Da sauri Ummu ta k’arasa inda take ta hau tambayarta “Mai ya faru??”.
A hankali Mama ta share hawayen da suka sake zubo mata sannan tace
“Bilkisu, barin garin nan zan yi!! Na gama deciding. Ba zan iya ci gaba da zama ba.” Ummu na shirin yin magana
Mama ta katse ta ta hanyar ci gaba da magana “Duk tsawon shekarun nan da aka d’auka ina hak’uri, ina rok’on Allah yasa su Hajiya su sauk’o daga fushin da suke yi da ni amman har yanzu ace sam babu chanji babu wani sassauci daga ita har Abba Madu??
Abun yana damuna ba kad’an ba!
Saboda Allah idan ni nayi mata laifi
Ita Hudan meye nata a ciki?. Yanzu fa naga kiranta ina bin kiran ta d’auka ko gaisuwata bata tsaya amsawaba tace
‘Wai taga Khadijah ta warewa Hudan da Sakina ankon su, In tabbatar na hana Huda zuwa saboda ba zata iya yiwa mutane bayanin wacece ita ba!’.”
Kuka ne mai k’arfi ya kufcewa Mama, cikin kukan tace “Saboda Allah sai kace wata shegiya? Shiyasa kawai na gama yanke shawara zan bar garin nan inaga zaman da nake yi a kusa da su ne ya sanya har yanzun bamu daidaita ba! Watak’il idan muka d’anyi nesa da su abun zai yi sauk’i in basa ganinmu akai akai! Kuma nima har ga Allah hankalina zai fi kwanciya..”
A hankali Ummu ta d’an juyar da kanta ta share hawayenta kafin ta juyo ta cewa Mama “Maganar ‘barin gari’ bata taso ba Mama, Ki tuna fa barin garin nan da kika yi a farko shi ya janyo komai in the first place! Ki kwantar da hankalinki duk abinda kika ga yayi zafi tou zai yi sanyi da izinin Allah. Kiyi hak’uri wata rana sai labari…”
Cikin tausasawa da lafazi masu tsuma zuciya Ummu tayi ta kwantar mata da hankali. Sai da taga ta d’an yi sanyi
sannan tace “Yanzu alfarma d’aya nake nema a wajen ki ‘ki tashi mu tafi asibiti dan Allah’.” Shiruu, Mama tayi, chaan! Ta d’auki wayarta ta kira Baba..
Sai tayi mishi 3 misscalls tukunna a kira na hud’un ya amsa. Bayan sun gaisa ne take ce mishi “tana so zata je asibiti, Ummu zata rakata.” Ba tare da ya tambayi mai yake damunta ba yace
“A dawo lafiya, kar kiyi dare!.” Daga haka ya katse kiran. Shiruu, tayi still da wayar a kunnenta bata cire ba. Jiya har amai tayi a gabanshi amman bai damu ya tambayi me yake damun ta ba! Kuma wai a haka ne yake cewa ‘yana sonta’. Dafa ta d’in da Ummu tayi, tana mai cewa “mai ya ce?”
ne, ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi “Ba komai” Kawai ta iya cewa sannan cewa Ummu “ta mik’o mata hijabinta a wajen kayanta”
daganan suka fito tsakar gidan.
Jikin Huda ba k’aramin sanyi ya sake yi ba dan kasa zama ma tayi a d’akin! Tun lokacin da taji bayanin Mama akan abunda Hajiya Shuwa tace ta juya ta fita, daga d’akin gaba d’aya! Sakina da Sumayya ma suka bi bayanta. Kamar yadda ta shawo kan Mama da kyar haka nan itama Sakina tayi fama da Huda dan da farko itanma cewa tayi ‘guduwar zata yi!’ Wai “tunda Mama ta haifeta bata huta ba har yau! Maybe idan bata nan Maman ta samu sauk’in wasu abubuwan. Ta gaji da ganinta cikin tashin hankali kullum.”
Sai da Sakina ta bud’e mata wuta daga baya ta dawo lallashinta tukunna ta saduda.
