Skip to content
Part 4 of 12 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Zainab da yusra suka taso makaranta Amma suka Tara’s da gidan nasu a kulle.

Suka Soma dukan kofar Amma shiru Babu wani motsi. Zainab da take itace k’arama Mai Shekaru shida sai ta fara kuka don yunwa take ji ga Rana tana kwallar su.

Yusra Mai Shekaru Tara itace ta kama Hannun Zainab suka koma gefen gidan Suka zauna itama yinwar take ji Amma da yake tafi Zainab wayo ita batayi kuka ba Amma kallo Daya Zakayi Mata ka San a Dame take itama in aka wuce wannan galan din dab take da yin Kukan.

Zaman su Babu jimawa sai ga sagir ya K’araso Yana hango kannen nashi a rabe tamkar wasu almajirai…..

“Yusra me kuke a waje ne Baku shiga gida ba?

“Kulle gidan yake munyi ta bugawa ba a Bude ba.

Ya nufi kofar gidan Yana fadin “Kila bacci mama take Bata ji ba.

Ya Soma buga kofar Amma sai yaga jamlock din ya Ratsa Alamar Rufewa akayi.

“Bata Nan kuwa mama to Ina ta tafi? Ya juyo Yana Fadin,

“Yusra shiga gidan Anty kiji ko Mami ta aje Mana key din.

Ta Mike ta shuga gidan ta fito tace Bata bayar ba.

Kukan Zainab ya sa ya juyo Yana fadin, “Baby ya akayi ne?

“Yaya yunwa nake ji ni.

Ta fada da Kara sakin Kukan.

Ya kwanto jakar makarantar sa wacce ya Sako dankalin Hausa soyayye Wanda zai Wuce gareji da shi a matsayin Abincin Rana ya mikawa Zainab ita da yusra suka lashe tas duk da koshi sukayi ba Amma dai Zainab tayi shiru sai sude hannu take Alamar Bata koshi ba.

Yana son ya tafi gareji kar ya makara Amma Dole yabi zaman jiran tsammanin jiran Uwar su wasila wacce ke can tana b’are b’aren samun kudin da su Alhajin naira suka zube Mata don haka ta jiyo gida Bata ko k’arasa shigar da kayan filawar ta ba ta tare Napep cike da murna ta nufo Gida.

Sai ta manta da kayan da suke jikin ta Wanda murnar da take ciki ne ya Hana ta tuna hijabin da ta mayar a Jaka sai Dan yalolon gyale.

Har kofar gidan Mai Napep ya dire ta fito tana Sallamar shi kudin shi inda ta hango su yusra zaune a gefe.

Sagir ne ya Kalli Uwar tasu da kayan da suke jikinn ta Wani Abu ya tab’a zuciyar shi inda Zainab Kuma ta ido da gudu tana Bude mazubin da taga Uwar ta aje Wanda yake dauke da sauran boga da shawarma ta kuwa zaro boga Daya tana cin don bil hakki yunwa take ji.

“Mama Ina kikaje da wannan kayan ? Dubi fa har ana ganin Nan. Sai a Nan ta tuna da kayan da suke jikin ta….

“Kai ya isheka kaji ko? Tuhuma ta kake ko kuwa uban ka ne ya baka Aikin Saka mini ido? Kayan da zan Saka ma sai an nuna mini ko kuwa Yaya?

Yayi shiru Bai Kuma tankawa ba don sai tijara take sauke mishi.

“Kiyi Hak’uri in Ranki ya Baci Naga kamar Hakan Bai kamata ba mace Mai mutunci Bata barin ana kallon jikin ta.

“Da kyau nice marar matuncin yau ko?

“A a don Allah kiyi Hak’uri.

Ta figi sauran kayan ta ta nufi kofar gidan tana Budewa suka shiga ciki ya nufi D’akin shi ya dauko kayan gareji ya fito ko Ruwa Bai Sha ba ya zo d’akin wasila wacce ta sauya kayan jikin ta tana Lissafin kudin ta Amma Yana shigowa ta mayar a Jaka.

