina ma ace masu garkuwa da mutane ne suka sace shi, a tunaninta ko ba komai za su ji yana raye kuma su san nawa za su biya. Babban abinda ya fi tayar wa da mahaifin Safwan hankali shi ne irin yadda ya ziyarci ofisoshin ‘Yansanda har biyar amma babu inda aka yi mishi tarbar kirki, sai ma tayin kuɗi da suke masa. To ina matsalar take?
Rayuwata
Zuwan ‘Yan Bindiga rugar su Naja’atu ya yi sanadiyar mutuwar mafi yawa daga cikin ‘yan’uwanta. Yayin da ita kuma garin gudun neman ceton rai ta faɗa hannunsu har shugaban ‘Yan Bindigar ya mayar da ita tamkar matarsa.
Kukan Kurciya
Ana gobe ɗaurin auren Mujahida da masoyinta da suka yi shekaru biyar suna soyayya, wato Nura ya ce ya fasa. A gigice ta shiga gida da taimakon ƙanenta Mujtafa, sai dai shigarta cikin gidan ya yi daidai da furta kalmar saki da mahaifinta wato Habibu ya yi ga mahaifiyarta wato Bilkisu.
Ranar Birthday
Ruƙayya Mohammed (Rukky) ta shirya tsaf domin tunkarar ranar zagayowar haihuwarta da wani irin bazata. Ta sha alwashin kawo gyara, sauyi da kuma canji a zukatan mutane game da yadda aka ɗauki bikin zagayowar ranar haihuwa (wato Birthday Party) a cikin al’ummar Hausawa. Shin ko za ta yi nasara?
Wa Gari Ya Waya?
Tahir yana cikin matsananciyar damuwa, ba komai ya jawo mishi wannan damuwa ba kuwa face matansa guda huɗu. Basma na fama da ciwon ƙwaƙwalwa, Halima na da yawan cin bashi, Latifa amarya kuma yawon bin malamai. Ummul Khair ce kawai mutuniyar kirki a cikinsu. Shin ko Tahir zai iya magance matsalolin da ke ci gaba da tashi a gidansa?
Ibtissam
Adil Bin Mohammed Taufeeq, shi ne ɗalibin da ya fi kowa ƙoƙari da jajircewa a duk cikin ɗaliban da aka yaye daga Columbia University, da ke birnin New York, a wannan shekarar. Suna zaune ne a 5th Avenue tare da ahalinsa wato Prince, Uncle Iron Man, Yaya Big Boss da Kuma Yaya Bobo. Rayuwa ce su ke yi mai cike da jin daɗi, annushuwa da kuma daula. Sai dai akwai wani ɓoyayyen al’amari tattare da wannan ahali nasu.
Abla (Ibtissam), Arwa, Ilham da Husna kuwa, tsintar kansu suka yi a hannun Uwar Karuwai a birnin Abuja. Saboda sun ƙi biye mata su lalace ne ya sa ta haɗa kai da Zinariyya da ‘Yar Shila take gana musu azaba.
Son Zuciya
Hadiza da ‘yan’uwanta suna cikin halin jarabawa sakamakon irin son zuciyar da yake nuna musu. Ba ya basu ci balle sha, kuma bai damu da su ba, amma kullum yana tukubar mai nama ko mai shayi yana morewarsa.
Zuciya
Yayin da lamarin mutanen rugar su Nafisa (Fulani) ya ta’azzara na zarginta da laifin maita, Inna Hure wacce ta zamo wa Nafi bala’i da masifar rayuwa ta haɗa kai da Hinde domin a kai ta birni ta fara aikatau. Malam Iro, mahaifin Nafisa bai su hakan ba, amma babu yadda ya iya. Sai dai tun kafin tafiyar ta yi nisa ta fara fahimtar ba aikatau za a kai ta ba. Shi kuma Yarima Ahmad, wanda ƙaddarar rayuwa ta haɗa shi da Nafisa, aiki za a yi mai wanda har ya ma cire rai da ci gaba da rayuwar duniya baki ɗaya.
Auren Wata Bakwai
Bidiri ne babba ke ƙoƙarin ɓarkewa a Masarautar Benoni, domin kuwa shekarun sarki sun ja, don haka yana gab da yin murabus. Su kuwa matansa kowacce so take yi a ce ɗanta ne ya samu wannan sarauta. Yarima Adeel Muhammad Rohan, wanda shi ne babba, kuma shi ake sa wa rai da samun wannan muƙami na sarki, sam ya ƙi yarda da batun aure, wannan dalili ne ma ya sa mahaifiyarsa ke shirin yi masa auren bazata.
A ɗaya ɓangaren kuma, Zainab (Gaaji) ta zo neman taimako wajen Yarima saboda baffanta ba shi da lafiya, domin ya taimaka mata sai ta aure shi na tsawon wata bakwai a bisa sadaki miliyan uku kuma ba tere da mutanen gidan Sarautar sun sani ba.
Zarina
Abdulmalik Muhammad Bn Abdulmalik (Sultan), shi ne Yariman Daulatul Najees, kasancewar shi da ƙanwarsa Nailah ce kaɗai ‘ya’yan Sarki Muhammad Bn Abdulmalik Yusuf, gab ake da naɗa shi sabon sarki sakamakon murabus da mahaifin nasa zai yi. Mahaifiyarsa Sarauniya Basima da Sarauniya Najyla su kaɗai ne matan sarki. Duk inda ake neman namiji mai izza to Yarima ya kai. Ƙaunar Zarina ta mamaye zuciyarsa ta yadda ba ya tunanin zai iya rayuwa ba tare da ita ba. Babban tashin hankalinsa shi ne mahaifin Zarina, bai san yadda za ta ƙarke a tsakaninsu ba. Amma ya shirya tunkarar komai saboda Zarina.
Wace Ce Ni?
A gidan Alhaji Bello Mustapha, Rabi’atu (Adawiyya) ta zamewa kowa jalli-joga. Shagwaɓarta da ta da tsiyarta take tsulawa irin yadda duk ta ga dama sangarta da son jiki kuwa ba a magana. Dawowar Yaya Almu daga makaranta ce ta sauya komai na gidan, ciki kuwa har da yadda ya zuba wa Adawiyya ido abinda take so babu kwaɓa. Ita kuwa Adawiyya gani take duk abinda yaya Almu yake yi mata ƙiyayya ce da kuma ‘yan’ubanci.
Mijin Ta Ce
Humaira, mahaifiyarta da ƙannenta na fuskantar baƙin kishi da mugunta iri-iri a wurin matar mahaifinsu Alhaji Surajo. Hajiya Majadan ta mallake gidan, sai abin da ta ce a yi ake yi. Shi kuwa Alhaji Surajo babu abin da ya fi ƙi fiye da ganin ɓacin ranta. Hakan ne ma ya sa ta ƙwace girki daga wurin Inna ta kuma hana shi kwana a ɗakinta. Rigimar gidan ta kai ƙololuwa ne yayin da Hajiya Majadan ta ga Inna da cikin wata bakwai kwatsam da rana tsaka.
Hawaye
Lubabatu da mijinta Bello sun sha fama sosai kafin su samu haihuwa, shekaru biyar suka shafe kafin Allah ya ba su Safiyya, tun daga nan kuwa ba su sake samun wani rabon ba har yarinya ta cika shekaru huɗu a duniya. Kwatsam watarana sai wani mai kuɗi da ake kira Alhaji Aminu ya yi wa Safiyya fyaɗe, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta. Wannan mummunan lamari da ya afku ne ya sa Lubabatu ta haɗiyi zuciya ta mutu. Mutuwar iyalinsa ta sa Bello ya shirya ɗaukar fansa a kan Alhaji Aminu. Shin ko zai yi nasara?
Miskilin Namiji
Dr. Zayyad yana cikin gagarumar matsalar da ya rasa ta inda zai ɓullo mata. Iyayensa na jan kunnensa kan ya yi takatsantsan da rayuwarsa, matarsa Sakina ya kasa yarda da ita saboda alwashin da mahaifinta Alhaji Baƙo ya ɗauka na ganin bayansa da na Iyayensa. Samha kuma, wadda ita ce yake sa ran samun masalaha a dalilinta ta zamo masa ƙurjin gwiwa. Sai dai duk wannan rikici ya samo asali ne daga rashin jin shawarar iyayensa a lokacin da zai auri Sakina.
