Skip to content
Part 2 of 11 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

SHAAMEEKH or SHAMIKH : is an Arabic name that is use interm of naming a muslim baby boy, the name Shamikh is drive from the holy Qur’an chapter 77 verse 27, Shameekh mean’s HIGH, LOFTY and ABOVE ALL OTHER’S.

Yauwa waɗanda ke da matsala akan basu iya faɗan sunan ba, idan suka karanta ayar za su fahimci yanayin yacce ake ƙiran sunan, a cikin suratul MURSALAT aya ta ashirin da bakwai.

 

ADAMAWA STATE.

FEDERAL MEDICAL CENTER YOLA.

Wata farar mata ce ta fito a ɗaya daga cikin ɗaƙunan malaman asibiti da ke jere a floor ɗaya, office ne wanda yake a jerin na manyan likitoci masu duba mastalan da ya shafi mata, dattijuwar matar da kana ganinta kasan ta manyanta, sanye take da leshi baƙi ɗinkin dogon riga wanda ya yi mugun amsarta, hijab nata fari tass ɗan dai-dai, idanuwanta ta maƙala musu glasses fari, amma kana gani kasan medicated glass ne ba na gayu ba, hanunta riƙe da labcoat, tafiya take cikin nistuwa fiskanta yalwace yake da murmushi, jama’a sai ɗaga mata gaisuwa suke tana amsawa tun fitowanta office nata har ta iso inda drivernta ke jiranta, tana isowa wajan motan sai drivern yayi sauri zai buɗe mata ƙofa, amma sai ta dakatar da shi, fiskanta da fara’a ta buƙaci ya bari za ta buɗe da kanta, drivern ba dan ya so ba ya masta ta buɗe ta shiga tare da karanto addu’an hawa ƙarfe, ajiye abubuwan hannunta tayi a gefenta tare da gyara zamanta tana hamdala ga Allah.

Driver ne ya ce, “Sannu da aiki Hajiya.”

Tana murmushi ta amsa masa, tare da tambayansa nasa aikin, shi ma ya amsa mata, counter(carbin irge) da ke maƙale a yastunta ta gyara tare da cigaba da yin tasbihin da take yi, ƙira ne ya shigo wayanta dake cikin jaka, Jawo jakan ta yi ta buɗe ta ciro wayan, sautin qira’a na Amanar-rasulu yana tashi, amma kamun ta gama ciro wayan har ƙiran ya yanke, tana cirowa ta duba ta ga layin Alhaji ne, murmushi kawai ta kuma yi tare da bin ƙiran, yana shiga ringing ɗaya kawai yayi aka ɗauka, ita ta fara yin sallama cikin nistuwa da girmamawa ga wanda ta ƙira ɗin.

“Assalamu Alaikum Baba an wuni lafiya?”

“Lafiya ƙalau Alhamdulillahi Fatima, ya kike? ya aiki?” Faɗin muryan wani stoho a ɗaya ɓangaren.

Matar ta ce, “Lafiya Alhamdulillahi Baba, yanzu haka ma tasowana daga asibitin kenan ko gida ban ƙarisa ba.”

Gaisawa suka yi ta tambayi tsohon ƙarfin jikinsa, ya amsa mata da sauƙi sannan ya ce, “Fatima wai ina labarin abokinane kam?”

Matar murmushi ta yi ta ce, “Yana can lafiya baba, munyi waya ɗazu ma ya ce yana gaisheku kuma in Allah ya yarda yana shigowa.”

“To! To! Madallah, Allah kawo sa lafiya, Allah muku albarka duka ku da zuria’anku.”

Da “Ameen” matar ta amsa, sannan stohon ya faɗa mata ga Hajiya ya miƙa mata wayan suka gaisa, Hajiyan ta ce, “Faɗimatu wai yaushe za ki shigo ne?”

Matar na murmushin jin tambayan mahaifiyarta ta ce, “Mama wai daman ina jiran mai-gidanki ne, idan ya zo sai mu taho tare.”