Mama na tafi gareji, Bata ko Ranka mishi ba saboda ya kaita wuya, Shi Kuma ADDU AR ta yaso ta Neman dacewa Amma haka ya fice Ranshi Babu Dadi Na irin kayan da ya Gani a jikin Uwar shi.

Ta jawo sauran kayan filawar ta tana fad’in, “Zee zee kin koshi ko na Kara Miki Ta kada kanta Alamar bata koshi ba.

“Karbi d’ari biyar yusra siyo muku yuoght kuci wannan shawarma.

Da sauri yusra ta karbi kudin ta siyo suka ci snacks din Sosai suka Sha Ruwa suka yi shirin islamiya

Alhajin naira kuwa da yake Mayen Mata ne tunda wasila ta tafi yake zalamar yadda za ayi su hadu a yau. Don haka shi ya Riga kowa tashi ana gama sallar la asar ya wuce motar shi don yau din yake son lashe wasila da Abunda ya Kira soyayya

Ya shiga motar shi ya tashe ta Yana jawo wayar shi wacce ya Saka nomber wasila don haka ya auna mata Kira..

Wasila da ta jawo jakar ta ta fito da kudin ta tana Lissafin Abinda Zatayi da su Wanda Kaya ne kawai take da burin siye dangin sutura don tana Jin haushin makociyar ta da ke da Kaya na kece Raini har tana Fadin ana Mata homa da barazana don haka sutura Zata shiga central market ta Gallo Kaya na garari don ta Kara zama done.

Wayar ta ta dauki tsuwwa ta jawo ta da sauri tana Dubawa bakuwar lamba ce inda taji a Ranta Daya Daga cikin Wanda Suka karbi lambar ne suke Kira, Ta dauka da sauri Amma batayi magana ba.

“Ranki ya Dade Haj Mai kayan Dadi da girman kujerar ki.

Alhajin naira ya fada da salon bariki wacce ta nuna shi a gogagge a fannin.

“Wa ke magana? Wasila ta fada da wani sauti Wanda ta kawata murya dashi.

“Haba Ranki ya Dade Alhajin naira ne Wanda Baya jin wuyar saukewa mace tulin Nairori matukar zata bayar da gishi a Bata Manda.

A take wasila ta Gane shi ta saki murmushi har ya jiyo tace, “Ayya sorry Alhajin naira na Gane to ya kake?

“Yadda nake fa ai sai sannu don kin gama dama min lissafi mafita kawai nake nema a gareki Yaya Zakiyi Dani baby?

“Duk yadda kake so Alhaji na ai haka za ayi ko kuwa?.

“To gaskiya Ina son Ganin ki Yaya za ayi? Don tunda kika baro majalisar Nan na kasa gane kaina ke nake Gani da na Rufe ido na.

“Uhum to ai inda zamu hadun ne.

“Fada min in da zan zo na dauke ki Babu matsala ni wuri na daga nan har zaila zan iya zuwa bakiji ance garin masoyi baya Nisa ba.

Yusra da suke shirin makaranta ta Zubawa Uwar ta ta Ido tana son jin abban su ne yau take wa magana a Hankali?.

Ta juyo don jin idon yusra akan ta ta wuce Uwar daki tana Fadin

“Kazo bakin sabon titi kusa da Sauki venture sai mu Hadu.

“Ok to Gani Nan Zuwa gimbiya.

Ta katse wayar ta na nufar waje don sake sabon wanka inda yusra da Zainab zasu fice makaranta tayi maza ta tsayar da su tana fadin.

“Ke ku dawo yusra ku bar zuwa makarantar Nan zanje na Dawo ku Jira min gidan.

Yaran suka dawo zee zee na Fadin “Mama ba Zakiyi tuwo ba a yau ? Ta juyo inda ta tuna da garin da ishaq ya aje Mata Wanda ta tabbatar shi zee zee ta Gani.

