Skip to content
Part 41 of 58 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Idon sameer kyam akan tawul din da ke daure a kugun ta kafin ya ja kafafu ya nufe ta da karfi ya rungume ta ta fincike da karfi amma ya rike ta yana kai mata sumba tamkar mahaukaci.

Ta hankade shi ta kwace jikin ta ta gudu daki ya kuma biyo ta yana balle Riga idon shi jajir masifa na cin shi ita kam fareeda ta gane gaduwar su a ysnzu matsala CE komai na iya faruwa don haka tayi toilet ta murza key.

Kuka take tana hango Abdul ya dawo ya samu sameer me ye ba zai faru ba? Dole ta fito tana

Ba zan yafe maka ba wallahi matukar wani Abu ya samu aure na zan kuma fadi abinda kake kokarin yi min tinda baka tsoron Allah kai sameer nayi nadamat sannin ka a rayuwa ta wallahi.

Bakiyi nadama ba tukuna sai kinga abinda zanyi na rama wulakancin Da kuksyi min .

Ya Kara gyara kwanciyar sa a gadon ta yana fadin yana da sharadi Wanda zai gindaya mata.

“Wallahi karya kake Sameer Babu wani Shegen sharadi da zaka Kuma kindaya Mini Auren ka kuma na gama shi ba zan koma shi ba har Abadan ko kaine autan maza.

“Kice Zaki Bude muku kofofin balaki ke da Shegen mijin Naki don Babu ku Babu sauran zaman lafiya matukar Baki yarda ya sallamo mini ke .

“Ka tashi ka bar Gidan Nan tin kafin Miji na ya dawo ko kuma Wallahi yanzu na Kira shi yazo ya same ka Ka Kara Jan blanket Yana shafa fuskar shi Yana murmushi.

“Kira min shi dama Ina son mu Zauna dashi interview in fada mishi Bai san Auren KISAN WUTA kikayi dashi ba? In Bai sani ba sai na Sanar Dashi in Kuma Karbi takardar saki daga gareshi in Kuma ya kawo min taurin Kai Wallahi har batar Dashi zan iya ke kin Sani akan ki zan iya fatattake mutum ya koma toka.

Ta kalle shi cike da Mamakin shi akan wannan JANHURUN masifar da yake Shirin ballo Mata.

“Naji tashi ka tafi zamuyi magana bana son ya dawo ya same ka a nan ko Babu komai zaka Bata mini suna ne.

“Ai Babu inda zan tafi Farida tunda kika zama makaryaciya ai ba Zaki Kira ni ba. Ni ai nafi son mijin Naki yazo ya same ni don yaga Abinda bai zato ba Kuma in fada mishi in ba sakin ki yayi ba ba zai tab’a zama lafiya ba idan Bai kiyaye sharadi na ba Wallahi karshen sa ma na Zamo Ajalin sa Kinga inda kika gama takaba sai na dawo mayar da Auren mu tunda na lura duk yadda nake son ki kiyaye a wanye lafiya ba Zaki yarda ba.

Kwan Kwan Kwan.

Aka kwankwasa kofar da karfi inda Sukayi saurin kallon juna Amma sai taga Sameer ya Kara gyara kwanciyar shi maimakon ma ya tashi su nemi mafita tunda Bata ko shakka Abdullahi ne ya Dawo . Abinda yayi matukar tayar da hankalin Farida kenan wacce ta zurma Uban hijabi a guje ta nufi kofar fita.

Ta fice daga D’akin ta Kuma Bude kofar falon ta fito inda ta ke sauke Ganin ta a kan Basma wacce take Zaune akan kujerar falon tana murmushi.

Cikin faduwar gaba Mai tsanani Farida take kallon Basma Abinda ta kawowa Ranta ko dai Basma taga shigowar Sameer ne shiyasa ta shigo don tayi C I D ? Don Bata iya tuna Basma ta shigo sashin nata a tsayin Zaman ta a gidan tun fa Ranar da aka kira ta don baba Yusha U yayi musu nasiha . Amma sai gata a Yanzu.

Ta zauna tana Fadin

“Maman Najwa ya yaran ?

Basma tayi murmushi tana Fadin

“Lafiya Lau Amarya ya hanya? Dama cewa nayi bari Nazo Nayi Miki Sannu da hanya Kun Sha abroad.

“Nagode Sosai ai Kam dai Wallahi bari na kawo Miki Ruwa.