Hajiya a ɗaya ɓangaren ta ce, “Me haɗin Dubai da Adamawa?”

“Babu mama” faɗin matar tana murmushi dan tasan za’a yi haka daman.

“To idan har kin yi niyan zuwa kawai ki zo, shi kuma idan ya ga dama kar ya zo za mu haɗu ne, ni da shi ɗin” Hajiya ta ƙarishe maganan da ƙwafa.

“To shikkenan Mama, In sha Allah za mu taho ranan asabar tare da kishiyanki.”

“Allah kai mu, Allah miki albarka, Allah kawo ku lafiya dukanku.”

“Ameen Mama.”

Suna gama magana suka yi sallama ta kashe wayanta, daidai lokacin sun iso gidansu dake anguwan Abuja road, buɗe musu gate aka yi suka shige, bayan driver ya yi parking ta fito dan shigewa cikin gidan, sai ga wata kyakkyawar yarinya budurwa, yar kimanin shekara sha takwas ta zo da gudu, tana faɗin, “ayoyoo Ummiy sannu da dawowa”, ta rungume ta.

Ummiy na murmushi ta ce, “sannu babyn Ummiy, ɗauko jaka na da labcoat a mota”, ta faɗa tare da raba yarinyar da jikinta.

Yarinyar ta ce, “To Ummiy na.”

Shigewa cikin gidan Ummiy tayi da sallama, Talatu yar aikin su dake goge palourn ne ta amsa, stugunnawa tayi har ƙasa ta ce, “Sannu da dawowa Hajiya.”

“Yauwa Talatu sannunki kema da aiki”, Ummiy na gama faɗan haka ta wuce ta haura matakalan da zai kai ta sashinta da ke sama, sannan ta nufi ɗakinta.

Shiga ɗakin ta yi da sallama duk da ba kowa a ciki,(Ku zama masu yaɗa sallama ko da kuwa babu mutane a wajan, domin akwai salihan bayi mala’ikun da ke amsawa, kuma suke jira ka yi sallama dan su rubuta maka ladanka), hijab nata ta cire ta wuce banɗaki direct.

Yarinyar da Ummiy ta ƙira da Baby ce ta shigo ɗakin da sallama ita ma, jin shiru ba wan da ya amsa mata sai ta turo ƙofan ta shigo, jin ƙaran sauƙan ruwa a banɗaki, shi ya tabbatar mata da Ummiy na ciki, ajiye mata jakan tayi da labcoat nata a ma’ajiyarsu, sannan ta nemi waje ta kwanta a kujeran dake cikin ɗakin daga gefe, tana jiran Ummiyn nata, bayan mintuna Ummiy ta fito.

Wucewa ta yi wajan dressing mirrow ta shafa mai da turaruka masu qamshin gaske ( lallai anan Shamikh yayi gadon stafta, son ƙsmshi da komai ma).

Bayan ta gama shiryawa dogon riga mara nauyi ta ɗauko ta saka, sannan ta zauna a bakin gadon nata, sai da tayi hamdala na daɗin jikinta da ta ji, sannan ta ce, “Baby ina ga dai bakinki akwai magana.”

Baby taso wa tayi tana murmushi ta ce, “Ummiy nayi missing na big bro ne wallahi.”

Ummiy ta ce, “Ikon Allah! Baby anya magananki akwai gaskiya?”

Turo baki tayi ta ce, “Da gaske fa Ummiynmu, yauwa Ummiy yaushe za mu je Maiduguri ne ni kam?”

“Yauwa kin tuna mini ɗazu mun yi waya da Hajiya Mama na faɗa mata za mu shigo ranan Asabar in Allah ya yarda.”

“Wayyooooo! Allah bar mana ke Ummiy, Allah nayi missing na Maiduguri barin ma aunty Jidderh ta, shiyasa nake son wannan family meeting ɗin, saboda lokaci nayi za ka kalli kowa, gaskiya Allah sambaɗawa stoho albarka, da ya kawo wannan ingantacciyar shawara.”

