Skip to content
Part 48 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Gwaje gwajen likita ga Farida suka tabbatar mishi da cikin Farida ya Kuma Sanar wa Abdullahi .

Yayi FARIN CIKI Mai yawa har yayiwa likitan kyauta ta musamman.

Suka taho Yana Rungume da Salman wanda yayi BACCI a jikin shi . Yana tuk’i Yana Kara Godewa Allah da ya azurta shi da Auren Farida wacce yake so bakin Ranshi ga Kuma Albarkar Ya’yan da Allah ya Basu.

“Darling me kike so Nayi Miki ko na Baki? Kin gama min komai Farida ko akan Salman da kika Haifa min . Shiyasa aka hore mu da Auren Mata fiye da Daya. Kinga ita Basma ta bani Mata ke kuma kin fara bani Namiji ga Kuma Wanda yake cikin ki koma meye Ina godewa ALLAH da ya Bani ZURIA tsakanin ku da Basma .

Tunda aka Sanar da bayyanar cikin yake hidimtawa Farida tamkar zai kwanta tabi ta kan shi kome ya dauko Farida . Kullum Kuma Yana zaryar siyen kayan fruit don wannan karon kam da fruit tazo komai zata ci in ba shi ba zai dawo Amma fruit lafiya Lau don haka kullum zai shigo tare da su Kuma fridge din ta cike yake fal da kayan marmarin.

Basma ta Rik’e Baki cike da Tashin hankali Jin wai Farida ce ke laulayi. Ta Mike tana nufar sashin Farida tana Fadin

“Sannu maman Saddam Allah ya Kara lafiya Wallahi ban Sani ba sai Dazu yake fad’a mini nace ko za ayi Miki Wani Dan girki ne?

Farida ta kad’a kanta tana fadin

“Nagode Babu Abinda za ayi mini tunda ba cin komai nake ba .

“Ayya to Allah ya Kara lafiya ya Kuma Raba lafiya. Ni kuwa Shekaran jiya kamar naga shigowar baban Saddam Nan ko? Naso na tsaya mu Gaisa Amma Bai tsaya ba .

A Rude Farida ta dubi Basma tana Fadin

“A Ina kika ganshi? Ba Nan ya shigo ba .

“To ba Gane Amarya in ma ya shigo meye a cikin ido Banda Ruwa? Ai karya ne a Raba ku farida kin zama shi ya zama ke.

“Kar ki Kuma Yi min maganar mutumin Nan Basma bana so . Haba daga Ganin mutum kin ishe ni da Maganar sa sai akace Miki kullum Yana tare da ni ? Babu iko Babu zarafi ki shigo nan sai kin Yi min maganar shi? To Fadi Abinda yake Ranki don Allah.

“Kai Farida me yayi zafi haka ? Allah ya Baki Hak’uri ni Babu Abinda yake Raina illah kawai Ina son mutane masu kama Daya shine kawai Dalili don Naga kamar Saddam da Uban sa .

“To ba a Nan Zaki ke kawo min wannan maganar ba Mai kama da kina son Jin Wani Abu to bana so .

“Kiyi Hak’uri banyi da wata Niya ba .

Ta fice tana murmushi Abinda ya tabbatar wa Farida matar Nan akwai tsiyar da take Shirin kulla Mata akan wannan muguntar da take .

A wannan karon ma Abdullahi ya shiryawa Farida tafiya waje a duba ta ita da cikin ta Abinda ya matukar kone Ran Basma.

Cikin satin ya gama musu Shiri suka Wuce lass Vergarn don ya yarda da Asibitin Nan

Basma ta is gidan lawisa tana Fadin

“Lawisa sawun giwa fa ya take na Rakumi matar can ta Kuma yin ciki yanzu haka ma sun bar Nigeria suna lass Vergarn.

“Ni Kuma ba Haihuwar ta ce Abinda zan tambaye ki ba shin Yaya maganin malam zulk’e kuwa ? Ni har yanzu banji kince min ga sauyin da kika Gani ba sai ma Akasin da Ake ta samu ba su tsani juna ba sai ma kusanci da suke ta Samu.

“Mtsss lawisa ai ni Wallahi na dawo daga Rakiyar mutanen Nan Babu komai a Cikin Aikin su sai cuta da yaudara. Ni fa kaf magungunan malam zulk’e Wallahi Babu Abinda na Gani duk karya ce na haka kaina sakat Ina ta faman bud’ad’a Uban hayaki Amma tamkar Ina Kara musu soyayya. Ni Yanzu haka zan zauna kenan ? Duk in yarinyar can tayi ciki kudin da take ja kadai sai nayi shekara ban ci su daga Abdullahi ba? Ni kenan na zama Yar gadin Gida?.