“Bari na hada Miki wuta yusra kiyi Miku tuwo ai kin ga yadda nakeyi ko?

Da wata irin murna irin ta yaron da zaiyi girki yusra ta amsa da ta iya Alhalin ko hada wuta Bata iya ba itama ta San Babu Abinda yusra ta iya Amma a haka ta hada Mata wuta ta Dora Ruwa a tukunya ta Bata Aikin tankade garin ita Kuma ta shige Bandakin tana faman darzar jiki tamkar Mai Shirin sauya fata.

Ta gama Shirin ta tsab cikin shiga Mai daukar hankali Amma sai ta zurma hijabin ta ta fito taga yadda yusra take tankaden duk ta watsar da garin Amma da yake hankalin ta ya tafi ga Rudin shaidan sai tace da yusra idan tayi Rude sai ya dahu Ake zuba garin a tuka Shima sai ya sulala suke kwashewa.

Yusra tace, “Ai naga yadda kikeyi Amma ban iya wanke tsakin ba.

“Zuba shi ma haka Nan ai anyi Amma ki motsa Sosai kar yayi kullutu.

Ta fice Bata tsaya jiran Amsar yusra ba.

Sai da ta fita bakin Sauki venture ta hango motar Alhajin naira wata mashahuriyar mota ta garari.

Ta matsa don sai auna Mata Kira yake ya bude Mata motar ta shiga yaja suka wuce hotel din da ya kama d’aki. ISHAQ ya iso gida ana dab da Kiran sallar magaruba inda ya iske yusra a gaban murhu tana ta banka Wuta don tuni akayi rude ko minti Sha Biyar ba a Rufa ba Kuma aka auna garin aka tuka duk da dai Bai tuku ba Kuma yayi Abinda Ake Gudun wato kullutu.

“Abba yau ni zanyi Mana tuwo har na gama Miya kawai zan Dora. Yayi tsaye cike da Mamaki Yana kallon yusra kafin yace, “Kice akwai kwamacala yusra kin taba yin tuwon dama? Ina mamar taku da ta bar Miki wannan Aikin?

“Ta dai fita Amma ban San inda taje Amma fa ban taba yin girki ba sai yau zo ka Gani a kwashe haka?

Ta fada tana Bude tukunyar tuwon inda yayi Arba da garin duk ya nade Bai tuku ba yayi kurnu.

“Yayi Mana yusra mayar ki Rufe.

Ya wuce d’aki Yana Jin Bak’in cikin yadda ya hada kud’in garin Nan da sagir ya bayar Amma Kuma ya tabbatar da wancan tuwon ba zai cuwu ba asara zai zama saboda mugunta Ina yusra Ina Aikin girki?

Yana Daki Yana Aikin Saka maballi don yau ya samu Aikin Dunkin Wanda aka biya kudi don na sauri ne gobe gobe Ake son shi na daurin Aure ne shiyasa ya gama maballi kawai za a Saka.

Yana cikin Aikin yusra ta shigo tana Fadin, “Abba zo kaga yadda tuwon yakeyi da na zuba a cikin flasks sai yayi ta kwantawa Yana Ruwa Ruwa.

Ya Mike don ya San Dole dama za a zo ga Hakan.

Ya Zubawa tuwon ido Mai kama da shasshaka don ya gama narkewa Yana fidda Ruwa tamkar tsari. Ya Gane danyen tuwo ne Dole sai dai Akai tsari.

“Kwashe shi a haka ki ajiyewa mamar ku ai ta San za ayi Hakan ta bar Miki Aikin. Zo ku siyo Wani Abu ku ci.

Ya wuce bayan ya bawa yusra d’ari biyar ta kwashe tuwon ta jera a kofar D’akin wasila suka siyo taliya da manja suka ci ita da zee zee .

