Sameer yabi bayan Baba Yusha U da kallo tamtar Wani sakarai ko Wanda yaga abin Mamaki.
Tamkar Wanda aka zuk'ewa Jinin jiki haka ya zama sai maimaita Kalmar Baba Yusha U yake ta an daurawa Farida Aure. So yake ya banbance daurin Auren da Wanda ya Sani da Wanda yake son sani a Yanzu.
Farida matar shi aka daurawa Aure? Da wa ? Mai gemu! Zuciyar shi ta sanar Dashi.
Ya Mike da sauri Yana Jin Bai YARDA ba ba dai Faridar sa ba Kuma ba dai Auren Mai gemu gare ta ba.
Idanun shi jajir ya shiga gidan ko. . .