A gida suka bar su Sakina Ita da ummu suka tafi asibitin basu dawo ba sai wajajen k’arfe 10:00pm dan sai da aka k’ara mata ruwa Jikinta yayi weak sannan jininta ya hau. Da kyar ma asibitin suka barta ta taho gida da ragowar drip ukun da bata gama shanyewa ba bayan Ummu tayi musu bayanin ‘akwai wata nurse mai chemist a bayan layin su da zata na chanja mata (drip d’in) sannan zuwa gobe da yamma in shaa Allah za su dawo’. Kamar kullum yau ma Ummu ce ta biya bill..
Kusan a tare Adaidaita sahunsu suka tsaya a k’ofar gidan da motar Auwal.
Sam Jalila bata lura da su Mama ba, da yake duk a rud’e take kuma tayi dare tsoronta kar taje Baba ya dawo ya nemeta bai ganta ba! Dan bata san lokaci ya tafi haka ba Sai ta kalli wayarta yanzun tukunna ta gani..
Shiyasa ta zo ta wuce su tana ta sauri nik’i nik’o da ledoji ta shige gidan.
Kallonta Ummu tayi sannan ta kalli motar kafin tace “Allah ya kyauta!”
Daga nan taci gaba da k’ok’arin taimakawa Mama ta samu da sauk’o daga napep d’in saboda har yanzu jikin nata babu kwari.
Suna shiga suka tarar Sumayya tayi bacci Sakina da Huda kuma idonsu biyu sun yi tsuru tsuru da alamun hankalinsu ba a kwance yake ba dukda kuwa sun kira tace musu jikin nata da sauki.
A hanzarce bayan Ummu ta samu Mama ta kwanta ta cewa Sakina
“Maza ta tashi Sumayya Babansu yayi mata waya ya kusan k’arasowa, su samu su wuce.” Kalar tausayi Sakina tayi kafin tace “Ummu dan Allah ki barni mana. Kinga Mama bata da lafiya. Itama Huda ba zata ji dad’in zaman haka ba.” Nan itama Hudan ta saka baki suka hau rok’ar Ummu..
Shiruu, Ummu tayi kafin tace “to muje ki yiwa Babanku bayani.
Gashi nan ma na san shi yake kirana.”
Tayi maganar tana d’aukar wayar ta kara a kunnenta..
Hakan kuwa akayi Allah ya taimaka ya barta. Sai da Ummu ta je ta samu mai chemist d’in tabbatar mata ‘gobe da safen dan Allah taje ta sauyawa Mama drip d’in kafin ta k’araso’ tukunna suka wuce ita da Baban Sakina da Sumayya.
Jalila tana shiga d’akin taga duhu, dan haka ta zaro wayarta ta d’an haska. Ga mamakinta sai taga Umma kwance tana ta sharb’ar barcinta!. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Barka na, gobe idan ta tambaya sai ince da wuri na dawo..” Sad’af!!sad’af!! Ta wuce ta ajjiye ledojin ta fara k’ok’arin kashe wayar gudun kar Umma ta farka tana yi tana d’an kallonta. Sai dai kuma bata kai ga kashe wayartata ba taga Umman ta bud’e idanunta. Nan take ta diririce ta hau kame kame “Au um Umma k kin farka? Na d’auka kin yi bacci mai nisa ne.”
“Zo nan Jalila” Shine abunda Umman tace tana mai mik’ewa ta zauna a kan gadon.
A hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna. Kallonta Umman tayi ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Jalila, amma kin dai san halin Babanku ko? Ga waennan munafukan y’an bak’in ciki suma har sun fara k’ananun maganganu. Nan gaba idan kin san za ki dad’e ki dinga fad’amin sai inyi k’aryar ‘nice na aikeki’ ko kuma ince kin yi bacci tuntuni. Allah ne yau ya taimake mu lokacin da Baban naku ya dawo bai nemeki ba! Na san da sai mun gane kuranmu daga ni har ke
dan na san kowa sai yaji kanmu da shi, gashi gida ba mu kad’ai ba cike da y’an bak’in ciiki. Da kyar ma na lallab’a na bud’e miki k’ofa bayan naji ya shiga wanka amman da har ya rufe.”
