Skip to content
Part 56 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

A Ranar da Abdullahi ya tafi Sulaiman yasha kuka Farida nata Rarrashin sa Amma yaki Shiru ga maganganun Basma da suke ta Mata yawo aka. ta kasa manta mugun Alwashin Basma Wanda ta tabbatar da Abinda ta fada ne take nufi Amma ta Riga ta Cewa ALLAH dukkan Abinda take nufi in na ba Alheri bane Allah ya watsa Shirin ta ya Kuma mayar Mata da koma meye a kanta .

Salman Yana Rungume da Sulaiman Yana fadin

“Yi Shiru Sulaiman Daddy yanzu zai dawo kana zuwa wurin Daddy?

Tana kallon yaran da Abinda ya Bata Mamaki Domin kuwa tuni Sulaiman yayi shiru Salman Yana tambayar shi Yana zuwa wurin Daddy? Yace mishi Eh shine yake Cewa ya bari zai Kai shi sai Kuma gashi yayi shiru har Yana bashi sweet. Tana kallon su da tabbatar wa kanta jini yafi k’arfin wasa .

Tuni suka hau wasan su Suka manta da komai sai Zuwa dare ne Abdullahi ya Kira wayar Basma Amma Bata dauka ba sai ya Kira ta Farida ita Kam ta dauka don ta Kira taji a Rufe ta San Basu sauka ba ko Kuma sun sauka Yana hutawa dai. sai gashi ya kira ta dauka tana tambayar sun sauka? Ya amsa da sun sauka Ina Salman da Sulaiman.? Tace Sulaiman dai yayi bacci sai Salman don haka ta bawa Salman wayar Yana Fadin

“Daddy ka taho ? Sulaiman Yana kuka fa zai zo wurin ka na bashi sweet yay Shiru .

“Yauwa babban Yaya haka nake so kake Rarrashin sa idan Yana kuka kaji ko? .

“To Daddy ka taho ?.

“A a ban taho ba Salman Amma maman ka lami zata kawo ku wuri na next week in Sha Allah ka bawa Sulaiman hak’uri kaji ko?.

“To Daddy muma jirgin zamu shigo?.

“Sosai kuwa jirgi zaku shigo.

“Har da Mami zamu taho?.

“A a Banda ita Kai da Sulaiman da mama lami.

“To Daddy ka aje Mana sweet.

Sun Dade da yaron suna Magana Yana biye mishi kafin Farida ta amsa tana Fadin

“Derling ka huta zamuyi magana da safe in ka biye ta wannan zaka kwana kanayi .

“Nima zan kwana Ina biye mishi Ina Sulaiman Salman yace yayi kuka?.

“Kuka kuwa Sosai a Dole sai an kawo shi wurin ka duk Rarrashin Duniya yaki saurare na Amma abin Mamaki Salman Yana cewa zai kawo shi wurin ka yayi shiru har da bashi sweet kafin ya manta da kukan .

“To Dan Uwa Wasa ne Darling? Ai jini yafi k’arfin wasa mune muke mayar da Yan Uwan taka Banza mu Kuma dauki kiyayya mi dorawa dan Uwa Alhalin mun banzatae da zumunci da yan Uwan mu ba Dole Duniya ke Rikicewa ba? Watsi da Zumunci na Daya Daga Cikin Abinda ya Hana Duniya zama lafiya.

“Gaskiya ne Darling Allah ya ganar da Al Ummar musulmi girman zumunci.

Sukayi sallama ya sake Kiran wayar Basma Amma Bata dauka ba sai ya tura Mata text na sun sauka lafiya Kuma Yana tambayar lafiyar su ita da su Najwa da Nabeela.

Taja tsaki Lokacin da take karanta text.

Ta Mike tana daukar Jakarta ta fice daga gidan ta nufi gidan lawisa.

Lawisa ta tarbe ta tana fadin

“Kai matar Alh Abdullahi Mai gidan Nairori Yaya mutanen Gidan suka kwana Suka tashi? .

“Uhum ai lawisa an kusa Zuwa wurin Wallahi wai kinji wulakancin da Abdullahi yayi mini? .

Lawisa ta Dube ta tana fadin

“Sai kin fada Allah dai yasa ba kiran ki yayi da sunan Farida ba don na San duk Duniya idan Akwai Abinda kika tsana to sunan Farida ne .

“Ai wulakancin ya wuce wannan Wai fa kin San Ya’yan Farida ya biyawa makka a jirgin yawo ma?.

Lawisa ta kame Baki tana zato idanu .

“Da gaske ko kuwa mafarki kikayi ?.

“Ke fa kinji tsiyar ki iskanci in mafarkin ne zan Wani daga kaina? Da gaske yake wai ba zai iya jure Rashin su har na tsayin Lokaci ba shine wai zai biyawa Uwar su jirgin yawo su tafi tare nice nace ban yarda ba shine ya sauya da yayar shi lami.

“Kuma ke kika yarda?

Cewar Lawisa da take son Jin kanun Labaran.

