Skip to content
Part 19 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

A Rikice Sameer ya koma gida cike da tashin hankali akan turjiyar da ya kula Farida za ta kawo mishi har tana fadin su musulmi ne kenan dai idan ya fahimce ta ba za ta yarda da mafitar da ya samo musu ba? Ba za ta yarda ta mara mishi baya ba?

Ya jima bai runtsa ba yana tunanin idan Farida ta watsa mishi k’asa a ido shi kenan ya shiga uku matukar dai bata yarda ta mara mishi baya ba. Ita kadai ce tabbaccin shi to ta fara Sharar fagge da wannan maganar.

Gari ya waye idanun sun yi mishi zajir saboda damuwa. Ruwan zafi yake son ya samu ya Sha Amma shi din ba gwanin iya ko da Ruwan Lipton ba . Tunda Al Amarin Rabuwar su da Farida ya faru ya shiga gararin Rayuwa abinci wannan sai dai yaje gida ya Roki abinci wurin Haj wacce zata bashi Abincin tana balbale shi da Bak’ak’en maganganu akan ta Gaji da bashi Abincin ta don ba zata iya shiga kitchen tayi girkin ta Yana Zuwa ya wage Baki ya lamushe Mata ba. Tun Yana jurewa har ya koma cin na restaurant Wanda Sam baya gamsar da shi Dole yake Hak’ura da Wanda Ake fad’a mishi Bak’ak’en maganganun don shine Wanda ya yarda yafi kowane abinci Dadi a Duniya kafin na Farida ya biyo bayan shi Wanda ya tabbatar da Hajiyar Farida itama gwana ce a fannin girkin shiyasa ma Farida ba daga baya ba. Ko akan Rashin daddadan girkin Farida yaci Mai Kaunar shi ya Taya shi alhini…

Yayi wanka da Ruwan zafi ya samu k’arfin jikin shi ya Mike zuwa gidan su…

Yayi sallama Haj ta Amsa mishi tana zaune tana Duba atamfar da aka kawo Mata…

Yana Duke a Gaban ta Yana Gaishe ta bayan sun gama Gaisawa ta ce

“Ga shi can na aje Maka na San dai abin Kari ne matsalar ka to gashi can ka dauka.

Wani Abu yazo mishi a Wuya ya kasa wucewa sai kawai yaji hawaye na bin idon shi . Shi Kam a yau ba matsalar abin Karin ne damuwar shi ba Amma dubi yadda Haj ke Mishi Arashi don kawai tsautsayi ya fada mishi ya saki matar shi shikenan duk wata Kima tashi ta zube a idon Haj wacce ta tattaro Dukkan laifin ta Dora akan shi . Babu Mai tausaya mishi bare ya Dubi Halin da yake ciki…

Haj da taga Bai motsa ba ta kalle shi sai taga hawaye ba gudu a fuskar shi…

“Subhanallahi wani abu ya faru ne Sameer?

Me kake wa kuka haka da girman ka?…

“To Haj in ban yi kuka ba in yi me? Yanzu Hajiya har a tambaye ni me yake damu na? Shikenan Saboda Allah ni kadai nake damuwa ta Babu Wanda ya kula da Halin da nake ciki bare ya Taya ni jimami? Kowa ya kawar da Kai ya kyale ni Ina ta Bakin ciki na ni kadai. ? Da karfin tsiya an haramta min matata da Aure na Amma Babu Mai damuwa da Halin da nake ciki sai ni kad’ai Haj? Sai kace bani da kowa ni kadai nake bare a Samu Mai tausaya min? Ni kadai na San Halin da nake ciki Haj ni kadai nasan irin Balakin da nake Sha Amma duk yawan dangi na da Yan Uwa Haj har ku Amma ace Babu tayani alhini da jimami ?

