A takaice sabuwar rayuwar da Saratu Bello (Inteesar) ta tsinci kanta kenan a gidan tsohon Brigadier Bello Makarfi. Kullum aiki take tukuru kuma bil hakki, tun safe har dare hakarkarin ta bai ganin kasa, ta zo kwanciya baya yace bai san wannan ba, ta kuma kwanta a dandaryar kasa, ga sanyi da ake mai tsanani a lokacin kin san kuma sanyi irin na marbles, abinki da yarinya ‘yar hutu, bata dauki wata guda ba cikin wannan aikatau din kakkarfan ciwon kiriji da matsiyaciyar mura su kai mata mugun kaye, saida ta galabaita tsahon sati biyu kamin Dela ta watsa mata. . .
Aslm
Sannu da kokari
Muna biye takori
Muna godiya takorin mu👌🤗