Wasila Kam suna Isa hotel din Alhajin naira ya bude Mata ido da barikin shi wacce ta Bata Mamaki inda yake fada Mata mijin baya Bata matsala kuwa? Tayi Mamakin yadda ya San tana da miji don ta so ta lullube mishi tana da Aure Amma da ta ce ya akayi ya San tana da miji ? Sai ta Sha mamaki don yace Mata Yana Gane mace tana da miji ne a tsayen ta ko Bai tab’a ta ba kuwa.

“Miji na baya iya Rik’e ni shiyasa na mike don na nemi kudi na na biyawa kaina bukata don haka Babu wata matsala da zai kawo min kar wannan ya Dame ka in baya iyawa sai ya aje Mai iyawa ya dauka…

Wannan tabbaccin da wasila ta bayar shi ya k’arawa Alhajin naira karfin gwiwa aka shiga bariki da sheke Aya aka ketawa Ubangiji haddi aka ketawa Aure haddi aka Kuma ketawa sagir da yusra da Zainab haddi sai Kuma Uban su Mai girman hakki

Sai karfe Taran Dare Alhajin naira ya sallami wasila da tarin kudade har Dubu d’ari da Hamsin ya Kuma kawo ta har in da ya dauke ta ya aje Yana fadin zai Kira ta.

ISHAQ Yana zaune tare da sagir da su yusra wasila ta shigo Gidan Kai tsaye ta wuce D’akin ta tana sauya Kaya inda ta Yi Arba da tuwon yusra Wanda ta tabbatar dama haka zata faru Amma Bata bi ta kan shi ba don tafe take da take away din farfesun kaza da fresh milk a Jakarta don haka Ruwan zafi kawai take bukatar watsswa don haka sai ta jona kittle a wutar NEPA yayi zafi ta juye ta fice Bandakin tayi wanka tana Jin wata irin gajiya da Bata taba Jin irin ta ba inda ta Gane ba a wofi zata ci Dubu d’ari da Hamsin ba. Tana fitowa ta daura alwala ta wuce daki Bata Cewa ishaq ci kanka ba bare su sagir da yusra don Zainab tayi bacci tuni

Tana gama sallar ta jawo take away din ta ta Soma cizgar Naman kaza ta gama ta kora da fresh milk ta Mike a gado tana kashe fitila don gajiya ce fal a tare da ita.

*****

Washe gari ishaq ya fice Aikin shi don Akwai garin masara akwai komai don kilo biyar ya siyo yusra ta lalata Daya sauran Kuma sai ta Dora in Kuma taso ta baiwa yusrar ta lalata sauran.

Dole ta Kuma Dora Wani girkin tayi tuwo don na yusra dai Dole ta Kai tsari . Tana gamawa kuwa ta fice kasuwa ta fara Gallo wayar android Mai Daraja ta farko kafin ta wuce shagon atamfa da lass ta Gallo Kaya na garari ta wuce ta Kai dunki kafin ta Dawo gida tana tunanin irin fantamawar da zatayi a wannan dan tsakanin da Duniya ta tuna da tana Raye.

Abinda yayi matukar bawa ishaq mamaki shine yanzu wasila Bata Wani bi ta kanshi akan ya bayar da kudi akan Abun Kari . Komai ya kawo zata karba ta sarrrafa ta bawa yaran Amma fa ita babu ita a ciki sai Abinda take so take ci. Haka Kuma karatun littatafan ta na Hausa in tanayi sai ka dauka Bata gidan inda take ta samun idea ta yadda mata suka waye suke yadda suke so a yanzu. Haka ma a wayar ta idan ta kutsa social media tana samun abubuwa da yawa. Kuma har yau din Bata yarda ishaq ko sagir Wani ya ga wayar ta ba don ta San da sun Gani akwai matsala don haka a boye take yin BLACK MARKET din ta. Don da gaske take son ta wataya yadda take so Babu wani shamaki tunda ta Gane a wannan Rayuwar duk Mai son Auren Duniya matukar da gaske son Auren ta to zai Aure ta ne da irin kokarin Da zai cika mishi mafarkan shi na gaskiya.

<< Tana Kasa Tana Dabo 4Tana Kasa Tana Dabo 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×