Haj ta Dube shi Dariya na shirin kwace Mata amma ta maze tana fadin

“Au ! Ka ce haushin kowa kakeji tunda Babu Wanda ya Taya ka alhini da jimami. To Amma wane irin alhinin da jimamin zamu taya ka ? Mu Dora Hannu aka Muna kwatsa ihu ko kuwa muyi ta Rusa kuka sai kace muyi Shiru? Ai da kaji Abinda Ake ta fada Maka Sameer da baka zo wannan galan din ba. Idan Akwai Wanda ya kamata ya Taya ka alhini da jimami to Ina Ganin muguwar zuciyar ka ce da zuga ka ta kuma Kai ka ta baro ita ya kamata kuyi alhini da jimami tare da ita Tunda ai Bata tuna Maka kana da mu ba ta fada Maka ka dauka kaga itace wacce tafi cancantar ku Hak’a ku binne a tare da ita Amma mu me kake so muyi Maka Kuma bayan gaskiyar da mukayi ta nuna Maka ka Saka kafa ka Shure Sameer? Kuma Kai yanzu har kana iya fadar cewa Wani ya Haramta Maka Aure da matar ka? To naji tsaya ma Kai yanzu a me kake son ce mini ? Ina ce Saki UKU kayi ko kuwa kana inkarin Hakan ? Ko dai bakaje makaranta ba Sameer ai ka tsinci Auren saki UKU ya haramta a titi da gidajen radio…

“Haj ni fa ba saki UKU nayi Mata ba waccan na karshen cikin fushin ZUCIYA nayi shi Amma kowa sai Cewa Ake Shima wai saki ne…

“To kaga don Allah mu Rufe wannan babin Sameer Allah ya jikan baba iro da Ragama yau da Yana Raye da ya tuna Maka da Abinda yayi ta maimaita Maka Sameer Amma kayi kunnen Uwar shegu. Ni Kam zanso naji Alamar da ta Alamta Maka Wani Abu akan Farida da har ka Hana kanka zaman lafiya ka addabi kanka da zargin ta Alhalin ka San kana son matar ka Amma Abu kadan sai ka furta kalmar saki wacce Dukkan ukun Nan Babu wacce bakayi nadama fin yawan Shekarun ka ba har dai kazo gargara ka cewa kanka kurunkus kan Dan Bera to mu Rufe wannan babin don Allah mu Bude Wani Wanda zaka ce min ka ga wata kana so ka aura don ni yanzu shi nafi bukatar ji daga gareka don na San babu yadda za ayi Namijin da ya Rayu da mace sama da Shekara Tara Rayuwa tayi Mishi Dadi matukar babu wata macen a tare Dashi…

“Ba zan iya son wata mace bayan Farida ba Haj . Farida kawai nake so Kuma ita nake so ki fahimce ni mu dawo da Auren mu don Allah ki fahimce ni Haj…

“To ayi Yaya kenan Sameer? Ta fada a tsorace don ta gama Gane ya kusa ya zautu…

Ya gyara Zaman shi a gaban Haj Yana Fadin
“Na samu Wani Alfa a garin partacout na zayyane mishi Halin da nake ciki ya Kuma fahimce ni shine ya bani wata fatawa wacce na gamsu da ita…

“Waye haka Alfa? Haj ta tambaya tana kure shi da Kallo.

“Wani limamin Yoruba ne Kuma Yana da sani na Sosai tunda har karatu yake badawa Kuma shine limamin unguwar da nake…

“To shi kuma me ya ce maka?

“Ya ce min lallai sakin da nayi a karshe Wanda nayi cikin fishi ba saki bane makaruhi ne tunda Sabanin zato ne sai Wanda nayi akan daidai Amma Banda wannan . Sai dai in Ahali na ko na matar sun kafe akan saki ne to Akwai Wani Abu da yace min suna Yi a kabilar su wai shi ujun Wanda Ake nade hannun mijin da yayi sakin da wani zare ko mayani Wanda za a tamke tamau ace ya since cikin dakika UKU idan ya sunce cikin dakika UKU to Auren su ya koma sai dai in ya kasa suncewa ne to Babu maganar auren sai dai suyi hak’uri…

“Kuma Kai kaji ka gamsu da Hakan kenan?
Haj ta tambaye shi tana mamakin shi .

Yayi saurin kada Mata kanshi Alamar ya yarda.