“Ba Dole na yarda ba tunda na kasa yadda zan Hana abin? Na ga dai ga Najwa ga Nabeela Babu wacce ta tab’a ketare k’asa Amma su za a kaisu Saudi Arabia don in sun dawo yaji dadin sabon wulakancin Kiran su da alhazai ko? .

“To gaskiya sai kin San Abinda kike ciki don ya gama nunawa Duniya Cewar Ya’ya Maza sune Wanda yake so ba Mata ba tunda in Adalci za ayi ai ya hade har da su Najwa da Nabeela a tafi ba Wai ya ware Ya’yan so ba.

“Haba lawisa ai in yasan wata Bai San wata ba tuni nayiwa tufkar hanci don tunda ya Fara da wannan wulakancin in na barshi Nan Gaba ma Zai iya Cewa Salman da Sulaiman sune gaba da su Najwa to na kawo karshen komai Nan da Dan Taki kad’an Zaki ji Wani Abu inda zan fiddo wulakanci Mai kalar Ruwan zaiba Wallahi ai na San komai shiru kawai Nayi to nayi ta yanke ta gundule.

“Ban Gane ba? Kamar Yaya to?.

Basma tayiwa lawisa Rad’a a kunne tana kyalkyala Dariya.

Lawisa ta Dube ta fuska Babu sassauci tana Fadin.

“Kina da Hankali kuwa Basma? Wallahi kinyi kuskure ba haka akeyi ba wannan Hukuncin yayi tsauri da yawa Baki Gudun Abinda zai faru?.

“Wallahi duk ma Abinda zai faru sai dai ya faru lawisa ana mini wulakanci irin haka zan Zuba idanu? Ai ni Wallahi Hakan da nayi shine kawai mafita in yaso a mutu har liman in yaso sai a Rasa Mai yiwa kowa sallah Wallahi Yana musu haka tun yanzu kika San ko Yana can Yana Siya musu share a bankuna duk Yan kudaden su kare garesu ni Kuma Ina Nan Baki sake?.

“Gaskiya Basma wallahi tallahi ban ji Dadin Abinda kikayi ba. Ba haka naso kiyi ba . Ina laifin ace kin sace passport din ko kin Kona ? Amma wannan Abinda da kikayi ai Babu wata Riba a cikin yin sa sai faduwa tunda ko ba komai yanzu in akace Babu shi sunan ki bazawara kin San Wanda Zaki fadawa ? Kuma don ka Saka kishiya kuka ai bakayiwa kanka Silar kuka ba tunda yanzu kema Ya’yan ki sun zama marayu Kuma Abinda Baki son shi zai faru Ya’yan Farida sune da kaso Hudu ke Kuma Biyu kinga ko a Nan kinjawa kanki Wani Bak’in cikin Ina laifin ma ki tsaya a manne idanu kina wankar kudi da sunan magani ?.

“Ke lawisa banji Ina nadamar Hakan ba Wallahi tunda na Gane alkiblar da Mutumin Nan yake Kallo . Aka ce Miki zan yarda ayi kasafin gadon yadda kike zato ne? Ai wannan shine Sirrin da zan bankado in ta fahimce ni kalas in Kuma Bata fahimta ba mu ci gaba da istigifari Kawai.

Lawisa ta kame Baki tana kallon Basma wacce take jawo wayar ta da take ta Kara ta Duba sai ta ga Abdullahi ne ta mayar ta a Jaka tana Fadin

“Ai Kuma na gama magana da Kai Kai Kam daga can ba zaka dawo Nigeria ba ma bare a Gane Akwai Wani BOYAYYEN MAKIRCI ai kayi Arziki ma da za a binne ka a garin ma Aikin Allah wai gobarar titi a jos.

Lawisa ta bi ta da kallo tana Fadin

“Gaskiya kinyi Nisa in ma Wani ya Baki wannan shawarar Basma Wallahi Bai Baki ta kirki ba .

“Babu ma Wanda ya bani ni na samawa kaina mafita lawisa Mai d’aki fa shi ya San inda yake mishi yoyo ni na San matsala ta don haka barni kawai kiga yadda za ayi ai ban fito ba sai da na shirya lawisa ke dai barni kawai ni naga mafita ta In ke Baki Gani ba .

Lawisa kam Tasha Mamaki matuka Gaya akan Basma da muguntar da ta danawa mijin ta Wanda take cika bakin tana so har ta ke fatan sauya halitta don ta burge shi Amma yau ga Abinda tayi mishi ?.

A yau dai Kam Babu wani armashi a zuwan da Rabuwar don mamaki Kam ya kasa barin lawisa.

Kwana biyu ta isar su Abdullahi a birnin Riyad Wanda har yanzu Basma Taki daga Kiran shi inda Kuma yake Shan fira tsakanin shi da Salman da Sulaiman har yana Kiran Farida Vedio call Yana kallon yaran suna kallon shi su jima suna Magana kafin ya koma ga Farida wacce yake tambayar Basma kuwa lafiya take da yake ta Kira Bata dauka? Ta kan ce mishi lafiya Lau take wata Kil dai fushi take har yanzu tunda a Ranar ma sai da ta Doki Nabeela wai kawai don ta dauki Sulaiman.