Murmushi Ummiy tayi tare da amsawa da Ameen, an ce Allah ya yiwa stohonta albarka, sannan ta ce, “Ki tabbatar dai kin shirya kamun ranan idan ba haka ba kuma tafiya zan yi na barki dan ina son mu tafi da sassafe ne.”

Zaro ido baby tayi ta ce, “Ummiy dan Allah mu bi Flight wallahi nikam bazan iya zaman mota ba.”

Kallonta Ummiy tayi, tare da yin murmushi ta ce, “Da man so nake naji me za ki ce baby, ke kam ko tsuntu ya ganki ya barki da son firewa, ke da jirgi kam inaga pilot zan bai wa aurenki.”

Cunna baki tayi ta ce, “Ni dai Ummiy koma me in dai Flight za mu bi shikkenan komai dai-dai ba mastala, kuma maganan big bro ma nafasa sai ya zo”, daman har ta miƙe tsaye sai ta koma ta zauna kusa da Ummiy ta ce, “Ayya Ummiynmu, dan Allah idan big bro ya zo ki faɗa masa ya sauya mini waya, dan Allah dai kin ji Ummiyna.”

Ummi cewa tayi, “Ai daman nasan kwanar zancen, ba zai wuce wani abun kike so ba, ban da dai haka kawai baby ki ce kina kewan Shamikh, amma dai baby duk yaushe ya sanja miki wayan? ki din ga jin tausayin yayanki fa baby, akwai mutuwa, akwai jarabawar ubangiji, yau kana da shi gobe ba ka da shi, bana so ki saba da irin rayuwar nan, domin Allah na jarabtar bawansa a ko da yaushe, idan babu mu wa zai jure miki haka?”

Sunkuyar da kan ta tayi ta ce, “Insha Allah Ummiy zan zama mai yarda da ƙaddara a duk lokacin da hakan ya samemu sannan zan kasance mai haƙuri da akwai ko babu.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “To Allah ya miki albarka, ki shirya da wuri ko, insha Allahu kuma idan ya dawo zan saka shi ya sanya miki, ai ya zama dole a sauyawa autar Ummiy abin da take so, kuma autar Ummiy ma tasan yayanta yana ƙaunarta, mai mata komai ne ko babu Ummiy, muddin yana da halin mata.”

Murmushi mai kyau baby tayi tare da cewa, “Ameen Ummiy, Allah ya ja kwana ya barki da Daddy.”

Murmushi kawai Ummiy tayi, tare da faɗin Ameen ɗin a zuciyanta.

“Ummiy bari na je nayi assignment da wani lecturer ya bamu tun jiya, amma fa Ummiy ki fito ki ci abinci kamun ki kwanta, kin ji Ummiyna” ta faɗa tare da tashuwa ta nufi ƙofa.

Taso wa Ummiy tayi ta bi bayanta, suka fito tare, dinning Ummiy ta wuce, ita Baby kuma tayi ɗaki ta ɗauko system nata, ta ajiye a kujera a palourn ta wuce dinning, samun Ummiy tayi tana shan kunun gyaɗa da ya ji haɗi.

Langwaɓar da kai baby tayi ta ce, “Yanzu Ummiy kunun kawai za ki sha fa na sani, ba za ki ƙara komai ba, bayan kinsan big bro baya son hakan Ummiy.”

Ummiy ta ce, “Sarkin surutu Ummiy bata jin yunwa, sai zuwa anjima.”

Ɗiban kunun tayi ita ma ta ce, “to Ummiy Allah ya kai mu anjiman, kamun na gama assignment ɗin sai mu miki favorite food naki.”

“To a gama lafiya, daman dai shi nake sha’awan ci.”

Baby cikin Palourn ta wuce riƙe da kofin kununta, system nata ta jawo ta buɗe tana assignment tana kurɓan kunun.

Ummiy dake dinning ɗin ƙira ne ya shigo wayanta, ɗauka tayi tana amsa sallaman da aka mata a ɗaya ɓangaren tana faɗin, “Mamana kuna lafiya?”

