Skip to content
Part 38 of 66 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Shama ta shigo falon a guje tana kankame wasila tana Fadin

“Ke Albishirin ki ? Don Allah ce min Goro fari kwalele? Kai Wallahi sa ar ki yawa gareta Wallahi wasila wai kin San waye a waje? Wallahi distinguish senator Yan doma ne Kuma wai ke yake nema? Gaskiya Allah ya Yi Miki baiwa da yawa wasila duk Wanda zaizo gareki BABBAN mutum ne Wanda zai kankaro Miki girma? Ga Kuma kudi Babu Abinda ba Zaki samu ba.

Wasila ta dubi Shama da take ta kambama Yan Doma Wanda ta Gane saboda sunan da taji. In Bata manta ba shine Wanda Suka hadu a Filin jirgin yace Gona ya bari su gaisa yace ba zai bari ya Ganta ba.

“Ni ya ce Miki yake Nema?”

“Ta tambaye Shama wacce ke ta Fadin ta tashi ta shirya Yana jiran ta.”

“Ki je ki sallame shi Shama don ni yanzu na sauka Daga wannan layin. Idan dai haka bariki take to nayi kaicon shigar ta sama da Shekarun Uwa ta da Uba ba. Namiji Daya zan iya saurara shine Wanda zai fuskance ni da maganar Aure Amma iskanci Kam na Rufe kofar.”

“Haba Hajiya ta ko kin rufe kofa dai ai kya yi na bankwana. Kuma in kika yi saurin sallamar shi ai kinyi Riga malam masallaci kije kiji Abinda ya kawo shi kika sani ko Auren ne ya kawo shi?”

“Ke Shama bana bukatar Ganin shi kije ki sallame shi . Tunda a bariki nake Babu Namijin da zai min kallon Kima duk Kuma Wanda zai zo ba da komai zai zo ba sai bariki tunda a ciki ya ganni . Da ya Ganni a gaban iyaye na wannan Kam karya yake ya zo min da bariki.

“Don Allah ki rufa mana asiri kar ki yiwa wannan Arzikin Kullin tsiya ya tarwatse . In kika koreeshi ai ko ni kinja min don Wani Abu nake so Hannun gayen Nan wai kuwa Kinga wankan shi da kyallin da yake ? Na Rantse Miki da zoben hannun shi kadai ya Isa ya siyi Rabin garin Abuja Wallahi . Bari na Kai mishi Ruwa don Allah tashi ki dan gyara kije kiji Abinda ya kawo shi in kika wuce Arzikin Naki ba tare da kin sani ba fa wurin gajen hakuri?…

Da sauri Shama ta hada tire Wanda ta shake da kayan lemu da kayan kwalam ta nufi inda ta sauke Bak’on wato Sanata Yan doma ta girke mishi kayan tana ta Rawar jiki tana fadin wasila tana Zuwa.

Ya fito da Rafa ta Dubu Dubu guda UKU ya bawa Shama wacce ta karba tana ta Godiya ta fice tana kankame da kudin Sabbi karr.

“Kin Gani ? Don Allah tashi wasila ko Zaki sallame shi dai ba yanzu ba in dai ba black stomach Zakiyi min ba.

Wasila ta Dube ta taja tsaki kafin ta wuce Zuwa inda ta sauke shi. Ba don komai yasa ta amsa Kiran Nashi ba don taji a Ranta kamar ba Abinda take zato ne ya kawo shi ba. Kuma ita da kanta Taji honorable Gona Yana fadin shi da Babu shi a harka Mata meye nashi na tankawa wasila? Ko a wannan kadai ta fasa ta Isa ta Gane ba Lallai bariki ce ta kawo shi ba tunda ma har shaida ya Samu akan baya harka da Mata.

Ta SHIGA da sallama ya tado kanshi daga wayar da yake tabawa ya dago Yana Amsawa.

Ta zauna akan kujera suna fuskantar juna idon su ya Hadu yayi Mata welcomed da wani tattausan murmushi Yana Fadin.

“My flowers

Tayi murmushi tana Fadin, “Barka da yamma distinguish.

“Barkan mu dai sai kika ganni babu sanarwa?”

“Na kuma yi mamakin yadda ka iya gane gidan nan tunda ban San ka San Nan din ba.”