“Na yarda Mana haj tunda dama ni a zuciya ta ba sakin na ayyana ba fushi ne kawai.

“To Amma shi a kabilar su ta Yoruba Ake hakan ai Kai ma Yoruban ne ? Kuma Kai yanzu ka yarda a nade Maka hannun ka ware kullin a dakika UKU? To in ka Kasa Kuma har dakika ukun?

“Shiyasa nake so ki fahimce ni Hajiya.

“Ba zan tab’a fahimtar ka ba Sameer tashi ka bani wuri . Ni Kam ban sani Wani SARKI ba face Allah SARKI. Ba zan taba bari Farida ta dawo gareka ba saboda Ina guje Maka hadarin da kake Shirin Kai kanka Kai da Farida sai dai ko idan tayi Wani Auren Amma dai a yanzu haramiya gara ka Rik’e wannan a Ranka ka Kuma Saka tauhidi don na lura shaidan na Shirin yaudarar ka to ka dawo hankalin ka. Tunda akayi Duniya a garin musulunci dai Babu inda aka halatta Auren saki UKU Kuma Kai baka Isa ka kawo shi a yanzu ba. Don haka garan Maka kawai ka shiga laluben matar Aure shine ma inin Zance Amma wannan kame kamen halaka kawai kake kokarin Kai kanka Sameer to in Kai idon ka ya Rufe ni da sauran mutanen da suka tabbatar maka da haramcin Auren ku Hankalin mu Bai gushe ba kaje ka dauki kaddara ka Rasa Abinda yafi Auren Farida Kuma kayi hak’uri gashi kana ta Rayuwa to itama in ka Rasa ta ka Roki Allah Alherin da yake gareshi yafiye Maka wannan Rara gefen. Maganar Auren ku Bai haramta ba ko wani ya baka wata tsinanniyar fatawa kar ka Kuma tunkaro ni da ita in ka yarda da fatawar Al Kur ani da Shari ar musulunci baka bukatar wata da zata zamar da Kai tashi daga gaba na Daga yau muce kurunkus kan Dan Bera akan Rabuwar ka da Farida kaji na fada maka. Da ka dauki Abinda Ake fad’a Maka da ba a zo Nan ba.

Kuka yake a gaban Haj wacce ta bar Mishi wurin.

Ya jima kafin ya tashi ya bar Gidan inda ya nufi Hajiyar Farida don a yanzu ita kadaice tabbaccin shi duk da Yana hango Rashin nasara a gareta ma tunda tashi Uwar ma taki Goya mishi baya ai kar yayi mamaki idan itama ta kasa yarda da Hikimar shi.

Yana sallama gaban Farida ya Fadi Amma sai tayi lub a d’aki yayin da haj take Sakawa Hanan hular sanyi tana Jin sallamar Uban ta ta auna Aguje ta makale shi ya daga ta Yana sumbatar ta.

Ya zauna a gaban Haj Yana gaishe ta ta Amsa fuskar a sake Suka gaisa.

Ya danyi shiru har Haj tace mishi, “Yaya ne Sameer?

“Haj dama wata magana ce nazo da ita Duk mutane sun kasa fahimta ta Kuma sai Cewa suke wai Auren mu ya kare tsakani na da Farida Alhalin na tambaye Wani malami yace akwai sauran igiyar Daya a tsakanin mu tunda cikin fushi Nayi shine nake so Haj ki kwatantawa Hajiyar mu don har da ita a cikin Wanda Suka kasa fahimta ta Akwai hanyoyi da yawa na gyaran auren mu Amma kowa ya kasa fahimta ta.

Yayi shiru Yana kallon Haj wacce ta kame Baki cike da Mamaki.