Shiru tayi da alama magana ake a ɗayan bangaren, can kuma ta kuma cewa, “Duk muna lafiya muma mamana, ga ƙanwarki lafiyarta lau ko ɗazu sai da tayi magananki.”

Murmusawa wa ummeyh tayi ta kuma faɗin, “Allah ya miki albarka Mamana, Insha Allahu muma muna zuwa ba jimawa.”

Juyawan da Ummiy za ta yi ba sai ta ga baby a gefenta ba tana faɗin, “Please Ummiy ki bani mu gaisa nasan Aunty Jidderh ce.”

“Mai anguwan garinku baby, ba dai kina da wayarki ba, to ƙira ta da naki ba zan ba da nawa ba.”

Jidderh ce ta yi murmushi ta ɗaya ɓangaren ta ce, “Ayi haƙuri Ummiynmu a bata naji muryan ƙanwata.”

Ummiy miƙawa Baby wayan ta yi ta ce, “Karɓa ba dan halinki ba, kin ci albarkacin Mamana.”

Baby amsa ta yi tana murmushi ta shagwaɓe murya kaman tana gaban Jidderh ɗin ta ce, “Yaya Jidderh ni fushi nake dake kwana biyu ba ki ƙirana shi kuma yaya inaji ya manta da ni ma kwana biyu shi ma bai mini recharging ba balle na ƙira ki.”

Jidderh ta ce, “Amana afuwa Babynmu.’

Ƙara tura bakin ta yi ta ce, “Ni dai naƙi yaya Jidderh.”

“Haba dai in-law ta kuma ƙanwata.”

Murmushi ne ya kuɓuce wa baby har da gyaɗa kai irin ta ji daɗin sunan, ta ce, “Insha Allah kuwa yaya Jeeddeerh ta, daga ke ba wata bayan ke ba ƙarii Allah bar mana ku.”

Jidderh ta ce, “Ameen ƙanwar kirki, yaushe za ku shigo?”

“Ranar Saturday yaya Jeeddeerh, kuma ni awajanki zan sauƙa, bro Yusuf yana nan ai?”

“Eh baby yana nan, Allah ya kawo mana ku lafiya.”

“Ameen yaya jeeddeerh”, Baby ta faɗa tana murmushi.

Wayansu suka yi tana faɗin a gaida mata kowa da kowa, sannan suka yi sallama ta kashe wayan.

Ummiy da already taga call nasu bame ƙarewa bane wucewa tayi sama dan ta huta kamun lokacin sallah yayi.

Baby da ta juya taga ba Ummiy a dinning kuma bata palourn, ajiye wayan tayi a gefenta bata je kai mata ba dan ta san hutawa Ummiy taje yi, assignment nata ta ci gaba da yi.

*****

Jeedderh ce a ɗakin da yake mallakinta, komai na ɗakin blue colour ne sai white, kwance take akan haɗaɗɗen gadonta, tana riƙe da wayanta ta zuba masa idanuwanta gaba ɗaya, da alama wani abu mai muhimmanci take yi duba da yacce hankalinta duka ke kan wayan.

Wani sihirtaccen murmushin da jeedderh ke saki, wanda ya ƙara mata kyau, shi ya sanya ni leƙa wayan dan ganin abin da ke sanya ta, irin wannan sansanyar murmushin.

Message Jidderh ke rubutawa, wanda na tabbata santin message ɗin ke sanya ta wannan haɗaɗɗen murmushin.

Tana gamawa ta tura wa mallakin saƙon ba ɓata lokaci, turawanta kuma yayi daidai da shigowan ƙira a wayan nata, “SAFWAN” shi ne sunan da ya bayyana ɓaro-ɓaro, akan layin da ya ƙirata, Jidderh tura baki tayi kaman ba za ta amsa ƙiran ba, tana ji yana ringing amma sai da ta tabbatar ya kusa stinkewa, sannan ta ɗauka a hankali cikin nistuwa ta kai wayan kunnenta, muryanshi ta jiyo yana faɗin, “Hello Baby ya kike?”

