Ya Mike cikin mutuwar jiki musamman da ya laluba aljihun shi ya ji Babu komai dama ya San Babu komai sabo da Yi ne wai kuturu da gatsine.
Hankalin sa yayi matukar tashi da ya tuna yanzu ne zai bayar da Abinda za a sarrafawa Yara na Karin kumallo shi kam dama baya Jira in dai yaran sun karya to Alhamdulillah bukata ta biya. K'aramin karfi ne dashi Amma Allah ya hada shi da mace Mai dogon Buri. Wasila Kam in son samu ne a wurin ta wannan Duniyar tayi Mata kad'an sai Kuma gashi Auren su Babu. . .