“To kema dai kokarin sake Haihuwa Zakiyi in ma kin Saka Robar implants ne gara ki cire ta ko kema a kaiki lass Vergarn din Nan .

“Wallahi Babu wata Roba da na Saka lawisa Ina tsoron Wani Abu dai Wallahi don na Soma tantama.

“Lallai kuwa Ashe za ayi Babu ke Kinga Idan matar can ta Kuma haifar Namiji? Shikenan ta zama itace da gida . Ko a yanzu da take da Namiji Daya daidai yake da su Najwa a gado su Duka Biyun kuwa kason su su biyu shine nashi shi Daya Kinga ko da ba Namiji ta Kuma Haifa ba itace gaba Dake bare Kuma ace ta Kuma haifar Namiji shikenan ke Kam kin zama mabaraciya.

Wani irin matsiyacin firgici ya shigi Basma tabi lawisa da kallon Allah sarki Kuma kasa Cewa uffan don ta yarda da Abinda ta fada Mata kwarai da gaske.

“Tabdijan Amma kuwa kin kad’a min ganye lawisa ban tab’a wannan tunanin ba sai a yanzu. To Amma na San Abinda zanyi .

Tayiwa lawisa Rad’a a kunnen ta Suka kyalkyale da Dariya suna tafawa.

Wata Biyu cif da fitar Mai gemu da Farida suka dawo gida Farida tayi shar da ita ga cikin ta da ya tura ga Kuma Salman da yake ta Gudun shi ko Ina Yana Jin karfi irin na yaro Mai lafiya da k’iriniya.

A Ranar da suka Dawo Basma tana kwance kanwar ta labuda wacce Basma ta Kira tace tazo ta zauna Mata zaman jinya Bata da lafiya.

Abdullahi ya shigo suka gaisa da labuda ya Isa ga Basma ya same ta kwance Yana tambayar ta lafiya?

Ta tashi Zaune tana Runtse idanun ta take Fadin

“Wallahi bani da lafiya tunda kuka tafi nake kwance Ciwon idanu bana ko son na Bude idon idan iska ya shiga .

“Subuhanallahi kuma kika zauna da Ciwo Baki sanar min ba?.

“Ta Yaya zan sanar da Kai Alhalin na San wata marar lafiya gareka? Na dai je Asibitin ido sun Rubuta mini magani Kuma sunce idan maganin baiyi ba Aiki za ayi mini ga takardar Nan na karbi Maganin nace in ka dawo zaka tura musu kud’in.

Ta Soma laluben takardar idon ta a Rufe har ta jawo takardar ta Mika mishi.

Ya karba Yana Dubawa ya Kuma duba magungunan kafin ya duba account din da ke kasa a Rubuce ya tura kudin Bai damu Da yawan kud’in ba.

“Na Tura musu kud’in idan har kikayi amfani da maganin Baki ji yayi ba sai mu wuce lass Vergarn suna da bangaren ido kuma likitocin su sun kware matuka Amma kiyi amfani da magungunan muga ci gaban da za a Samu.

Ya fita Yana fadin idan taji ba yadda take ba ta Yi mishi magana.

Yana fita Basma ta Kira labuda tana Fadin

“Ke jeki Maza wurin Hamza kice an tura kudin maganin ya fidda nashi ga account Dina Nan ya tura min sauran.

Ta fada tana dafe idon wai Bata son iska ya shiga.

Labuda ta fice Basma ita Kuma ta Bude idon ta Ras tana Dariya tana Fadin

“Ai Kuma shikenan ni kaka ta ta yanke Sakar ta na Bude Asusun da zan ja nawa kud’in.

Tana Nan kwance Rik’e da waya taji shigowar alert Hamza ya tura Mata kudin ta Duka.

A Ranar Nan wurinta Abdullahi yake don haka suka shigo shi da Farida wacce take gaishe da Basma tana mata ya jiki.

Idon Basma a Runtse take Amsawa inda Farida take kallon ta da Jin Lallai akwai makirci a cikin wannan manubar.

Tayi Mata fatan Alheri ta Mike ta fice

Itama Basma Abdullahi ya shiga hidimar ta da ciwon ta Yana kuma kashe kudi Wanda mafi yawa yaudara ce Asusun Basma suke tafiya ba tare da ya Sani ba.