Kaddarata
Rayuwa takan zo wa wasu da sauƙi, wasu kuma takan zo musu da akasin haka. Rayuwar Fatima Zahra cike take da ƙalubale, kuma ga dukkan alamu ba ta gama fuskantar ƙalubalen ba.
Tsaka Mai Wuya
Umar Bin Ally ba shi da aikin yi a kullum face kula ‘yanmata a shafin sada zumunta na facebook. Kusan kullum sai ya yi sabuwar budurwa, bisa tsautsayi wata rana sai ya fara soyayya da matar ministan tsaro na ƙasa ba tare da ya sani ba.
Martabarmu
Ahmadi cikakken ɗan boko ne, auren soyayya suka yi shi da matarsa Maimuna wacce kuma ‘yar danginsu ne. Sai dai rikici ya ratso cikin zaman lafiyar da suke yi da juna ne daga lokacin da ya sa ɗambar auren Maryam wadda ita ma ‘yar danginsu ce.
Hukuncin Allah
Salim matashi ne da bai yarda da cewa abubuwa suna faruwa ba ne a bisa yadda Allah ya ƙaddara za su faru ba. Abinda ya aminta da shi kawai shi ne, duk wani mummunan abu da ka ga ya faru, to sakacin wanda abin ya faru gare shi ne ya ja mishi.
Fatalwar Sinu
Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.
Tun A Duniya
Alhaji Garba ya shiga wani irin mummunan hali na ban mamaki. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk dukiyar da ya tara ta salwanta, sannan lafiyarsa ma kanta ta fara ƙoƙarin ƙaurace masa.
Amnah
Amnah nutsattsiyar matashiya ce mai kyau da kamala, domin har sauka ta yi. Sai dai mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki ne ya sa ta shiga harkar karuwanci, a harkar karuwancin ma har tarihi take ƙoƙarin kafawa na ganin cewa duk mutumin da ya yi tarayya da shi ba ta ƙarawa. To sai dai kuma ta kamu da soyayyar matashi Taufiq. Shin ko za ta samu cikar burinta?
Kasaitar So
Zaid sangartaccen matashi ne wanda ke ji da kansa da kuma taƙama da kuɗi. Yana da yaransa ‘yan daba da ke masa aiki, su ne Gaye, Mugu da kuma Wizzy. Ƙaddarar rayuwa ta sa Gaye ya fara bibiyar Jidda, wadda ƙanwar Ibteesam ce wato Maryam, zafin rai irin na Ibteesam ya sa ta yi musu kaca-kaca, shi kuma tun daga nan ya sha alwashin sai ya lalata mata rayuwa.
Allah Daya Gari Banban
Yayin da matar Abdullahi masunci ta haihu a karo na goma a rayuwarta, sun yi farin ciki sosai. Hakan ne ma ya sa Abdullahi tafiya bakin kogi domin ya yi su ya samo abinda zai ciyar da iyalansa. Amma wani abin mamaki shi ne, sai da ya yi kwanaki arba’in yana zuwa su ba tare da ya kama ko da kwaɗo ba, ga shi yana matuƙar jin kunyar mai gurasa wanda ke binsa bashin da yake ta bashi a kullum ba tare da gajiya ba.
Nawa Bangaren
Gimbiya Naheela ita ce ‘ya guda ɗaya tilo a wurin sarkin aljanun Zuwatu, wato Zawatunduma. Naheela ta jarabtu da soyayyar Yarima Naheel ɗan sarkin aljanu Zimba, sai dai shi kuma baya son ta, ya tsane ta matuƙa. Wannan dalili ne ya sa ta aika Zamzila domin ya nemo mata inda Yariman ya ɓoye.
Alkawarin Allah
Alhaji Usman Ibrahim Matawalle ba ya barin kowa zuwa zance wajen ‘ya’yansa, watau Maryam da Fatima saboda mutum ne shi mai zafi sosai. Soyayyar Maryam ta kama Nuraddeen, kuma sai bibiyarta yake yi har sai da ya gano gidansu. Shin ko zai dace da samun soyayyar Maryam tare da amincewar mahaifinta?
Sirrin Boye
Mairo yarinya ce mai kaza-kazar, bata da son jiki ko yanƙwana. Talakawa ne su masu rufin asiri. Tana da yayye guda biyu, Amadu da Kabiru. Tana matuƙar tsoron Yaya Amadu, sannan ta shaƙu sosai da Yaya Kabiru. Babban abin da ke ɗaure wa Mairo kai shi ne irin yadda ba sa so Kulu tana raɓar inda take, ta kasa fahimtar wane irin ɓoyayyen sirri ne ke tattare da Kulu wadda tun tana ƙarama take fama da cuta mai kama da ta hauka.
Zuciya Da Hawaye
Rumana tana cikin wani irin mummunan hali sakamakon farmakin da mahaifinta ke yawan kai mata don ganin ya cimma burinsa. Alhaji ya damu sosai bisa mafarkin da ya yi da masoyinsa Jabir, yayin da ita kuma Zully take fusace da mahaifinta sakamakon irin azabar da yake gana wa mahaifiyarta. Shin me ke faruwa ne a cikin zukatansu? Me ke hana duk wanda ya yi yunƙurin keta wa Rumana haddi damar cimma burinsa?
Mafarkin Deluwa
Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maƙabarta ce da ke ƙauyen Ɗanduƙus. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maƙabartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.
Kaddarar Safwan
Safna da Safwan ɗalibai ne a jami’ar Ahmadu Bello University da ke Zaria. Kowa tunani yake soyayya suke yi, amma su a tsakaninsu zumunci kawai suke yi. Safwan na son karatu sosai, kuma yana da alheri tare da kula mutane babu wulaƙanci. Babban damuwar Safwan ita ce shaye-shaye.
Meenal
Kyakkyawar matashiya mai taƙama da kyau, kuɗi da kuma ilimi wadda ake kira Meenal ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa yin soyayya ba ballantana ta yi aure, domin ita a nata tunanin, babu wani sauran abu kuma da za ta yi sha’awa a wurin ɗa namiji da har zai kai ta ga yin aure. Me ya sa Meenal ta tsani maza? Me ya sa ba ta da ƙawaye?
Uban Da Ba Namu Ba
Tanimu Sambo wanda aka fi sani da Baban Nawwara malamin makaranta ne da ke koyarwa a wata makarantar mata. Jajircewa da ƙwazonsa a ɓangaren koyarwa tare da tsayuwa akan gaskiya suka sa ya ƙi yarda ɗalibansa su ba da kuɗi domin a basu amsar jarabawar fita daga Sakandare. Maimakon haka, sai ma dagewa da ya yi wajen horas da su yadda za su amsa tambayoyin yadda ya kamata.
Ko Wace Kwarya
Allah ya albarkaci Umma Saratu da ‘ya mai hankali, kyau, nutsuwa da kuma ilimi wadda ake kira da Zaliha. Zaliha na soyayya da wani malamin Islamiyyarsu mai suna Abdullahi. Shi ma mutumin kirki ne kuma ɗan aminin mahaifin Zaliha ne. Malam Sirajo, wato mahaifin Zaliha ya yarda da Abdullahi sosai, amma ita Umma Saratu ta fi so Zaliha ta auri Alhaji Saminu saboda yana da kuɗi, alhali ita Zaliha ba ta son shi. Hakan ya sa Umma Saratu, tare da taimakon ƙawarta Yahanasu suka je wurin boka domin ya basu maganin da za su raba tsakanin masoyan. Shin ko za su yi nasara?
Yar Wanke Wanke
Sadeeq ya tsani ya ji an yi mishi maganar aure, duk kuwa da cewa ya kai minzalin yin auren kuma Allah ya hore masa abinda zai yi auren.
