Lokacin da Sameer ya fita Daga Gidan su Farida idon shi a Rufe ya fita Saboda kid'ima don ko a mafarki Bai tab'a zaton Jin wadan Nan kalaman daga Bakin Farida ba sai gashi a yau Farida ce ke Fadin ta Hak'ura da shi idan shine Rayuwar ta ta zabi ta zama GAWA wata Kil idan yaga tudun kabarin ta zai Raka ta da ADDU A Akasin tana Raye.
Bai lura ba idon shi a Rufe sai ji yayi ya afka kwatamin Dake dab da motar shi wacce Mustafa yake ciki Yana Jiran fitowar shi.
Da sauri. . .