Cunna baki tayi kaman yana gabanta ta ce, “Uhmn lafiya.”

“Ma sha Allah Babyna ya labari?”

 Jidderh da ke jin kaman ta shaƙesa, a hankali ta ce, “Please Safwan zan yi sallah, idan na idar zan ƙiraka.”

“Okay Baby am waiting a saka mu a addu’a, Allah kuma ya mallaka mini ke.”

Sai da Jidderh ta harari wayan, dan jin ya ce wani Allah Sa ya mallaketa, sannan ta ce, “Okay byee”, tana faɗan haka a taƙaice ta kashe wayanta.

Sai da ta datse ƙiran sannan ta tura baki tana ƙun-ƙuni, can kuma ta tuno da maganan da suka yi da baby na katin waya, dafe kai tayi a hankali cikin sanyin muryanta ta ce, “Bari nayi sallah tukunna, zan tura miki babynmu ƙanwar miji”, ta ƙarishe faɗa tana murmushi ita kaɗai.

Sai da ta yi dialling wani number da ta rubuta “ZAWJ”, amma har sau uku tana ƙira ba’a ɗauka ba, haushi taji ta jefa wayan kan gado, tana tura baki har da bubbuga ƙafa ta yi hanyan toilet.

Jidderh alwala ta ɗauro ta zo ta saka hijab tayi sallah, ta jima tana addu’ointa sannan ta shafa, tare da mayar da darduman da hijab ɗin mazauninsu.

Banɗakin ta koma tayi wanka ta fito ɗaure da towel mai madedecin girma, fari tasss da shi, sai da ta shafa wani ruwan turare mai haɗi, ta zauna a haka jikinta ya bushe, sannan ta zo ta bi da man ta mai ƙamshi da Humra da kuma turaruka, iya abin da tayi kenan bata tsaya wani kwalliya ba, domin Jidderh ba ma’abociyar ɗige-ɗige ba ce.

A iya shafe-shafen turaren da Jidderh tayi kawai, kar ku ga haɗuwan da tayi na kyau da baiwan da Allah ya mata, don jidderh kyakkyawa ce ta gaske, ita ba fara ce sol ba har can, sannan kuma ba za’a ce mata baƙa ba, ba ta da jiki sannan ba siririya ce sosai ba, tana da dirinta dai-dai wan da ya tafi da yanayin aukin jikinta, ƙirjinta madaidaita Masha Allah, ƙugunta ma duka Masha Allah son kowa ƙin wanda ya rasa, tana da dogon gashi har bayanta baƙi wuluk gwanin sha’awa, dogon hanci Masha Allah, ga bakinta ɗan dai-dai kaman ramin asusu, idanuwanta manya-manya waɗanda ake kira da golden eye’s, a taƙaice dai jidderh kyakkyawa ce ta ƙarshe ma, duk iya yacce ake buƙatan mace to ta kai wajan, dan Allah ya wadata da komi Alhamdulillahi Masha Allah.

Shiryawa tayi cikin pink sleeping dress mai kauri sosai, amma kayan akwai laushi da santsi, gashi har ƙasa wandon ya kai mata, rigan kuma iya guiwa amma a buɗe gaban rigan yake sai igiya kawai, kayan sosai ya amshi Jidderh kaman ka sace ta ka gudu da ita.

Wani ƙaton zumbulelen hijab ta saka black color, wayanta ta ɗauka da duk abin da za ta buƙata, sannan ta fice a ɗakin nata ta ja ƙofa ta rufe.

Ɗakin mummy ta shiga ta sameta tana ninke hijabi ta idar da sallah kenan, tana kallonta ta murmusa tare da cewa, “Uwar masu gida sai ina haka da wannan hijabi kaman matar limami?”

Murmushi Jidderh tayi ta ce, “Mummy za ni wajan takwarata na gaishe su da stoho, wataƙila ma na kwana a can.”

“Tom ki kula sosai-sosai, Allah ya tsare ki gaishe da baba Alhaji.”