Halin babu da ƙaddarar rayuwa ta sa Hameeda da mahaifiyarta zuwa aikin gidan su Sadeeq domin ta maye gurbin mahaifiyartata s matsayin ‘yar aikin gidan. Sai dai bisa ƙaddara, tun daga wannan rana Sadeeq da Hameeda suka fara samun matsala da juna.
Nacina Ya Jawo Mini
Saee’da yarinya mai haƙuri tare da ƙwazon karatu, tare da mahaifiyarta suna fuskantar cin kashi a wurin kishiyar mamanta wato Umma Kande da ‘ya’yanta su Nusaiba. Saee’da na son karatu sosai, amma bata da halin biya, mahaifinsu na da shi amma Umma Kande ba za ta bari ya biya mata ba. Shi kuwa Sadam, baya son zuwa karatu Jami’ar Oxford kamar yadda aka saba tura sauran ‘yan gidan nasu.
Nakasar Zuci
Abubuwa sun taru sun yi wa Badi’a jingim a ka, sakamakon sakin da mijinta Adamu ya yi mata da tsakar dare bayan da ya gano cewa tana da cikin wata uku a jikinta, alhali ba su wuce wata ɗaya da ‘yan kwanaki da yin auren ba. Ga shi mahaifinta ya ce in har ta baro gidan miji kada ta zo mishi gida, ko yaya za ta yi?
Tsantsar So
Labibu ɗan gaye ya maida Hazel tamkar abokiyar wasansa, kullum sai sun ci karo da juna kuma kullum sai ta ba shi haƙuri duk kuwa da cewa da gangan yake yi. Ita kuwa Teemah, shaƙuwa ce ta ƙullu tsakaninta da Kyakkyawar baƙuwar Amurka, wato Sameera Adila Dina. Ko mene ne labarin Sameera da dalilin Zuwanta Nigeria?
Tsakaninmu
Sa’adatu yar gidan Abida da Habibu wacce ‘ya ce da ta shiga ran iyayenta da kuma ‘yanuwanta sosai musamman ma yayanta Abdallah, duk dai ba uwa daya ce ta haife su ba. Amma duk da wannan soyayyar bai hana Sa’adatu gamuwa da kaddarori na rayuwa da suka wuce shekarunta ba, shin Sa’adatu za ta ga karshen matsalolinta?
Fadime
Bayan Uwale ta yi wa ‘yar mijinta Faɗime asiri ta haukace,’ yarta Hainsai na ganin cewa ta fidda ita kawai daga ƙauyen kowa ya huta. Sai dai Uwale ba za ta iya ba saboda sharuɗɗan da aka gindaya mata. Kuma a shirye take ta bi takan ko waye domin cikar burinta. Sai dai ƙaddarar da ke cikin rayuwarsu duka mai girma ce.
Rumfar Kara
Malam Iliyasu shahararren malamin addinin Musulunci ne da ke da kima da daraja a idon jama’a. Sai da sai dai ɗansa Sidi bai biyo halinsa ba. Hakan ya ƙara fitowa ne bayan ya yi wa tsohuwar budurwarsa Hanan ciki, ita kuma ta je ta sanarwa mahaifinsa. A gefe kuma ga Halima, wadda ta biyewa su Gwaska da Hayat wajen neman abin duniya ta gurɓata rayuwarta.
Tekun Labarai
Bayan Sarki Shamsuddini da matarsa sun gudu da tsakar dare domin su tsira daga harin da waziri Ashfanu da mabiyansa suka kawo musu. Dole tausa suka bar ɗansu jariri a tsakiyar dokar daji. Bayan komai ya lafa sai suka yi neman duniya amma basu ganshi ba. Sai dai ƙaddara ba ta gama jaraba su ba, domin kuwa ɗa ya dawo gidan ubansa ba tare da shi kanshi ya sani ba.
Tsanin Nasara
Duk da cewa amaryar ta jima a gidan mijinta har ma ta tara yara. Gwalagwalan shawarwarin da mahaifinta ya ba ta sun zamo mata tsanin hawa matakin nasara a gidan aurenta da ma rayuwarta baki ɗaya.
Soyayyar Da Na Yi
Mamma ta fidda rai gaba ɗaya da samun soyayyar gaskiya sakamakon rashin masoyinta Abdul da ta yi a baya. Ga kuma wani matashin saurayin na ƙoƙarin kunno kai cikin rayuwarta a wani irin yanayi mai ban mamaki.
Marigayiya
Bayan tarin wahalhalu da kuma ƙalubalen da suka fuskanta kafin su yi aure, Rumy ta yanke shawarar yin amfani da kayan amfanin yau da kullum ɗin mijinta domin ita ma ta kamu da irin cutar da ke damun shi, wato cuta mai karya garkuwar jiki.
Lailerh Mansoor
Uncle Idris ya yi ƙoƙari sosai wajen samo wa Lailerh scholarship ɗin karatu duba da cewa ita ce ta samu lambar yabo ta Best Student Of The Year kuma tana da baiwar ɗinki, ba ya so ta rasa wannan damar. Babbar matsalar ita ce, mahaifiyarta da ake kira da Ammi ba ta son rabuwa da ‘yar tata.
Waye Zabin Munibat?
Munibat natsattsiyar yarinya ce, maraici ya sa ta shiga cikin uƙuba a hannun matar mahaifinta wadda a kullum take nuna mata ƙauna a fili, a ɓoye kuma tana gasa mata gyaɗa a hannu. Shin wane zaɓi Munibat take da shi? Yaya za ta yi wajen ganin ta fita daga wannan ƙangi?
Lullubin Biri
Hankalin Yusuf ya yi matuƙar tashi sakamakon halin da matar da aka kwantar a asibitin take ciki, matsananciyar damuwa ce take fama da ita wadda har ta kai ta ga fita hayyacinta. A gefe kuma, Fillo (Halimatu) da masoyinta Amir suna ci gaba da more soyayyar su, har ma maganar aure ta shiga tsakani. Kwatsam sai Turaki, wanda ke ɗauke da wani ɓoyayyen sirri ya shigo cikin rayuwar Halima. Shin ko menene wannan sirrin.
Wa Ya Kashe Zahra'u?
Matakin tashin hankali da ruɗanin da ya ɓarke a gidan Alhaji Aliyu Ibrahim MD ya kai maƙura, yayin da aka wayi garin ranar ɗaurin auren ‘yarsa guda ɗaya tilo a duniya aka same ta a mace. Angon nata, wato Zayyan ya suma sakamakon jin wannan mummunan labari. APC da DCP Sardauna suna ta bincike domin gano wanda ya shigo har cikin gidan ya kashe Zahara’u duk kuwa da tarin matakan tsaron da ke gidan.
Ya'yanmu
Rayuwar zaman marina ake yi a Unguwar Hayin Talaka. Unguwa ce ta talakawan da basu san ciwon kansu ba ballanta na ‘ya’yansu. Rayuwa ce ake yi cikin rashin tsafta, nutsuwa da sanin yakamata. Ko yaya rayuwar yara masu tasowa a wannan Unguwar za ta kasance a gaba? Shin ko za su samu mafita?
Sa'adatu
Zarah da Ahmed masoyan juna ne, soyayyarsu har ta kai ga an saka ranar aurensu. Ana saura sati biyu bikin ne sai aka sace Zarah, ba kowa ne ya sace ta ba face Aljana Zainab da masoyinta Safwan ɗan sarkin aljanu. Sun yi hakan ne kuma domin su cimma wani mummunan ƙuduri nasu da suke da shi akan waɗannan masoya.
Akwai Ciwo
Akan ce ‘naka shi ke ba da kai’, Jidda ta ga gaskiyar hakan a zahiri yayin da ta tsinci kanta a matsayin marainiyar da ‘yan’uwa suka yi watsi da ita. Ƙuncin rayuwa tare da tunanin yadda za ta ciyar da kanta da ƙannenta ne ya sa ta faɗawa ashararanci ba tare da ta yi tunanin abinda zai biyo baya ba.