Shiru ya Ratsa su kafin Haj ta sauke AJIYAR ZUCIYA tana fadin

“Sameer dukkan Wanda ya fada Maka Auren ku ya lalace ba kasa fahimtar ka yayi ba gaskiya ya fada Maka. Wannan itace kaddara in kaji ana fadar kaddara to itace wannan wacce mafi yawan ta take Zuwa da abubuwa marasa Dadi. Nima Kuma in har zan fad’a maka gaskiya to zance Auren ku Kai da Farida ya lalace ayi Hak’uri matukar dai ana son kiyaye dokokin Ubangiji. Kuma ka yarda Hajiyar ka ta fahimce ka Kuma Dukkan Duniya idan Akwai Wani Mai sonka to bayan ta zai biyo Sameer don ta so ka ne tun Bata sanka ba. Da Bata son ka da ta zabar da cikin ka tun kafin ta San me zata Haifa….

Hawaye ya kawo mishi Yana Fadin
“Haj kece kawai tabbacci na a yanzu idan kika ce ba haka ba shikenan SHIGA UKU ta same ni dama Farida ta fara fada min ba zata yarda ba…

“Ni Kuma Ina son nuna maka tabbaccin Yana wurin Allah Sameer ba ni ba. Ni da Kai duka tassarrafin mu Yana wurin Allah Amma dai ka yarda Kuma ka Amince dukkan Wanda ya nuna maka illar Komen Auren ku masoyin ku ne ba makiyi ba kamar yadda zuciyar ka take Raya Maka. Don Allah don ANNABI Sameer kayi hak’uri ka sakawa zuciyar ka Aminci wata Rana ma za a wayi gari ko Kai ne ko Farida Ina ce ku duka Kun Rasa iyayen ku Maza Kuma gaku Kuna Rayuwa bare wata Farida da in Allah yaso sai ya hada ka da wacce ta fi ta. Kuma Kai da Farida ai Baku Rabu ba ko tana Gidan Wani mijin Saddam da Hanan sun gama hada ku ….

Ya dire hannan da take kwance a jiki shi daboda shigar maganar Haj tacewa ko Farida tana Gidan Wani mijin wannan maganar ta tab’a shi matuka Gaya. Don haka ya Mike Yana dire Hanan yayiwa Haj Sallama wacce ta Gane Bai so gaskiyar da ta sanar da shi ba. To Amma Kuma gaskiya Daya ce duk dacin ta kuwa za a dawo Mata ko anje za a dawo …

Farida tana Jin su da Haj har ya fice daga gidan inda taji hawaye Yana bin fuskar ta tausayin shi take matuka Gaya. Wani Abu Yana tab’a zuciyar ta idan ta tuna Yana cike da damuwa Amma Yaya zasuyi da kaddara? Ta Bakin Haj wannan itace kaddarar su Amma ita Kam tana Hangen ta yadda za ta iya duban Wani Namijin da sunan Aure….

A Ranar Sameer ya hada Kayan shi ya wuce partacout ko sallama baiyiwa su Haj ba don ya ganin su Duka suna maraba da Rabuwar su da Farida ya Isa partacout Amma Kuma damuwa da Rashin sukuni ya ishe shi har ya Soma laluben mafita don baiji za ayi barin Farida ba. Amma Kuma ya tabbatar Babu wata hanya da zai kuma samun Farida a karo na Biyu kar ma ace Yaya dauda yaji maganar. Sai kawai yaga Wani ya kamata ya Samu ya Auri Faridar ya biya shi in yaso tayi Auren KISAN WUTA in yaso sai a Sako mishi abin shi ya dawo a mayar da Auren su shikenan Abinda zaiyi Amma fa in yayi sake to an Raba su da Farida Rabuwa Kuma ta har Abada.

Wannan shawara da yayi shi ya Dan saukar mishi da Aminci duk da dai Bai yarda koma waye zai hada Auren da shi ya tab’a mishi Mata ba. Domin kuwa Abinda yake yiwa kenan ace Wani Namiji ya tab’a mishi Farida hakikatan gara ya mutu da dai ya samu mummunan wannan Labarin Wallahi gara mutuwar shi don haka sai ya kasance cikin damuwa duk da ya na ganin kamar ya Sami mafita Amma Kuma Yana sane da shi Auren baya tabbata ko anyi sai anyi Abinda baya son raayin Yaya kenan.

<< Tana Kasa Tana Dabo 18Tana Kasa Tana Dabo 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×