“Ke barshi Nagode sai kace dai wata bakuwa? Tun Dazu zan shigo ne har na fito sai Kuma naga kamar giccin mutum ya shigo Nan sai naja baya nace to ko Dan Uwan ki ne .

Wani irin matsiyacin Duka da Farida taji a zuciyar ta shi ya kusa Saka ta Suma . Ashe dai ba Lau Basma ta shigo ba da gaske tsegumi ya kawo ta .

“Kai Anya kuwa Nan kika ga ya shigo? Gaskiya Banga Wanda ya shigo ba don ni kwance ma nake sai da kika buga kofar na jiyo ki.

“Ayya Wallahi Nasha nan ya shigo wata Kil ido na ne ke gizo .

Farida ta kasa tankawa don ta San matukar matar Nan ta Gane Abinda yake lullube Bata ko shakka itace wacce zata fara tona Mata Asiri tinda Wanda yace baya son ka har Abada din baya son ka.

Basma ta Mike tana Fadin

“Allah ya huta gajiya Amarya dama Sannu da Zuwa nazo Miki don nasan shine zaman taren kuma don Allah Abinda ya wuce a baya to a bashi baya Babu Ruwan Allah da wane yayi min laifi matukar ka sani ka take sanin ka to zai Maka hisabi daidai da zunubin ka don Allah mu Yafi juna Kuma mu Rik’e juna da Amana .

“In Sha Allah Nagode Sosai Allah ya bamu ikon fita hakkin juna

Sukayi sallama Basma ta fita tana Leke Leke wai da gaske so take taga wata Alama da zata nuna Mata Wani ya shigo sashin Farida.

Tana fita sai ta Zauna a kofar sashin ta don ita da kanta taga shigowar Wani mutum ya shiga sashin Farida inda mamaki ya kamata in dai dan Uwan ta ne ai ba haka ya kamata yazo ba. Don haka ta Basu lokaci ko zai fito Amma sai taga Anja lokaci Amma Bai fito ba shine ta shiga sashin Farida da wannan manubar ta Kuma San Farida Rufe Mata tayi sai dai ko idan boye shi tayi.

Don haka ta kafa kujera tana son Ganin kwal Uwar daka

Farida da ta Raka Basma ta fice ta mayar da kofar ta Rufe tana dafe kirji.

“Idan matar Nan taga Sameer meye ba zai faru ba? .

Ta koma D’akin da sauri tana Fadin

“Don Allah ka tashi ka tafi in baka sani ba Wallahi anga Zuwan ka Gidan Nan Kuma ka sani Wallahi in baka ta shi ka tafi ba duk Abinda ya biyo bayan Hakan zan Fadi gaskiya tunda na nuna maka baka yarda ba.

Ya tashi zaune Yana kallon ta kafin yace

“Yanzu Ina muka tsaya da maganar mu? Shin Zaki yarda ki fito Nan da sati Daya? Wallahi idan kika wuce sati Daya zanzo na tayar da Balakin da zai kashe Mijin ki Ina jiran Kiran ki Nan da One week.

Ya Mike Yana balle botiran Rigar sa inda farida dai Bata tanka mishi ba ya Mike Yana fito da kudi Yana Mika Mata ta kawar da kanta.

“Karbi Mana ko kuwa kina son ce min bani da kudin Baki tunda an Gina irin wannan gidan an Saka ki ana Baki kyautar mota da fita kasashen waje?.

“Ni dai nafi bukatar ka tafi don Allah na fada maka ina bukatar kudi ne?

Ya ajiye Mata kudin tayi gaba tana dage labulen tagar inda ta hango Basma ta kafa kujera tana Dakon Ganin Mai shiga da Mai fita

Ta juyo tana nuna Mishi Basma tana fadin

“Kaga Abinda nake nuna maka kishiya ta taga zuwan ka Kuma wancan Zaman zaman tsegumi ne da son Lallai sai taga fitar ka don taji dadin watsa ni yanzu Nan Kuma sai kace min Sona kake Alhalin baka fahimtar Abinda nake son fahimtar da Kai. Me kake zato idan ta tabbatar da fitar ka a Yanzu,? Wane kalar sharri ne ba zata ja min ba tunda ba da Alheri take nufi na ba? Kana Sona ne kake ja min Abinda za a wulakanta ni ? .