Almajirai Ma 'Ya'ya Ne
Sa’idu da Halliru sun zamo tsayayyu kuma bayyanannun misalai na irin mummunan halin da al’majirai ke faɗawa a cikin rayuwarsu ta al’majiranci. Duk da cewa an nuna irin yadda mugun halin mutanen zamani yake game da al’majirai har suke cutar da su, Hajiya Maryam ta fita zakka tare da zamowa misalin da kowa zai so zama kamarta.
Sanadin Kaddaratata
Dattijo Malam Inuwa da matarsa Gaje sun fito daga gida kenan domin zuwa asibiti sai suka ci karo da wata matashiya na ƙoƙarin kwance goyon da ke bayanta. Hakan ya sa ya yi sauri ya nufi gidan Mai Gari domin ya sanar masa. Ita kuwa Gaje, tsoro ne ya hana ta aikata komai har matashiyar ta aje jaririn ta yi gaba. A yayin da Mai Gari ke ƙoƙarin yin bincike game da wannan jaririya da aka tsinta, Habi matar Malam Habu kuwa tuni har ta fara kitsa wani mummunan shiri akan wannan jaririya.
Sakamakon Zunubi
Hamshaƙan masu kuɗi guda uku, wato Sir Benjamin, Alhaji Mu’azzam Gidan Dala da kuma Alhaji Habu, waɗanda kowannensu biloniya ne, sun haɗa kai sun gina wani katafaren Estate a bayan gari inda suke zaune tare da ahalinsu gaba ɗaya. A cikin wannan estate, akwai komai da suke da buƙata, don haka ba bu ruwansu da sauran jama’ar waje. Shi ya sa ake kiran su da Billionaire’s Family a jimillance. Akwai cakwakiya iri-iri da ke faruwa a Estate ɗin nan, musamman a tsakanin ‘yan matan gidan waɗanda suka ƙwallafa ransu a kan Captain Henry, ga kuma ‘yan aiki Amali da Julia waɗanda ke fuskantar mabanbantan ƙalubale a wajen mutanen gidan.
Yar Karuwa
Rayuwa ta yi wa Banafsha ƙunci sakamakon irin abin da mahaifiyarta Mami ke aikatawa, wato karuwanci. Babu irin ƙoƙarin da ba ta yi ba wajen ganin mahaifiyar tata ta daina wannan aiki, domin ita a ganinta, sana’a ce ta ke yi, sana’ar da da ita take ɗaukar ɗawainiyar Banafshan tun tana ƙarama. Bayan munanan kalaman da Banafsha ke sha a gari, babban abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne abin da zai faru gareta idan ta tashi yin aure.
Ina So
Halima mace ce mai kamun kai da shiga ta kamala a kowane lokaci, ba ta taɓa bayyana fuskarta hatta a wurin aikinta. Kullum cikin saka niƙabi take. Rayuwarta ta canza ne sakamakon dawowar ɗan mai kamfanin da take yi wa aiki daga ƙasar waje. Shin ko izzar Ali za ta yi tasiri akan Halima?
Lokaci
Alhaji Yusuf na kwance yana barci sai ga kiran ƙaninsa Khamis cewa ya zo ofishin C.I.D cikin gaggawa ya fitar da shi daga komar wata azababbiyar mace da ta jawo mishi jarfar da bai san yadda zai yi da ita ba. Wace ce ita? Kuma wanene mai gaskiya a cikinsu?
Rayuwarmu
Hajiya Beeba ta asirce Auwal domin ganin ta mallake shi ko ta halin ƙaƙa. A sanadiyar wannan asiri ne har ta raba shi da matarsa ta farko, kula da su ya dawo hannun Dawud duk da ƙarancin shekarunsa. Tashin hankali ya yi wa Labeeb yawa, abubuwa sun cukurkuɗe mishi. Dukkan ‘yan gidansu sun canza mishi. Ga Dawud na fushi da shi saboda cikin da ke jikin Zulfa, ga yaro an kawo mai da bai san daga inda ya fito ba, ga matarsa na neman rabuwa da shi, babban abokin shi ba sa ko magana, kwatsam kuma sai ƙaramin ƙanin shi ya mutu.
Rigar Siliki
Mujahid da Binta ‘yan dangi ɗaya ne. Akwai kyakkyawar fahimtar juna sosai a tsakanin su, domin ya zamo mai share mata kukanta a kowane lokaci. Abinda ba ta sani ba shi ne, Mujahid na matuƙar ƙaunarta fiye da komai na duniya. Sai dai kuma ta zaɓi Shukuranu a matsayin miji ba tare da ta san yana da wata gagarumar matsala ba.
Kishiyar Katsina
Tataburza ta fara wakana a gidan Khamis tun bayan da matarsa ta farko, Aisha ta ji cewa zai mata kishiya, kuma ‘yar Katsina ce. Wannan dalili ne ya sa ta ɗau aniyar ajiye kyawawan halayenta da aka sani tare da ɗaukar sabbi bisa shawarar ƙawarta Zuzee domin tabbatar da cewa Maryam, wato amarya ba ta samu sararin yin numfashin kirki gidan ba. Duk wannan saboda dalili ɗaya: ‘Wai an ce mata ‘yan Katsina suna da asiri.
Yini Sittin Da Daya
A fadar sarkin namun dawa, wato Zaki. Dabbobin dawa, manya da ƙanana kan zo masa da labarai iri-iri domin tattaunawa da samo mafita a cikin al’amuran yau da kullum irin nasu na dabbobi wanda yake kamanceceniya da namu na mutane.
Kuskuren Wasu
Khadija ta yi kuskure mai girma a rayuwarta, ciki kuwa har da na rabuwa da ‘yarta. Maryam ita ma ta yi kuskure mai girma, musamman na auren mijin da bai san daraja da kimarta ba. Fatima kuwa da-na-sani ne ya kamata yayin da mijinta Kabir ya fara nuna mata asalin halinsa. Alawiyya na matuƙar son mijinta, sai dai kuma wata ƙawarta na neman jefa ta cikin bala’i.
Jini Ba Ya Maganin Kishirwa
Kamal ya shirya tsaf domin ganin ya auri Hajiya Shema’u, duk kuwa da tazarar shekarun da ke tsakaninsu. Shi dai kawai miliyan ashirin ɗin da zai samu yake hange. Wannan dalili ne ya sa har suka fara samun matsala da babban abokinsa Zayyad da kuma ƙanwarsa Farida. Ita kuwa matarsa ta fari, Sakinah, haƙuri kawai take yi tare da maida komai ba komai ba. Shin ko zai hankalta ya sauka daga kan keken ɓeran da yake ƙoƙarin jefa kanshi?
Fansar Fatalwa
Ƙawaye sun yi wa Amrah mummunan lahani a rayuwa, wanda hakan ne ya zamo silar mutuwar ta. Hakan ya sa ta dawo a matsayin fatalwa tare da shan alwashin ɗaukar fansa a kansu. A bisa wannan dalili ne ta kawo wa Afrah farmaki ana saura kwana uku bikinta da masoyinta, wato Anwar. Shin wa kuma za ta kai wa hari na gaba?
Na Sake Ta
Hamshaƙin matashin mai kuɗin da ake ji da shi, wato Usman One boy ya samu Kamal mayen kuɗi da batun wani irin kasuwanci mai ban mamaki. Usman ya yi alƙawarin ba wa Kamal kuɗi naira na gugar naira har miliyan biyar, matuƙar dai ya yarda zai saki matarsa Hajir domin ya aure ta. Ashe Kamal na gab ne da fahimtar cewa ba komai bane kuɗi ke iya yi wa mutum.
Muradin Rai
Alhaji Kasim Banazir ƙasurgumin ɗan kasuwa ne a fili, a ɓoye kuma gogaggen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi. Yana da wata kyakkyawar ‘ya guda ɗaya da yake matuƙar ji da ita, sunanta Nooreyn. Nooreyn da Ekram tare da Saleym sun je River Kaduna domin yin wani shagali, kwatsam sai ta ci karo da wani mutum ruwa ya jawo shi daga wani wuri, jikinsa duk tabbai.