Sai da jidderh ta juya tana ƙoƙarin ficewa ta ce, “Insha Allah mummy za su ji, yau zan je na ƙwace mijina.”

Mummy murmushi tayi tare da ɗaga murya yacce jidderh za ta ji, ta ce, “Za ku yi ku bari duk ku gama alhaji baba na hajiya mama ita kaɗai ce.”

Jidderh Ficewa tayi a gidan nasu tana tare da jan ƙofan palourn ta rufe, hanyan ficewa a gate na gidan nasu ta nufa, kusan cin karo suka yi da wani matashin saurayi kyakkyawa da shi, murmushi ya saki yana kallonta ya ce, “Ke kuwa tsohuwa lafiya haka da ƙaton hijabi kaman mai zuwa ɗaukan darasi, gashi sai sauri kike kaman mai shirin tafiya sama, sai ina haka?”

Cunno baki jidderh tayi ta ce, “Allah yaya Faisal ba na so nikam, ni ba tsohuwa ba.”

Murmushi saurayin da ta ƙira da yaya Faisal ya yi ya ce, “To naji Hajiya jidderh an daina, sai ina da daren nan?”

“Yaya faisal gidan takwara zan je.”

“Au ki ce soyayyan tsoho ta motsa za ki je ganinsa.”

“Ai kuwa kam kai da ka sani, idan ban ga wannan tsohon ba ai babu bacci hankali kwance, balle kuma cikin nishaɗi.”

Murmushi Ya Faisal ya yi tare da girgiza kai ya ce, “Faɗi ɗayan gaskiyan kada ki yaudari tsoho, dan munsan ba shi kike nufi ba, wancan na Dubai ɗin kike nufi.”

Jidderh murmushi tayi kawai tare da kulle fiskanta wai taji kunya.

Ya Faisal ya ce, “Gashi na zo gaishe da mummy ne da na raka ki.”

“Lahh! Ya Faisal kar ka wani damu zan je ni kaɗai, kuma may be zan tafi da motana idan ƙuya bai hanani ba.”

“Okay sis Allah ya tsare hanya ki gaishe da su ni kam ba su ganina sai ɗan Dubai ya shigo.”

Murmushi Jidderh ta yi kawai dan tasan tsokana irin na ya Faisal, ta ce, “Byee Yaya Faisal.”

Wucewa jidderh tayi, tana isa bakin ƙofan, sai mai gadi ya taso zai ya buɗe mata ƙofa, ita kuwa tana murmushi ta ce, “lah! a’a baba wallahi ka bari zan buɗe da kai na, ka huta abinka.”

Baba mai gadi yana murmushi ya ce, “Hajiya Uwar masu gida ina za ki je da daren nan haka kinsan Alhaji ya hana fitanku, muddin aka yi Magriba.”

“Gidan takwara zan je Baba, zan kwana a can ma.”

“To amma ai ke ɗaya bai yi ba kuma ga shi da ƙafa, ai ya kamata ki ɗau mota uwar masu gida, tunda dai kin iya”, Baba mai gadi ya faɗa yana murmushi, dan duk cikin jikokin wannan family a mata dai babu ya Uwar masu gida(sunan da ake ƙiranta da shi kenan), jidderh tana da hali mai kyau, ga kirki ga haƙuri, ga girmama manya, da sanin ya kamata, ba ruwanta da rena mutum dan yana aiki a gidansu, ba za ka taɓa jin ga jidderh tayi faɗa da wani ba tun tasowanta, shiyasa manya da yara ba wan da baya son ta a familyn, dan ta fita Zakka, kirkinta na daban ne(Wannan kuma hali ne na masu suna Hauwa’u kulu mai jidda).

Jidderh ta ce, “Ba komai Baba, in sha Allah zan je lafiya”, suna cikin magana sai ga Faisal har ya fito daga wajan mummy, yana murmushi ya ƙariso wajansu tare da cewa, “tsohuwa har yanzu baki tafi ba?”

“Eh Ya Faisal, inji Baba Mai Gadi ne sai na ɗau mota ni kuma ƙuyan driving nake ji, daga nan zuwa gidan takwara kam.”