Takardun magani na bogi Ake ta Rubutawa Basma na karbar kud’in ta siyi Dan magani Wanda Bai wuce na Dubu Biyu ko uku ba wani ma maimai take cikin wands take da su ne take daukowa.

Cikin farida na girma ana Mata Hidimar Haihuwa wacce Ake ta Tara kayan baby don an duba musu baby Shima Namiji ne don haka Ake ta tara mishi kayan welcome.

A Ranar da farida ta Haihu a Ranar ne Kuma Basma ta bijiro da son su fita lass Vergarn wai nan dai duk Aikin Banza suke . Ta Yi Hakan ne don ta San Abdullahi ba zai yarda ya bar Nigeria a yanzu ba Yana murnar Samun baby boy don haka sai dai ya shirya musu tafiya ita da labuda. Dama haka take so shiyasa tace ayi tafiyar yanzu ta San ba zai je ba .

Ai kuwa tuni suka wuce lass Vergarn amma Basma Bata yarda shiga Asibitin ba sai dai ayi lissafin karya a tura wa Abdullahi shi Kuma ya tura Mata kud’in

Labuda bata San Cewa akwai makirci a cikin ciwon yayar tata ba sai da suka Sauka a lass Vergarn taga ta ware idon ta tar tana kallon komai dai dai sai mamaki ya kamata har ta dubi Basma tana Fad’in

“Anty ? Wai zuwan mu Nan ne idon ya bude ko kuwa dai .

“To Uwar Sharri wannan Maganin ne da nake sakawa naji a Nan Babu iskan da in ya shiga zan Wahala. Bana son Saka ido bana son binbini kinji na fada Miki ki kame Bakin ki .

Haka labuda tabi Basma da Kallon tana tunanin akwai makirci a cikin Ciwon Nan wankiya ce kawai Ake son Yi.

Sati Biyu ana wankar Abdullahi kullum da kud’in da za a ce mishi ya tura tun daga na magani Zuwa na Aiki Wanda tace anyi mata kala takwas Banda Gwaje gwajen da hotunan idon.

Duk Abinda tace zai tura Mata kudi ita Kuma tana dannewa sai da sukayi sati uku inda Abdullahi ya Gaji da tura kudin yace zai bi su yaga irin ci Gaban da Ake Samu .

Da sauri Basma tace an tsayar da shi tana Fadin

Ai an sallame su gasu Nan Zuwa yau in Sha Allah.

Haka kuwa akayi Basma ta hado kan Ahalin ta Najwa da Nabeela sai labuda Kuma duka Mai gemu ne ya biya musu komai .

A Ranar da suka Sauka garin katsina Basma sanye da katon gilashin ta a ido ta na dafe da Najwa wacce take mata jagora.

Suna Isa gida Farida ta iso tana mata barka da Arziki tare da fatan allah yasa anyi Aiki cikin nasara. Ta Kuma Dora Mata jariri Wanda yaci sunan Sulaiman tana fad’in

“Ga Sulaiman Nan Allah ya kaddara zai zo Duniya Baki Dora ido akan shi ba .

Basma ta Soma shafa shi tana Fadin

“Allah sarki Sulaiman Allah ya Raya ka da Imani in Sha Allah ai da yake Aikin yayi nasara in Sha Allah Nan da kwanaki kad’an za a cire Abinda aka Rufe idon da shi in Sha Allah zanga komai.

Wani Bak’in ciki ya ishi Basma Jin Maza Biyu Farida ta mallaka ita Kuma Bata mata ne Wanda Suka linka ta har sau buyu.

Kudin da Basma ta samu ba k’anana bane shiyasa ta Hak’ura da wankar Abdullahi ta cire bandanar da ta like idon ta da ita ta Kuma Dawo warai idon ta fess tana ganin komai da kowa ana ta Mata barka da Arziki. Sai Kuma taga a yanzu fa zama Bai ganta ba Domin kuwa a yanzu ne garnakiki yake tunkarar ta na mamayar Gidan Da Farida ta Yi mata . Ta tabbata dai Babu wani Abu da Zatayi a yanzu Wanda zatayi nasara akan Farida da Abdullahi shine sai Abu Daya wato kawar da Abdullahi daga Doron Duniya hakan shine kawai zai Bata Damar fadawa Farida Abinda yake ZUCIYAR ta a game da ita Kuma ta Bata zabi cikin Biyu ta zabi Daya Amma ta Yaya Hakan zata yuwu?.

<< Tana Kasa Tana Dabo 47Tana Kasa Tana Dabo 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×