Abinda Babba Ya Hango
Okasha Sani Sa’id matashi ne mai taƙama da kuɗi da kyawun halitta. Hakan ya sa yake wasa da hankulan ‘yanmata tare da ɓata musu rayuwa. Ƙaddara ce ta haɗa shi da Jameela, wadda ta bijirewa shawarar mahaifinta ta auri Okasha ba don suna so ba. Kash! Da ta san abin da zai biyo baya da ba ta yi wannan aure ba.
Nisfu Deeniy
Nadeefah Yusuf Yerwa, wacce a gidansu ake kira da Lele, kyakkyawar budurwa ce ajin farko. Allah ya jarrabe ta da son Burhan Abdallah Yerwa wanda ake kira da Islaam, son da take yi masa ya yi ƙarfin da har sai da ta fito fili ta faɗa mishi abinda ke cikin zuciyarta. Sai dai shi kuma ba ya sonta, bai ma ɗauketa da muhimmancin da zai iya ko kula ta ba, a madadin hakan, Suliem Aliyu Yerwa yake so, ita kuma bata ma san yana yi ba. Wannan soyayya ta mutane uku kuma ‘yan ahali ɗaya tana ɗauke da jimirɗa sosai. Waye zai yi nasara?
Al-Mustapha
Malam Jibrin da matarsa Larai sun saka wa Al-mustapha (Baɗɗo) karan tsana tare da ba shi aikin wahala saboda mahaifiyarsa ba ta gidan. Wasu lokutan Malam Jibrin da kanshi kan yi mamakin irin yadda yake nuna wa ɗansa tsana tare da kasa tantance cewa Al-mustapha jininsa ne ko ba jininsa bane.
Baragurbin Kyau
Mardiyya da Hamdan masoyan juna ne. Sun yi auren soyayya har Allah ya azurta su da Shahid. Komai na tafiya musu daidai a rayuwa, kafin babbar aminiyar Mardiyya wato Zainab ta shigo cikin rayuwarsu. Tun daga wannan lokaci ne zaman lafiya ya ƙaurace musu har sai da ta kai su ga rabuwa. Mardiyya ta sha alwashin ƙin yarda da kowa a gaba bisa wannan cin amana.
Ameera Da Adam
Adam, wanda suka yi auren soyayya shi da matarsa Ameera ya shiga cikin wani irin yanayi mai wuyar faɗa. Ameera ta canza daga yadda take, tun bayan da ta samu ciki ta zama masifaffiya ajin farko, abin har ya kai ga tana dukan mijinta tare da korarsa daga gida. Ko yaya zaman nasu zai ci gaba da kasancewa?
Dutse Daya
Bayan an yi wa Nana Aisha aiki har an ciro yara guda biyu, kai tsaye likita ya sanar wa da Haidar, cewa Nana ta rasu. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma, ga Dr. Lurwanu na fushi da shi bisa maganar da ya furta game da son yaran su rayu fiye da uwar tasu, gashi yanzu maganar ta tabbata. Ana binne ta kuwa ya faɗi sumamme, yayin da su Maman Hafiz kuma suka shiga yada zance a kan mai rasuwar bisa zargin ta asirce musu ɗan’uwa.
So Da Buri
Kishin da Umma ke yi da Maman Huda ya sa ta ɗauki karar tsana ta ɗora mata. Duk wani aikin gidan ita ake jibge wa ta yi, duk kuwa da cewa Jalila na nan, amma sai su fake da cewa ai ita tana zuwa makaranta. Jafar kuwa, dukan tsiya yake yi mata. Kaf gidan Junaidu ne kaɗai yake tausaya mata, wanda hakan ya sa Umma kullum cikin yi masa balbalin bala’i take.
Ko Da So
Mukhtar Adam da matarsa Hafsat Muhammad auren soyayya suka yi, kuma suna ƙaunar juna fiye da tsammani. Allah ya albarka ce su da ‘ya’ya har guda uku, Abdalla, Kursum da kuma Aiman. Komai na tafiya musu daidai kafin zuwan wata rana, ranar da ta canza komai na rayuwarsu, ranar da Mukhtar ya sauya daga yadda Hafsat ta san shi, ranar da ya furta mata kalmar saki!
Ba ta taɓɓa tsammanin hakan daga gare shi ba, ba kuma ta san dalilin hakan ba. Ko zuciyarta za ta iya ɗaukar irin wannan hukuncin?
Yadda Kaddara Ta So
Tafida likita ne, kuma shi ne tafidan masarautar haɗeja. Kyakkyawa ne sosai kuma ga shi da kuɗi, mata da yawa na son sa, samari ma da sauran mutane haka. Sai dai yana fama da wata irin lalura da aka rasa gane kanta. Lokaci bayan lokaci wani shaiɗanin ruhi kan ziyarce, kuma a duk lokacin da ya kawo masa wannan ziyara, sai ya rikiɗe ya zama wani irin dodo mai ban tsoro.
Kwaya Tushen Tsiya
Ƙalubalen rayuwa ya sa wani matashi yanke shawarar shan miyagun ƙwayoyi domin su taimaka mishi wajen ɗaukar fansa. Abinda bai sani ba shi ne, su ma ƙwayoyin tasu rigimar ta musamman ce.
Kuskuren Waye?
Halima da Zarah maƙwafta ne kuma ƙawaye. Makarantarsu ma ɗaya. Suna tsaka da rayuwarsu mahaifin Zahra ya ba da ita ga Hafiz. Babbar matsalar ita ce, mahaifiyar Hafiz ba ta son wannan haɗi da za a yi duk kuwa da cewa su yaran sun fara kamuwa da son juna. Ko ya za ta kaya a tsakaninsu?
Rai Da Kaddara
Shin ko Daada za ta iya riƙe amanar Nawfal da Madina kamar yadda ta yi alƙawari? Sai zuwa yaushe ne Nawfal zai samu sauƙin halin kaɗaicin da ya riga ya saba da shi a gidan Julde? Matuƙar da rai, to ƙaddara za ta biyo baya. Yadda za su yi da wannan ƙaddara kuwa zaɓinsu ne.
Mijina Wukar Fidar Cikina
Salahuddeen na kwance tare da matarsa Muhibbat sai ga kidnappers sun yi musu dirar mikiya inda suka ɗauke shi tare da yi wa matarsa dukan tsiya. Bayan kwana huɗu da faruwar hakan sai suka buƙaci da a basu miliyan ɗari. To sai dai yanayin yadda suka san bayanai game da surikar Salahuddeen ya tabbatar da cewa akwai wani makusanci da ke basu bayanai a ɓoye. To amma waye?
Bincike
Sipeta Sani ƙawararren Ɗan Sanda ne da bai san faɗuwa ba a aikinsa, sai dai garkuwa da ɗan minista da wasu ɓata gari suka yi na nema ya kai masa ruwa rana a bincikensa.
A Daren Farko
Duk da cewa Dr. Jidda Abubakar Aliyu ƙwararriyar likita ce a fannin cututtukan mata da yara, hakan baya nufin ita ma ba ta da damuwar da ke damunta. Musamman wani mafarki da ya nace mata, wanda kuma duk in ta yi shi sai ta ji ta a sususce. Shi kuwa Dr. Sani, soyayya ce ta rabo shi da Kaduna ta kawo shi Katsina neman Jidda ba tare da ya taɓa ganin ta balle ya san inda zai same ta.
Zinariya
Tashin hankalin da ya afku a ƙauyen su Hamida ne ya sa ta rasa ‘yanuwanta gaba ɗaya kuma ta koma rayuwa a daji. A cikin wannan yanayi ne ta haifi Zinariya, kuma ba da jimawa ba ta rasu. Sarauniya Jahiyana wadda ke mulkin masarautar aljanu ta Gimatuwa ce ta tsince ta a dokar daji ta kai ta gidanta kuma har ya aiyana ta a matsayin wadda za ta gaje ta. Sai dai kuma wannan shiri bai yi wa gimbiya Juhaina daɗi ba. Shin ko yaya za ta ƙarke a tsakaninsu?