“Ai da gaskiyan Baba, uwar masu gida ba abar wasa ba, amma tun da har na fito sai muje na ajiyeki ba.”

“To Yaya Faisal.”

Baba mai gadi murmushi yayi tare da faɗin, “Alhaji Faisal ai zuwanka ya fi zuwan gomna, dan gwanda a kai ta, da daren nan gari ya kusa fara duhu tafiyanta ita ɗaya kuma a ƙafa bai yi ba, Allah ya kai ku lafiya, a gaishe da su Baba Alhaji.”

Amsawa Ya Faisal yayi yana murmushi, suka shiga motan nasa da jidderh, Baba mai gadi ya buɗe musu wangamemen gate ɗin suka fice, suna fita Ya Faisal na driving ba tare da ya kalli jidderh ba ya ce, “A gaskiya Baba mai gadi ɗan amana ne sis, kalli fa ai irin wannan kulawan ko ƴar cikin ka iya haka za ka kula da ita, Allah dai ya kare masa zuri’ansa shi ma.”

“Ameen Ya faisal, Baba mai gadi kam ai ɗan aljanna ne, da amana da gaskiys yake aikinsa, amma meyasa naga ka fito da wuri?”

“Daddy bayanan Mummy ce kawai kuma mun gaisa”, faɗin Faisal da ke driving nasa.

Suna zuwa ƙofan gate na gidan Baba alhaji ya tsaya ya ce, “Ni ba shiga zan yi ba sis, ki sauƙa anan zan juya gida lokacin zuwa masallaci ma yayi.”

Murmushi jidderh tayi ta ce, “Nikam ai nagode hakan ma ya Faisal, Allah ba da ladan rage mini hanya”, ta faɗa tare da ficewa a motan, suka yi sallama ta wuce ƙofan gidan, Faisal yana tsaye ta ƙwan-ƙwasa ƙofa, mai gadin ya tambayi waye? Ta faɗa kamun ya buɗe ta shiga bayan ta ɗagawa ya Faisal hannu, murmushi shi kuma ya sakar mata sai sannan yaja motansa yayi gidansu shi ma.

Mai gadin ne ya gaidata da fara’a, dan kowa yasan kirkin jidderh ta kyawun halinta, yana murmushi ya ce, “Uwar masu gida sannu da shigowa.”

Murmushi jidderh tayi ta ce, “Yauwa Baba nagode, sannu da aiki”, ta faɗa ta wuce cikin gidan har ranta tana jin daɗin wannan suna, da suke ƙiranta da shi manya da yara, musamman ma’aikatan familyn nasa, jidderh Uwar masu gida.

Ƙatoton gida ne wanda faɗan yadda yake ma ɓata baki ne, domin har kaman ya fi gidansu jidderh girma, da sallama ta shiga cikin gidan, bata bi hanyan da zai sada ta da babban palourn ba, ta ɓj hanyan da zai kai ta palourn takwarar tata, ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Amsa mata dattijuwar yar aikin da ke jera abinci a dinning tayi, tana sakin fara’a ta ce, “Maraba lale da uwar masu gida.” murmushi jidderhnma tayi ta ce, “Barka Baabaa larai.”

Wucewa tayi ɗakin Hajiya mama direct, ta sameta tana kan sallah, cire hijab ɗin jikinta tayi ta faɗa kan gadon kamn yarinya ƙarama, wayanta ta bude ta shiga ta turawa Baby recharge card na 5k, sannan ta tashi ta ɗauro alwala ta mayar da hijabinta ta tada sallah.

Baabaa larai ce tayi sallama a ƙofan ɗakin, gyaran murya Hajiya mama tayi alamun tana lazumi, jin haka sai Baabaa larai ta juya.

Jidderh bayan ta idar da Sallan ta ja carbi, ita ma tayi nata addu’an ta shafa, sannan ta cire hijabin ta ɗaure igiyan gaban riganta ta rufe.