“Ai ba zai yi min wahalar ganowa ba Saboda Ina son Ganin ki da gaske Kinga kuwa ai Babu mamaki don na Gano Gidan Nan. Tun Ranar da na ganki tare da gona na kasa Samun nutsuwa Babu Inda ban neme ki ba Amma na kasa Samun ki har gona nayiwa magana ya bani lambar wayar ki Amma ya Hana ni Kuma tunda na ganki Naji na samu matar Aure. Ba zan boye Miki ba ni din haka nake bani da Mata tunda matata ta Rasu ban Kara Aure ba sai fa yanzu da na ganki Naji nayi Mata don Haka Ina son in Roki wata Alfarma duk Wani Namiji da kika San kina harka da shi to ki sallame shi Kuma nayi Miki alkawarin ko nawa kike samu a tare da su zan linka Miki sau UKU don Ina son na datse Dukkan wata alaka tsakanin ki da Mazan waje tunda ni Kam Auren ki nake son Nayi Ina fatan ban shiga Rayuwar ki na takura ki ba?

Ta yi Shiru tana sauraren shi har ya Sauka

“Banji Abinda kika ce ba ? “To ai ni ban san Abinda zance Maka ba.

“Kina da ra’ayin ki Kuma kina da tsari. Idan Babu Ra ayin Abinda Nazo da shi wasila kar ki Cuci kanki ki fada min zan fahimce ki Amma dai na San wannan sa ar da kika Samu irin ta Mata da yawa suke nema . Kuma ko ba komai Auren yafi mutunci Kuma ga kudin da zan Baki a maimakon Hana ki harkokin ki da Nayi tunda ta iya yuwuwar Baki tashi ajewa ba na Saka ki ajewa ko ba haka ba?

Taso kaucewa mutumin Nan Amma sai ta Gane ya hada kwalitin da zata iya Auren shi don haka Bata ja ba ta sallama Amma ta ce ya bari ta koma gida sai ya bita can ayi magana.

Da zasu yi sallama tayi Mamakin kyautar shi gareta haka suka Rabu Yana Kara Rik’e zuciyar ta da kalar tashi soyayya.

A cikin satin da zata taho katsina ne ta Samu wayar honorable gona wanda ta dauka taji yana fadin

“Wai sweetie da gaske ne zaki auri Yan doma? Ke kuwa me zai sa ki auri wannan mutumin? To in…

“Abunda zai sa na Aure shi shine wanda ya hana na Aure ka Gona.

“Naji na yarda Amma don Allah Kar ki yarda ki Auri Mutumin Nan ba mutumin kirki ba ne Dani kika Fi dacewa don Allah ki watsar da maganar shi ni zan Aure ki Wallahi.

“Ka makara Gona don ko Kai kadai kayi saura a Duniya ba zan Aure ka ba don ka Gane Matan ka ne mahaukatan da suke haukan ka mutu su gaje ka yanzu don kaji zan auri Wani shine ka yarda ka Shirya Aure na? To Yaya kenan za ayi? In bar shi Yan doman in ce na fasa Kai zan Aura ? Ayya sai dai nace Maka try again later Amma yanzu dai wannan zancen is switch off.

“Naji Naji sweet Amma ko ba Zaki Aure ni ba to na Rok’e ki da ki samu Wani ba wannan mutumin ba bana son ki da shi Wallahi.

“Ni kuma da shi nake son Kaina Gona sai Yaya?”

“Sai nayi Miki fatan Alheri.

“To da a haka ka tsaya da nace Sam barka Kuma in ce na gode amma idan har ka san lamarin da akwai sukar Janabi sai nace ka rik’e zancen sai anjima.

Ta kashe wayar ta bar gona yana fad’in ya Gode.

Kulawar da distinguish Yan doma yake Bata tasa taji ta Aminta da Auren shi don kusan kullum Yana faman Kiran ta da Kara fasa Mata Kai ga aike kullum Yana hanyar Yi Mata aike da tura mata kudi a account din ta.

Kai hatta Shama kam ta San da zaman Yan Doma ta Kuma shaida.

Wasila ta hada Kayan ta zata wuce katsina a yau Shekarar ta daya da wata uku Rabon ta da gida ko waya Bata Kira Goggo ba bare ta Kira sagir taji lafiyar Yusra da Zainab. Shima Kuma ko da wasa Bai neme ta ba Abunda ta tabbatar yaron ya shaka da yawa don in da tafiyar ta lafiya ce sai ya Kira ta yaji Halin da take Amma da yake ta San Abinda ya Gani Dole ya manta da ita a Rayuwar sa.

Shama kam Bata so tafiyar Nan ta wasila ba don tana ganin yanzu ne ya kamata ta Samu Alheri a sanadin wasila Amma Kuma gashi zata barta Dole Babu Kuma yadda Zatayi.

Sukayi sallama Shama na Fadin idan an yanke Ranar Auren ta Kira ta don zata zo katsina ayi bikin tare da ita.

Distinguish ne ya yankar Mata tikitin jirgi har zuwa katsina.

Ta sauka a garin katsina wanda take ganin yayi matukar sauya Mata a shekarw daya da watanni Amma taga komai ya sauya Mata.