Indo A Birni
Indo ta gallabi mutanen ƙauyensu baki ɗaya. Kowa ƙorafi yake yi da ita, abu ya yi tsamari dai har da kai ta ƙara gaban Mai Gari, kullum iyayenta mutanen kirki suna zarya wajen magance matsalolin da take jawo musu amma kamar ba sa yi. Sai dai duk da wannan hauka da rashin kan gado nata, Allah ya jarrabe ta da soyayyar Muhammad Mustapha wanda ke zuwa daga birni. Anya kuwa za ta samu shiga a wurinsa? Musamman da yake akwai wata ‘yar uwar tasa ma a birni da take son shi amma ba ya ko kula ta.
Kudi Ko Rai
Alhaji Ahmad Mukhtar na ta faman kashe kuɗi wajen ganin ya samar wa ɗansa guda ɗaya tilo wato Mashkur lafiya amma abu ya ci tura. Sai dai duk da haka ya sha alwashin ƙarar da dukiyarsa gaba ɗaya wajen nema wa ɗan nasa lafiya. Abinda bai sani ba shi ne, matarsa Zinatu na da hannu dumu-dumu bisa rashin lafiyar ɗan nasa.
Labarin Asiya
Ba tare da tunanin komai ba Asiya A Baba ta shiga asibiti domin karɓar sakamakon gwajin da ta yi ranar Larabar da ta wuce. Sai dai hankalinta ya yi matuƙar tashi da jin cewa tana ɗauke da cutar ƙanjamau. Hakan ya sa ita da mijinta Hassan zuwa wani asibitin suka yi wani gwajin, sai dai a nan ɗin ma dai sakamakon iri ɗaya ne, ita da shi duka suna ɗauke da cutar. Babban tashin hankalin Asiya shi ne ba ta taɓa zina ba, don haka kai tsaye ta fara tunanin Hassan ne ya saka mata cutar.
Wata Rayuwa Ce
Alhaji Buhari hamshaƙin mai kuɗi ne na gaban kwatance, sai dai matarsa Hajiya Jamila ta hana shi saƙat saboda neman abin duniya. Wannan dalili ne ma ya sa ta sa Maza da Alamz suka sace Sadiya da ‘yarta suka jefar da ita. Ya zama dole Alhaji Buhari da amininsa Alhaji Saleh su nemo Sadiya matuƙar suna so burinsu ya cika.
Inuwa Daya
Fadila ta shirya tsaf domin ganin ta auri Uban riƙonta ko da kuwa duniya za ta yi Allah-wadai da ita, matuƙar dai za ta samu damar zama inuwa ɗaya da mai tarin arziƙi. Alhaji ya dage kan cewa lallai zai ƙara aure, kuma budurwa zai aura. Wannan dalili ne ya Hajiya Amina ta kasa zaune ta kasa tsaye wajen ganin ta samu mafita dangane da wannan ɗanyen aikin da yake ƙoƙarin jawo mata. A gefe kuma, babbar aminyarta Hajiya Baratu ba ta da burin da ya wuce ita ma ta aure mata miji. Tsakanin Fadila da Baratu wa zai yi nasarar aure Alhaji?
Barrister
Burin Yazid na zama Barrister ya cika, dukkan ‘yan’uwansa kowa sai taya shi murna yake yi. Ita kuwa Nadiya, ta ƙwallafa rai akan Yazid, babu abinda take so face ganin ta aure shi, duk kuwa da cewa shi ba sonta yake yi ba. Zahra na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon ciwon da mahaifiyarta ke yi wanda take buƙatar kuɗin kai ta asibiti. Ga kuma yayarta Zainab da kullum ba ta da aiki face musguna mata.
Ummu Hani
Rayuwar Ummu Hani ta sauya cikin dare ɗaya, bayan mahaifiyarsu ta rasu ta barta da ƙanne biyar ba tare da wanda zai kula da su ba, ciki kuwa har da jariri sabon haihuwa. Sai dai ta ɗauki aniyar kulawa da ƙannen nata ko ana ha maza ana ha mata.
Dare Daya
Salim ya shiga cikin jarrabawa babba. Shekaru uku kenan da kammala karatunsa amma har yanzu bai samu aikin yi ba. Kwatsam! Ana cikin haka kuma sai wani mai mota ya bige mahaifiyarsa, inda har ta samu karaya bakwai a jikinta. Likita ya bayyana za a yi mata aiki, amma ana buƙatar Naira miliyan uku domin yin aikin. Ga shi Salim ba shi da kosisi.
Kukan Zuci
Khamilarh da Khalilarh suna fuskantar musgunawa da cin fuska kusan iri ɗaya duk kuwa da cewa ba a wuri ɗaya suke rayuwa ba. Sai dai abinda ba su sani ba shi ne, ba wai kyawu, haƙuri ko nagartar hali kawai suka haɗa ba. Da alama suna da wata ɓoyayyiyar alaƙa wacce duk ranar da suka santa za ta girgiza su.
I Am Not Your Punching Bag
I Am Not Your Punching Bag And Other Stories is a collection of short moral and interesting stories depicting the daily struggles of African woman.
Lokaci Ne
Umaima ta shiga cikin damuwa sosai tun bayan da mahaifiyarta Salamatu ta kirata a waya domin ta ƙara jaddada mata batun gudunmuwar bikin ‘yar’uwarta Hamida da aka saka dubu goma sha biyar. Kuma idan ba ta ba da kuɗin nan ba ta san mahaifiyarta sai ta yi fushi da ita. Ita kuma ga shi ba sana’a take yi ba, kuma ta san halin birkitaccen mijinta Lawal sarai, in ma ta tambaye shi ba lallai su wanye lafiya ba. Maimuna ce kaɗai take sa ran samun sauƙi daga gareta. Ko za ta samu mafita?
Doctor Hassan
Doctor Hassan ya daina so matarsa Falmata, ya tsane ta kuma har mayya yake kiranta tare da dukanta. Wannan ya samo asali ne tun bayan da ya rasa yayarsa da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa da ke kwance ba ta da lafiya sakamakon iyayen matarsa. Hakan ne ya haifar da zazzafar gaba da kuma lalacewar zumuncin ahalin nasu baki ɗaya.
Unintended Vows
In the shadow of her parents’ tumultuous divorce, Hibbatullah, a young woman scarred by the emotional wreckage, finds solace in her independence and fear of commitment.
Her world turns upside down when her well-intentioned father, desperate to see her settled, arranges a meeting with a potential suitor, against Hibba’s vehement protests.
Reluctantly, she agrees to the meeting, only for an unexpected twist of fate to bind her in matrimony with Abdallah Modibbo, a man living on the opposite side of the world. Hailing from different cultural backgrounds, Hibba and Abdallah seemingly have nothing in common.
Unintended Vows is a collision of traditions, values, and lifestyles.
As they navigate the challenges of their accidental union, Hibba and Abdallah discover the beauty in their differences.
Their journey becomes a tapestry woven with threads of compromise, understanding, and a shared determination to overcome the odds. Amidst the clash of cultures, a unique harmony emerges, creating a love that transcends geographical boundaries and defies preconceived notions.
Auren Sadaka
Rayuwar wani naƙasasshen gyartai wanda hannunsa da ƙafarsa ɗaya suka shanye ta shiga cikin wani irin sabon salo na uƙuba sakamakon gashin da yake amsa a wurin matarsa. Sai dai ita ma ba daɗin take ji ba, domin kuwa kullum cikin ƙunci da zubar da hawaye take. Ko me ya jawo yin irin wannan auren wanda babu mai jin daɗinsa?
Gidan Gado
Kakan su Habiba ya mutu ya bar wa mahaifiyarsu wani makeken gida, sai dai ɗan uwansa Malam Umaru ya yi kane-kane akan wannan gida ya ƙi bari a raba a ba wa kowa haƙƙin shi. Duk wanda ya taso da maganar ma sai ya yi mishi barazanar ganin bayan shi. Magada dai sun sha alwashin ƙwato haƙƙinsu, shi kuma Malam Umar da matarsa Saude sun sha alwashin tauye wannan haƙƙi ta kowane hali.