Ya Dubi Basma wacce take Zaune dafa an akan kujera idon ta Kuma Kur a kan kofar Farida

Dole ya koma ya zauna Yana Fadin

“Ni Ina shakkar Wani ya ganni ne ? Ai nafi son a ganni ma saboda na fasa kwarya ayi Uwar watsi Kinga na kwato yancin da ke ce kike Shirin danne mini .

K’arar motar da ta shigo ce yasa gaban Farida ya Sara tayi saurin Duban agogo inda taga bakwai saura ta Kuma tabbatar da Abdullahi ne ya dawo don Lakocin Dawowar sa kenan .

Ta Mike tanna daga labulen tagar taga shine ya shigo da motar shi.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Sameer kaga Abinda kaja mini? Gashi Nan har mutumin Nan ya dawo ya same ka a Nan .

Ya Kara gyara zaman shi Babu wani Tsoro ko firgici Yana tab’a wayar shi.

Ta koma ga tagar inda taga Abdullahi ya fito daga motar Basma ta tashi da sauri tana karbar kayan da suke hannun sa don itace da girki . Don haka wannan Zaman Saka idon na Basma me Gemu ya kawo karshen sa don sashin ta Suka nufa .

Ta Sauke AJIYAR ZUCIYA tana fadin

“Ya SHIGA can tashi muje ka fita in dai kana nema min Zaman lafiya .

“Nifa ai in da na San inda Zaman lafiyar naki yake nine farkon Wanda zai tarwatsa shi .

Ya fada Yana mikewa Amma kafin su Kai ga kofar sukaji Amon sauti tafiya Wanda ya nuna Mata Abdullahi ne Dole suka yo Baya tana Kara Jin faduwar gaban ta.

“Kwan Kwan Kwan.

Aka kwankwasa kofar inda da ja Hannun Sameer suka baya ta kaishi har toilet din d’akin ta ta Rufe har da key kafin ta Dawo ta Bude kofar inda Mai Gemu ya Rungume ta Yana bata pick Yana hada tsinin hancin sa da nata .

“My dear BACCI kikayi ne?

“Kaina ne yayi Ciwo shiyasa nake Jin duk Babu Dadi.

“Ayya Kuma shine bani sanar Dani ba? Shirya muje hospital ko na samu baby ne? Don Allah ki bani baby my dear Mai irin fuskar ki .

“Ba sai munje Asibitin ba ko magani ma na samu ya Isa derling baby Kuma muyi ADDU AR Allah ya kawo Mai Alheri.

“Ameen ya Rabb my dear bari na samo Miki magani a pharmacy yanzu kar waccan Sarkin tsegumin ta ce na SHIGA hakkin ta.

Ya fada Yana sumbatar Bakin ta ya fice inda ta Bude Sameer suka fito motar Mai gemu na fita Shima ya fice kafin Farida ta sauke AJIYAR ZUCIYA tana Godewa Allah.

Fitar Sameer din Babu jumawa taga Basma ta leko tana kalle kalle ta Kuma Yi tsaye ta kasa komawa har sai da Mai gemu ya shigo kawo Mata magani Yana ta tarairayar ta ta nuna mishi da sauki fa Sosai Kuma kan ne kad’ai matsalar ta Shima da Tasha maganin zata samu relief .

Ya jima Yana Rungume da ita Yana nuna Mata soyayya da nuna Mata muhimancin ta a gareshi. Sai da ta tuna mishi Basma da ke Can tana Jiran shi kafin ya tafi Yana fadin zai Kira ta kafin ya kwanta.

Sameer Wanda ya tabbatar da Babu yadda za ayi ya iya Rayuwa ba tare da Farida ba. Domin kuwa ita kadai ce macen da ya gamsuwa da Samun nutsuwa a tare da ita Bai tabbatar da hakan ba sai yau da yazo gareta ya samu Abinda yake so. Don a haka a wannan Daren ya kasa runtsewa Babu Abinda yake bege sai fatan ace Farida tana gefen shi a irin wannan lokacin.

Da safe yayi Shirin wucewa pertercout ya Isa gidan su Hajiyar shi ta bukaci kudi Bai kawo komai a Ranshi ba ya tura Mata ta account yayi Mata sallama ya wuce ko Gidan Hajiyar Farida Bai je ba duk da Ya so Ganin Saddam da Hanan Amma ya wuce abin sa sai da ya sauka ne ya Kira Hajiyar Farida yana Bata Hak’uri akan wai Kiran gaggawa ya samu In da ya bukaci a hada shi da Saddam da Hanan sukayi ta mishi shirmen su Yana biye musu sama minti talatin Yana tare da yaran kafin yayi musu sallama suna bashi sakon sweet .