“To Umman mu, in shaa Allah.” Shine abunda Jalila tace, had’e da sauk’e ajiyar zuciya dan Ita har ga Allah tayi tunanin Umman zata yi mata fad’an da yafi wannan.
Umman har ta koma zata kwanta idanunta suka kai kan manyan ledojin da Jalilan ta shigo da su! Dan haka ta mik’e. Kallonta tayi sannan ta mayar da idanunta kan ledojin kafin tace “Ke kika shigo da su?”
Mik’ewa Jalilan tayi ta nufi inda ta ajjiye ledojin ta d’auko sannan tace “Eh, shopping muka je shiyasa ma muka yi daren.” Tana fad’i hakan tana mai k’arasowa ta ajjiye ledojin a gaban ta.
Sauk’owa Umman tayi ta hau bubbud’ewa tana cewa “Nifa daman k’amshin ne ma ya farkar da ni
Da farko mafarki na fara yi ‘inacin kaji’ sai kuma na fara jiyo k’amshi a hankali a hankali harya zo yayi mini yawa. Ashe d’an kirki ne ya had’o ko da su…” Tana maganar tana bud’e ledojin one by one. Ledar farko Fresh milk ne masu sanyi da chocolate masu mugun tsada da ice cream da popsicles birjik!
D’ayar ledar kuma kaji ne an yayyanka ledarsu daban sai k’aramin pizza da su shawarma da burger.
Ledar ice cream d’in Umma ta sake dubawa dan d’azu kamar taji wani abun a ciki bayan abunda idanunta suka gani, ai kuwa nan ta zaro kud’i!
Tun kafin tace wani abun Jalilan tace
“Ni kinga ban ma san ya saka ba.”
Jinjina kai Umman tayi kafin tace “Hmm, Jalila ina hango waenda za a kwantar a emergency ranar aurenki!”
Tana magana tana juya kud’in.
Rabawa tayi biyu, ta d’auki rabi ta bata rabi. Jalila kwata kwata hankalinta ba a gurin yake ba sannan jikinta duk yayi sanyi shiyasa ma bata wani damu ba, tasa hannu kawai ta karb’a
tana kallon Umma wadda ta mik’e taje ta ajjiye kud’in ta dawo ta zauna tana cewa “Ai gobe mai kankat! Zan cewa malan Yusuf yayi mishi. Yarinya burin mu ya kusan cika, Allah ya kashe ya bamu.” Daga nan ta janyo ledar kaji ta hau ci sannan ta b’alle marfin fresh milk tana ci tana korawa da shi.
Daman yau bata wani ci tuwon dare ba dan har ga Allah tuwo ya ginsheta wallahi ko sunanshi bata so taji an kira.
Sai da Umma taci kusan rabi, ta shanye fresh milk roba d’aya, tayi gyatsa!! Tukunna ta juyo ta kalli Jalila wadda kwata kwata hankalinta baya d’akin kana ganinta ka san tunani take yi, ta k’urawa waje d’aya ido kawai tanata kallo!.
Magana Umma tayi mata taga bata kulata ba, kamar ma bata jita ba! Dan haka ta kama k’afarta ta jijjiga sannan da k’arfi tace “Ke!!” Firgigit! Jalila tayi ta juyo tana kallonta, itama Umman ita take kallo tana sake nazartarta kafin tace “Tunanin me kike yi haka??”
Ajiyar zuciya Jalila ta sauk’e
sannan tace “Umma nifa Auwal d’innan na kasa gane kanshi!
A iya fahimta ta fa kamar yana tunanin ni budurwar Arshaad ce.
Sannan Umma, kwata kwata zuwanshi na biyu kenan amman na fahimci d’an iska ne! Kinga ranar farko rike min hannu kawai yayi ko? Amman, wallahi idan na fad’a miki abubuwan da yayi mini yau ke kanki sai kince ‘kar in sake kulashi’.”
Kallonta Umman ta hauyi irin kallon k’urillar nan! Kafin ta ajjiye robar hannunta tace “Kuma na ganki Garau!!” Cike da rashin fahimta Jalila take kallonta…
Fahimtar hakan (Jalilan bata fahimce ta ba) da Umman tayi ne yasa tace “Hmm” Kawai. Sai kuma ta sake cewa
“me yayi miki?”