Hakabiyya
Yayin da fafutukar nemawa mijinta magani ya kai Zawwa zuwa ga tone kabarin wata budurwa mai ciki, hakan ya zamo matakin farko na cukurkuɗewar rayuwar Haƙabiyya tun kafin ta fito duniya. Hameedu, wanda ya canza sunan shi zuwa Huzaif yana ɗauke shi ma da wani ɓoyayyen sirri wanda ka iya fayyace komai ko ruguza komsi. Makirci ya haɗu da makirci, tsafi ya haɗu da mugunta, sirri ya ci karo da sirri, shin ko gaskiya ita kuma za ta yi halinta daga ƙarshe?
Siradin Rayuwa
Karatu ne ya zama sanadin haɗuwar Al’Ameen Bello Maƙarfi da Ihsan a America. Bayan sun sheƙe ayarsu na wani lokaci sai suka yi aure ba tare da sanin iyayensu ba. Yanzu shekaru kusan goma kenan, rashin nutsuwa ya sa dole sun dawo gida Nijeriya. Babbar matsalar da ke gabansu ita ce, ba su san da wani ido za su kalli iyayensu ba.
Fitsarin Fako
A daren tarewar auren Lantana ne ‘yan ta’adda suka je ƙauyen da aka kai ta suka watsa jama’a tare da yi mata fyaɗe kuma suka kashe mijinta. Yayanta Kamalu, shi ma sun yanke masa hannu ɗaya a wani hari da suka kawo daga baya a ƙauyen Namu-Ya-Samu bayan sun kashe mahaifin Lantana. Sai dai kuma mutuwar Lantana ta bar baya da ƙura, musamman da wasu hujjoji suka fara nuna wa Kamala ɗan yatsa.
Canjin Bazata
Halin rashi ya yawaita, gashi bikin Yayar Shuhaina ya matso, sai dai babu kuɗin da za a yi musu kayan ɗaki. ‘Yar gonar gadon tasu da aka saka a kasuwa kuma ba a yi mata tayin daraja ba. Ga mutanen gida sai yada wa mahaifiyar su Shuhaina zance suke yi, domin su a wurinsu, duk macen da ba a yi wa gara da kayan ɗaki na kece raini ba, to ba ta cika ‘ya ba.
Hoton Mijina
Muka amsawa da amin muna sakar wa juna murmushi. Tun daga ranar duk wasu makaman yaƙina na zubar da su, har mamakin kaina nake yi da tambayar kaina anya kuwa ni ce Rashida? Zaman lafiya ya samu matsuguni a tsakaninmu tamkar ba kishiyoyi ba.
Duniyar El-Dorado
Bayan shuɗewar lokaci mai tsawo da rabuwarsu, Khadija Muhammad Lamiɗo, wadda aka fi sani da Deejah, ta kawo wa Abou Adem ziyarar bazata a gidan yarin Kirikiri Maximum Security Prison da ke Apapa, Lagos State, Nigeria. Wa ya faɗa mata an kama shi? Me ya kawo ta? Waɗannan na daga cikin tambayoyin da yake buƙatar sani a hanzarce.
Kishin Miji
Zuby na da tsananin kishi kamar ta kashe kanta, hakan ya sa hankalinta ya dugunzuma tun bayan da ta ji cewa an kai kai kuɗin auren mijinta Abdul wani gida. Duk lallashi da ban-bakin da ƙawarta Ummi ta yi hakan bai sa ta saduda ba. Domin kuwa ta sha alwashin sai ta sabauta duk wacce ta ce za ta aure mata miji, don haka a shirye take da ta aikata komai domin cimma buƙatarta
Abdulkadir
Kowa ya sha mamakin yadda aka yi har soyayya ta ƙullu a tsakanin Abdulƙadir da Waheedah saboda bambancin da ke tsakanin halayensu tamkar na ruwa da wuta ne. Yayin da wasu kuma ke tunanin halin da za ta shiga a zamantakewar aurenta da shi. Sai dai sun ba mara ɗa kunya sosai na tsawon wani lokaci kafin babbar ƙawar Waheedah da ake kira Nuriyya ta kutso kanta jikin Abdulƙadir tare da ƙoƙarin ganin ta aure shi.
Sakacin Waye?
Ummatin Mambila ta yi matuƙar ƙoƙarin gaske wajen ganin ta raini ‘ya’yanta maza uku a bisa nagarta da kamala. Ta kuma ci nasarar yin hakan har zuwa lokacin da manyan guda biyu suka yi aure. Sai dai rayuwa ta zo mata da bazata, inda mutuwa ta ɗauke matayen ‘ya’yan nata ta bar abin da suka haifa mace da namiji. Bayan zama na tsawon lokaci ba tare da aure ba, Giɗaɗo ya Auro Jaru, abinda bai sani ba shi ne, ita kuma a zuciyarta babu wanda take so sama da ƙaninsa Muhamman.
Jawaheer
Mujaheed Muhammad, wanda aka fi sani da M.D ƙawararren jami’in C.I.D ne da ake ji da shi a duk faɗin Nijeriya. An turo shi garin Kaduna ne domin ya gudanar da gagarumin bincike akan Alhaji Saleh Mu’azu Mainasara. Ƙaddara sai ta haɗa su da Jawaheer, wadda ‘ya ce a wurin Alhaji Saleh Mu’azu Mainasara, wadda ta faɗa kogin son shi kamar ta yi hauka. Shi kuwa ya yi alƙawarin babu wata mace da zai iya rayuwa da ita bayan tsohuwar matarsa. Babban abinda ke ƙara dagula mishi lissafi shi ne, irin yadda Jawaheer ke yin abubuwa irin na tsohuwar matar tasa, wato Nayla.
Baba Dattijo Dan Bursin
Yayin da wani ɗan jarida ya je gidan yarin Kurmawa da ke Kano ya gamu da wani dattijo mai ban mamaki da ke rayuwa a wannan gida na kaso. Shin ko ta yaya za a iya shari’ar kashe mutumin da ya riga da ya mutu tun shekaru 29 da suka gabata?
Izina
Aisha (Ma’isha) da Abdul’aziz ‘yan’uwan juna ne, kuma dukkansu lauyoyi ne. Sai dai a karo farko za su kara da juna a gaban ƙuliya domin kare mutane biyu. Iya Aisha tana ƙoƙarin ƙwato wa wata mata da ‘yarta
‘yancinsu ne a hannun wani mugun mai kuɗi. Shi kuma Abdul’aziz yana kare shi. A wani ɓangaren kuma, yayansu jami’in ƙasa da ƙasa, Deputy Commissioner of Police Abdulmalik Ibrahim Ahmad ya zo Nijeriya domin ya gudanar da bincike na musamman akan kisan da aka yi wa wani babban jami’in tsaro, kwatsam kuma sai ƙaddara ta haɗa shi da ‘Yar Jarida Intasar Mahmood Abdullahi.
Ta Ki Aure
Sawwama da Kawwama yaya da ƙanwa ne da suka jima basu yi aure ba. Shekarar Sawwama talatin da biyar ba ta yi aure ba, yayinda ita kuma Kawwama shekararta talatin da biyu ba ta yi aure ba. Hakan ya sa kowa a dangi ke ta faman yi musu surutu. Kwatsam sai ga Jalil ya zo neman auren Kawwama, an sha biki an gwangwaje, sai dai kuma Jalil na ɗauke da wani ɓoyayyen lamari da ba kowa ya san da shi ba.
Kwamin Nadama
Baƙin kishi ya sa Ladiyo cakumar wuyar mijinta tana mai sauke masa kayan rashin mutunci tare da tabbatar mishi da cewa bai isa ya yo mata kishiya ba. Shi kuwa Kabiru, don ya gwada mata lallai ya haifu bai yi wata-wata ba ya danna mata saki biyu. Tun daga nan ta shiga tashin hankali da ruɗani, musamman da ta tuna cewa za ta bar gidan kuma zai kawo wata.
Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi
Al’amura sun dagulewa Zainab tun bayan da bakinta ya jawo mata jalli-joga sakamakon sharrin maita da ta yi wa Jummai a gidan suna. Lamarin ya kai matuƙa a fagen tsamari ne ya yin da aka aiko mata da takardar sammaci daga kotu a bisa wannan zargi, ana tsaka da wannan kuma sai mijinta Auwal ya sake ta.
Na Kamu Da Kaunar Matacce
Rayuwar Munaya ta birkice tare da wuntsulawa wata duniyar sabuwa tun daga lokacin da ta ga hoton tsohon mijin Zuwaira, wato Zayyad Muhammad Hashim. Tafiyar da ta yi zuwa garin Kaduna da nufin shiga makarantar KASU domin ta ɗora karatun gaba da Sakandare sai ga shi yana neman komawa karatun binciken rayuwar matacce.
Shattered
A hidden secret was all it took…Can they ever trust again? For Haleema, it was love at first sight and Faruq was the man she chose. They were madly in love and the only thing they were waiting for was to be married.
But when the time came, at the very last minute, they were said to be long-lost siblings. Haleema and Faruq were quickly shoved into a world of lies, chaos, secrets, and destiny. Will they ignore everything and marry or will they embrace separation? Would they ever trust again?
Sharri Kare Ne
Masu azanci suna yawan ambaton jimlar alhaki kwuikwuyo ne, mai shi yake bi, sai dai a doron kasa akwai wasu nau’in jama’ar da ba su gama amincewa da wannan azancin ba, sun yarda cewa alhari kwuikwuyo ne, amma ba su yarda cewa wata rana ya kan dawowa wanda ya aika shi har ya yi masa mummunar rauni. Fauziya da Aisha suna daya daga cikin irin wadannan nau’in halittun da suka canza ma’anar wancan azancin, wanda shi ya saka suke sheke ayarsu ta hanyar yin gurbataccen rubutu kuma su aita shi wa dimbin al’umma cikin farin ciki da ribar da suke samu, ba tare da tunanin wata rana kaikayi zai koma kan mashekiya ba.
Sirrina
A yunƙurin ganin sun samu ƙarfin iko fiye da na saura, masarautun Manaaj, Nahar da kuma Hizaar sun fara yi wa juna zagon ƙasa tare da kai wa juna farmaki ta bayan fage. Karan, Sanam da Sahash duk ƙoƙarin samun ƙarfin iko suke yi. Sai dai tun Sarki Zahir na raye ya riga ya bayyana Aliya a matsayin wacce za ta gaje shi. A wannan rikici na masarautu, babu abin da kowane ɓangare ba za su iya yi ba domin su samu ƙarfin iko akan sauran.
Ƙuda Ba Ka Haram
Allah ya ba wa Usman mata tagari mutuniyar kirki, sai dai ita Sakina ba ta yi sa’ar miji ba. Domin kuwa ba ya ga kasancewar Usman Ɗansanda mai karɓar rashawa, yana caca tare da kurɓar barasa. Babban mugun abu kuma yana da biye-biyen mata, wato dai irin mazan nan ne da ake kira da ƙuda, babu ruwansu da haram. Sai dai ya ɗebo wa kansa ruwan dafa kansa, domin kuwa ya ƙwallafa rai akan ƙanwar matarsa wato Humaira.
Sarauniyar Kyau
Afeefarh Kyakkyawar mace ce zubin farko. Duk wata siffa da diri da ake nema a wurin ‘ya mace Allah ya ba ta, British Queen ko Glam Gueen na daga cikin takenta.
Bayan sun shirya zuwa bikin Birthday ɗin Zahra ita da su Haleesarth sai ta ziyarci ɗakin Zainab inda ta same ta ta yi shaye-shaye ta bugu, ɗakin kaca-kaca. Ba komai bane ya jawo haka ba face kasantuwar wannan rana ta dace da ranar masoya ta duniya, wanda hakan ke da manufa ta musamman a wajenta.
Mijin Novel
Bayan fafutuka da kai ruwa rana, Hindatu ta samu irin mijin da take so, wato mijin Novel. Kyakkyawa, mai ilimi, kuɗi da sauransu. Sai dai abinda ba ta sani ba shi ne, shin ko ta shirya yin sadaukarwar da ta dace domin yin rayuwar aure da Hamza?
Rikon Sakaina
Ammi na so ta karɓi shawarar juma na tura Zubaida bara, sai dai tana tunanin yadda za su ƙare da Maqsood domin kuwa ya sha nuna mata rashin amincewarsa game da hakan. Ita kuwa Zubaida sai murnar lashe jarabawar da suka yi take yi ba tare da ta san abinda ake kitsawa ba.
Jini Ya Tsaga
Hafsat bazawara ce da ke zaman zawarci a gidansu. Mahaifiyarta ta rabu da mahaifinsu mai suna Kamaluddeen, amma sauran matan nasa guda uku suna zaman lafiya sosai da junansu. Hafsat ta sha alwashin kai mahaifinta ƙara ofishin ‘Yansanda bisa zargin nuna rashin adalci a tsakanin matansa. Shin ko za ta ci nasara?
Su Ne Sila
Tsananin raɗaɗi da zogin da ciwukan jikin Zainab ke yi mata ba su kai rabin wanda zuciyarta ke yi mata ba sakamakon tsintar kanta da ta yi a gidan yari. Duk irin tsusayinta da Safiya ke ji bai sa ta saki jiki da ita ba. Daga ƙarshe ma dai yanke shawarar kashe kanta ta yi. Domin a tunaninta hakan kaɗai mafita a gareta.
Da Magana
Azeez shi ne ɗa ɗaya tilo a wajen mahaifiyarsa Hajiya Maryam. Babu abin da ya nema bai samu ba saboda suna da kuɗin. Babbar matsalarsa ita ce sata, ko ɓera ya sallama masa in dai wurin sata ne. Irin yadda yake iya yin sata ba tare da an ankare ba har mamaki yake ba wa mutane, wasu ma na zargin ko yana da aljanu ne masu nuna masa inda kuɗi ko kayan kuɗi suke.
Jahilci Ko Al'ada
An daɗe ana bidiri a wani gida mai mata biyu, wato Indo da Lami. Indo tana da ‘Ya’ya mata guda biyu, Mairo da kuma Hassu. Sai dai ba ta ba wa Mairon kula irin yadda ya kamata saboda ita ce ta ɗiyarta ta farko. Ganin haka ne ya sa ita ma Lami ko a jikinta. Baba Mairo ce kaɗai mai ji da yarinyar, kuma ba ta shakkar ta zazzage kowa akan duk abinda ya taɓa jikanyar tata.
Hawayen Jini
Hamdan da babban amininsa Mahfuz na ta shiri don ganin sun isa wurin taron walimar auren Hamdan ɗin da ake shirin yi a washegarin ranar. Ba zato ba tsammani kawai sai mahaifiyarsa Hajiya Mairo ta ce ba zai auri masoyiyarsa Raslima ba. Ko da Hamdan ya nemi jin dalilin da ya sa ta yanke irin wannan tsattsauran hukunci haka, bai samu komai ba face mari, zagi da hamɓara.
Mu'azzam
Irin biyayya da kuma soyayya da Mu’azzam ke yiwa mahaifiyarsa, Goggo, ya sa duniya ke kallon shi a matsayin da nagartacce. To amma a badini kuma yana da wata rayuwa da ko makiyinsa ne ba zai yi farin ciki da ganin sha a ciki ba. Wannan ya hada da rashin adalcin da yake tafkawa a tsanin matansa uku. A hakan kuma Goggo ta umurce shi da kara auren Husna, wacce ta ke kamar kanwa a gare shi, adalilin wani mummunar kaddara da ta fada ciki. Shin ko rikicikin da ke cikin gidan Mu’azzam zai barshi ya zauna lafiya?
Wata Kaddara
Mubarak Yusuf Maikuɗi matashin mai kuɗi ne da ya taso da taka-tsan-tsan da kuma jajircewa akan tarbiyya. Babban abin da ya fi tsana a rayuwarshi ita ce sata. Sai dai kash… Ƙaddara ta sa ya auro ‘yar wani ƙasurgumin ɓarawo ba tare da ya sani ba.