A Ranar da ya bar katsina a Ranar ne Kuma Hajiyar shi ta Kira Yar Uwar ta Asiya akan maganar auren Aisha inda suka Soma tsare tsaren su har Magana dai ta kankama Amma Sameer Bai San bikin da Ake ba don shi Yana can ma Yana jiran Kiran Farida ta fada mishi Abinda ta Yankee

Sati Daya daidai da tafiyar shi aka Daura Auren shi da Aisha Kuma a Ranar ne Farida ta kashe wayar ta don ma kar ya Kira ta ya Dame ta don zata je gida ne ta Gano Saddam da Hanan Rabon ta da su yau watanni UKU kenan don haka tayi musu tsaraba Sosai Abdullahi ya dauke ta a mota suka nufi gidan su

Har cikin gida Abdullahi ya shiga yayiwa Haj gaisuwar girmamawa ya Kuma Kai Mata tsarabar da ya Rukowa iyayen shi su Goggo Amu Matan baba isuhu kafin yayiwa Haj sallama Yana cewa Farida sai magaruba zaizo ya dauke ta su koma Gida

Ta biyo shi har kofar Gida tana Fadin

“To a Gaishe da su Goggo Amu sai ka dawo derling.

Ya Sumbaci bakin ta Yana Fadin

“Ki fa Shirya yau Babu bacci Yasin sai kin San yadda Zakiyi Dani.

“Sai na hadiye ka na huta derling.

Sukayi Dariya ya ja motar shi ya wuce

Ta dawo cikin Gidan tana tambayar Haj Ina SI Saddam da Hanan?

Haj tace

“Dazu Dazun Nan kuwa kanin Uban su Bello yazo ya dauke su wai Ashe an daurawa Uban su Aure da wannan Yar Uwar tashi Aisha shine Hajiyar su tace don Allah a kawo su Saddam din ayi Hidima tare da su shine na tattara Mata su na bashi kema duk da Baki tambaye Mijin ki ba kina iya zuwa ki Yi Mata Allah ya sanya Alheri tunda itama tazo Miki in yaso daga can sai ki Gano yaran Amma don allah ayi musu kara kar ace za a dauko su tunda Suma sunyi tasu Karar da Suka bar Mana su inda sun so tsiya fa ai da tuni sun karbe su tunda kikayi Auren ki .

Wani Abu ya soki zuciyar Farida Wanda taji idon ta Yana Neman fidda kwalla wai an daurawa Sameer Aure da Aisha? Zuciyar ta Tamkar zata tsinke saboda tashin hankali? Dama haka Sameer yaji da tayi nata Auren? Anya kuwa shi ba yayi Adalci ba ma da ya iya jurewa har tsayin watanni UKU? Sai taji tamkar ta tashi taje ta samu Aisha tayi ta Duka duk da Dama can ba son Aishar take ba musamman yadda take nunawa Sameer so ko a gaban Uba WA?.

Sai taji har shi Sameer din Bata kauna bare wata aisha can. Ba don taso ba ta ajewa Haj tsarabar ta ta Mike ta nufi gidan su Sameer Wanda ta samu cike da Yan Uwan su da Abokan Arziki ana ta Hidima. Yak’e kawai take ana Gaisawa da ita har ta shiga D’akin hajiya ta Gaishe ta tayi Mata fatan Alheri ita Kuma tayi ta Mata ADDU A. Ta kawo kudi da turare da sabulai masu yawa ta bawa Haj tana ta Godiya tana Saka Mata Albarka.

Ta Mike zata fice haj ke ce mata Khadija ta kwashi su Saddam sun tafi Amma in Sha Allah zuwa Gobe za a mayar da su .

“Lah Haj a barsu har a gama Hidima yaushe Rabon da agan su?.

Tayiwa Haj sallama ta fice Bata ko ganin gaban ta saboda tsananin kishi da Bakin ciki .

Da ta dawo gida ma daki ta wuce ta Soma kuka kukan da ita da kanta ba zata iya Cewa ga na meye ba. Amma dai koma meye Bai wuce Auren Sameer ba .

Haj ta Zuba Mata ido Lokacin da ta shigo D’akin ta Samu fuskar ta jage jage da hawaye don bata san lokacin ds Haj ta shigo ba sai dai ganin ta tayi tsaye a Kanta.

<< Tana Kasa Tana Dabo 40Tana Kasa Tana Dabo 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×