Komawa kan gadon ta yi ta kwanta, tare da ƙara yin dialing numbern ɗazu, yanzun ma dai kaman ɗazu ne har ƙira uku ta yi amma ba a ɗauka ba, ƙaramin tsaki ta ja tare da dialing numbern Safwan, yana shiga aka kashe aka ƙirata.

“Wahalalle”, haka ta faɗa kamun ta ɗau ƙiran, ba laifi yanzu dai ta sauraresa, sun yi hira amma sama-sama take amsa masa, shi kam Safwan da alama ko a jikinsa.

“Babe yaushe za ki bar ni na zo na ganki? seriously am eager to see you, and ina so na turo magabatana ayi maganan auran mu, i can’t wait to see dis beautiful diamond lady a gidana a matsayin halal wife tawa, kullum ki ce ba yanzu ba, dan Allah babe ki yanke rana.”

Jidderh tana jinsa har ya gama zancensa, ta taɓe baki ta ce, “Allah ya tabbatar da alkairi Safwan.”

Addu’ar da ta yi ba ƙaramin daɗi ya masa ba saboda ƙaunarta da yake yi, wanda hakan ya sanya shi cewa, “Babe guess what!”

Cike da zaƙuwa da kuma gajiya da wayan ta ce, “Yes am getting you.”

“Wayanki ya iso In sha Allahu, zan iya yin komai dan farincikinki, duk lokacin da kika ce a kawo ba ɓata lokaci zai iso gare ki.”

Taɓe baki jidderh ta yi ta ce, “An gode Allah ya ƙara budi.”

Safwan na murmushi ya ce, “Ameen wife material, mace mai godiya da iya addu’a ai ita ce macen da ko wani namiji ke fatan samu, Allah ya miki albarka.”

“Ameen, am please Safwan ina jin bacci”, faɗin Jidderh da ke jin kaman ta saka kuka.

“Okay Babe Allah ya tashe mu lafiya, ki kula mini da kanki sosai kin ji.” “Insha Allah.”

Safwan ya ce, “To Allah ya tashe mu lafiya, ina matuƙar sonki.”

Kittt! haka Jidderh ta kashe wayanta, tana taɓe baki tana faɗin, “Yen yen yen! Ka bi ka dame ni, sai ka ce an ce maka ko ina sonka ne, mutum shegen naci kai ba zaka fahimci ba’a sonka bane, ba abin da ban faɗa ba amma ka maƙale kaman chewing-gum, idan kuma ka ji wani labari nan gaba sai ka ce yaudararka nayi.”

Hajiya Mama da ta idar da addu’anta ta shafa ne, ta aiko wa jidderh dan-ƙwalo ta ce, “Gidanku cubulle, na faɗa miki ba a yiwa namiji haka amma sam ke ba kya ji, wulaƙanta mutum ba abu ne mai kyau ba, tunda kin faɗa masa gaskiya ya ƙi ji, ai sai ki kiyaye kawai ki bisa yadda yake so ku rabu lafiya, maza fa sai a hankali, a wannan zamani ba iya mata ke shige-shige ba, har namiji ya iya bin malamai dan haka ki bi a sannu a rabu lafiya ba na son damuwa.”

Abin da wasu matan ba sa ganewa kenan, maganan wulaƙanta namiji amma sam basa ji, kuma wannan na ɗaya daga cikin abin da ke damun yaranmu mata a yanzu, sai ka ga yarinya ta kwana biyu ba aure, tun tauraronta na haskawa har ya disashe, tabbas an sani komai sai Allah ya nufa ya kuma ƙaddara idan lokacinsa yayi, amma wasu da yawa makamancin iriyar wannan dalili ita ce matsalarsu, mu kiyaye, Allah kuma ya bai wa kowa miji na gari, masu aure Allah ya karo zaman lafiya da haƙuri da juna ya kuma raya zuri’a ya shirya mana su.

Turo baki Jidderh tayi ta ce, “To Hajiya na ji.”

# 𝙨𝙝𝙖

<< Shameekh 1Shameekh 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.