Ta iso kofar gidan su cike da matsanancin firgici don Bata san irin karbar da Goggo zatayi mata ba.

Tayi sallama a gidan cikin sanyin jiki.

Goggo da murja da suke magana suka juyo a tare Saboda kamar da muryar tayi musu da muryat wasila sai Kuma idon su duka ya fada akan wasilar wacce tayi tsaye a bakin kofar suna kallon kallo tsakanin ta da Goggo da Anty Murja.

Murja ce ta amsa sallamar yayin da Goggo ta ballawa Murja harara wacce ta Sa ta kame Bakin ta don ta gane abinda Goggo take nufi.

Wasila ta isa inda suke zaune suna magana ta durkusa tana fadin

“Goggo ki yafe mini don Allah kiyi min Afuwa Abinda nayi kuskure ne.

“Allah ya yafe Mana Baki Daya.

Cewar Goggo wacce ta mayar da Hankalin ta wurin murja tana Fadin

“Kinga ki fa fadawa ISHAQ din yayi Mata da gaske Tasha maganin Nan don Wallahi tace ba zata Sha shi ba laulayi Zatayi Mai tsanani dama ciki in ya Fara da haka ai Wahala Ake Sha Amma in Tasha maganin Nan har Maganin Zak’in nakuda yakeyi Allah ya Raba lafiya.

“Anty murja Ina wuni? Ta fada jiki a sanyaye don tunda taji ana wannan maganar ta San maimuna ce ke laulayi.

“Lafiya Lau ya kike?

“Ke murje tashi ki tafi gida tunda mun gama maganar kicewa maimuna Tasha maganin Nan zata samu Sauki zan zo na dubata Allah ya Raba lafiya.

Murja ta Mike tana Saka hujabin ta inda take ta Duban wasila ita kanta wasilar tasan don Kar murjar tace Zatayi mata magana.

“To Goggo Allah Ya ba mu Alheri.

Goggo ta Mike tana daukar buta ta daura alwala ta watsar da wasila Nan durkushe ta kasa motsawa.

Ta gama alwalar tazo ta wuce ta ta tayar da sallar ta har ta gama ta zauna zaman jan carbin ta.

Ta gama lazimin ta ta fito ta sake wuce Wasila a zaune tazo ta tana daura girkin ta.

Wasila ta kwanto Kayan tsarabar da jibgo tana saukewa ta dubi Goggo tana Fadin

“Goggon don girman ALLAH ki yi mini Afuwa Wallahi na Gane kuskure na.

“Wai Ba ki ji bane ba? Nace Allah Ya yafe Mana sai me Kuma?”

“Na gode Goggo ga wannan.”

“A a fa kar ki fusata ni don ke kanki Zaki ji kunyar bani Wani Abu naki don kin San Naga bak’ar kasuwar da kike da idona don haka kwashe Kayan ki ni Kam ko yunwa zata kashe ni ai kin San sai dai na mutu da dai naci kayan ki me Ake da kayan da aka Samu ta hanyar Haram?”

“Wallahi Goggo ba Haram bane.”

“Me kika siyar kika same su? Ina ce bi Ake ta kanki ana biyan ki ? A wace mazhaba yazo da halaccin Hakan? To ki iya bakin ki kar ki fusata ni Wallahi.”

“Ki yi Hak’uri Goggo ba zan gaji da Baki Hak’uri ba yanzu ma nazo ne don mun daidai ta da wani zanyi Aure shine nace yazo gaban ku.

“Ni ce Mai daura Miki Aure ne da Zaki kawo min mutanen banza gaba na ? Ki Kai shi can bindawa dangin Uban ki ni Kam duk abinda kike so na barki da shi ba Duniya bace ? Wanda Bai zo cikin ta ba ma tana Jiran shi bare ke da kika zo kika zabi zaman karuwanci.

Wani Abu ya soki zuciyar wasila jin Goggo na danganta ta da kalamar karuwanci. To Amma meye sunan Abinda tayi in ba karuwancin ba? Aure tayi ne da Mazan da sukayi Abinda Sukayi? Ta Mike taja jiki Zuwa Dayan D’akin da maimuna take ciki Wanda Suma Nan sukayi tasu Rayuwar tana Jin Wani irin Bak’in ciki akan kalmar Goggo ta karuwanci da Kuma laulayin da ta Tara’s ana magana na maimuna. Yanzu har ishaq yayiwa yarinyar Nan ciki har ta fara laulayi? Sai taji hawaye suna bin idon ta HAWAYEn kishi HAWAYEn nadama da bak’in ciki.

<< Tana Kasa Tana Dabo 37Tana Kasa Tana Dabo 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×