Kame kame ta hau yi kafin tace
“Har da rungumeni yayi, sannan ya dinga…”Sai kuma tayi shiru. Tsaki Umman tayi sannan tace “Iyaka wannan ne Ina?? Jalila naga alamar baki da labarin ‘Hudan! Ita har makarantar kwana aka fake da kaita.’ Ni na haifeki, inaso ki fahimci ba zan tab’a cutar da ke ba! Yanzu duniyarnan ta chanza! Kuma Yaron nan burinmu a kansa ‘aure’ Allah na tuba ko me ma yayi miki ai dai shi d’in ne zai aurenki a k’arshe ko? Yanzu abinda nake so dake ‘Ki bishi a hankali kawai! Gudun kar ya sub’uce mana’
Ki bishi kawai a duk yadda yace!
Ki barni da shi, ni na san me zan yi.”
A hankali Jalilan tace “Umma to ba yadda wai za ayi In auri Ya Arshaad? dole sai wannan? Nifa shi nake so!”.
Cikin fad’e Umma tace “Jalila wallahi zan ci buhun uban ki daga ke har Arshaad d’in! Nace miki ki hak’ura da shi ko? Ga hanya nan mafi sauk’i amman kin gagara fahimta? Da me Arshaad d’in yafi wanann??.
Cikin katseta Jalila tace “Umma shine a zuciyata da haka kawai ya fishi…”
Buge mata baki Umman tayi
kafin tace “Bara kiji in fito miki a mutum!! Wallahi ba zan iya kokawar bin Malamai da masu kud’i ba!
Ba zai yiu inje in bada dubu talatin mai kud’i ya zo ya ajjiye dubu d’ari ko d’ari biyu sannan kiyi tunanin za ai mana aiki iri d’aya ba! A nawa tunanin fa kenan, bansan ya naki yake a k’aramar kwakwalwarki ba. Ki cire wata soyayya a ranki. A zamanin mu ne muka bi soyayya, kuma gashi muna cin ubanmu!
Gata nake yi miki Jalila ki bari
mu nutsu waje d’aya mu yi abinda zai yiu, kar ki je kiyi saki reshe kama ganye! Na dai fad’a miki.” Tana gama fad’in haka ta mik’e tace mata “Asubah ta gari Bara in je ki saki net dan yau akwai sauro .” Daga nan ta fice ta nufi d’akin Baba.
Jalila ta dad’e tana tufka da warwara daga k’arshe ta yankee shawarar tabi zab’in Umma! Haka nan ta hak’ura da Arshaad ba dan zuciyarta tana so ba.
Ta zo kwanciya kenan kiran Auwal ya shigo wayarta! Tana gani har ta tsinke bata d’auka ba! Tabbas duk tsaurin idonta da rashin kunyarta yau ta had’u da kakanta! Kuma kalli ba kunya ba tsoron Allah kiranta ma yake yi
Ita kam kafin ta samu ta sake iya had’a ido da shi ma ai sai nan da kwana biyu ko uku ma..
Miss call d’aya ta samu daga gareshi daga nan bai sake kira ba! Dan ba zai tsaya kuchaka kamar ta tana ja mishi aji ba! Although ya san a d’an rikice take har yanzu wanda hakan ne ma ya sake tabbatar mishi da ‘Yarinyar sabon hannu ce!’ Ko banza ya san zai tsinci dami akala! Amman duk da haka
zai yi sauri ne kawai yayi abunda zai yi ya gama ya kuma gano dalilin alak’arta da Arshaad daga nan ya had’a mishi bomb d’in da yaga ya dace dashi! Ita kuma ya wurga ta a dustbin! Tun kafin wani a cikin Abokanayen sa ya gano yana kula mace irinta. Although, she’s beautiful, tabbas tana da kyau, ta fanni daban daban wanda hakan ne ma ya sanya ya d’an sake janta a jiki amman dai still ba zai bari Abokanayensa su ga yana kula a girl like her, ba!.