Yayi murmushi Yana Fadin

“Na Kira ta na tura mats text Amma har yanzu Babu Kira Babu replay Amma zan Kuma kiran ta .

A Ranar da suke da kwana UKU ne garba ya Kira Farida Yana fada Mata Abdullahi Babu lafiya har Yana Asibitin Riyad wai yaci Wani Abu da aka zuba guba a ciki.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un .

“Yaya yake garba ? Wane hali yake ciki? Farida ta jera mishi tambayoyin a Jere.

“Ki kwantar da hankalin ki da sauki tunda sunyi mishi Allurar da ya Amayar da Abinda yaci din sai dai ance gubar tayi mishi illa da yawa ne har ta tab’a wasu sashi na cikin sa Amma in Sha Allah za ayi nasara ADDU A dai yake bukata.

“La haula Wala kuwwa ta illah billah garba don Allah hada ni da shi idan zai iya magana Ina son naji muryar shi .

“To a yanzu dai baya iya magana gaskiya Kuma anyi mishi Allurar da ta Saka shi bacci Yana bacci Amma in Sha Allah da ya farka zan kira na hada ku .

Basma tana ganin Kiran wayar da bakuwar lamba Amma bata dauka ba ta watsar sai da garba ya tura Mata Sakon text ta karanta taja tsaki ta mayar da wayar sai Kuma ta kira Wayar Yaya lami tana Fada Mata an turo Sako ta wayar ta wai Abdullahi Babu lafiya Yana Asibiti kwance.

Yaya lami ta iso gidan inda ta SHIGA wurin Farida wacce ta Kira ta ta Kuma shaida Mata Kiran da garba yayi Mata ya sanar Mata halin da Abdullahi yake ciki.

“Ikon Allah ko ta Ina Kuma ya samu wata guba ni lami? Gashi Kuma saura kwana bakwai mu tashi ni Kuma gashi ban san halin da yake ciki ba? Sai Yaya lami ta fashe da kuka don ita kadai ce ga Abdullahi Babu sauran yan Uwa sai na Zumunci na uwa da ya Uba Daya Daga shi sai yaya lami suke ga Juna.

Farida ta Soma Rarrashin Yaya lamin har tayi Shiru tana share HAWAYE tana Fadin

“Ni Yanzu damuwa ta da ban San Halin da yake ciki ba gashi sai nan da kwana bakwai zamu Isa can .

“Babu komai Yaya muyi ADDU A in Sha Allah Komai zai zo da Sauki.

Haka Yaya lami ta tafi tana Kara jinjina Ciwon Abdullahi.

Basma Kam ko a jikin ta wai an mintsini kakkausa ita ai dama Nan wurin take so a zo an Kuma zo .

Duk lokacin da Farida zata Kira garba Abubakar don taji ko Abdullahi ya farka za a ce mata bacci yake Abinda yayi matukar tayar Mata da Hankali tun tana jurewa har ta kasa ta Soma kuka don ta fara ji a jikin ta Al Amarin ba karami ba ne tunda har yau kwana Hudu basuyi Magana inda Kuma Yara suka ishe ta da Cewa ta kira musu uban su Amma ta Rasa Abinda zata ce Musu.

Yaya lami kuwa tafi kowa son satin Nan ya cika don ta Isa Saudi taga Halin da Dan Uwan ta yake ciki Amma kana naka Allah Yana NASA nasan Kuma shine hakika.

A cikon kwanakin Abdullahi da Zuwa Saudi garba ya Kira Farida Yana fada Mata Al Amarin da Bata taba zaton shi akan Abdullahi ba Domin kuwa maganar da yake Mata ne duk da Bai fito fili ya fada Mata gaskiya ba Amma ta fahimci Rufa Rufa ne kawai.

“Garba kar ka boye min don Allah Ina Abdullahi?.

“Gashi Can Za a shiga theater room dashi don likitocin sunce Babu tabbas a fitowa da shi .

“Fada min kawai garba Naji a jiki na Akwai Abinda ka Rufe mini kowace Rai bakuwa ce a Duniya ko ni ko kai Idan Allah ya Kira mu Dole mu Amsa Kira .

“Sai dai muyi Hak’uri Farida Amma Abdullahi kam Babu don tunda yaci gubar Nan Bai Kuma Wani motsi na kirki ba sai dai bugun numfashi da ya nuna Yana da Rai to Amma yanzu Kam an tabbatar da Rai yayi Halin sa har ma ana Shirin sadar dashi makwancin sa na Gaskiya don ba za a kawo shi Nigeria ba .

Wani irin Al Amari da ya sauka a ZUCIYAR Farida Wanda ya sa tayi suman zaune ta kasa motsawa har garba ya gama Maganar shi Amma Bata iya fahimtar shi ba Jin tayi shiru ne ya sa ya kashe ita Kam Bata kuma sanin Halin da take ciki ba.

Ita Kam Basma da garba ya Kira ta dauka Yana fad’a mata ALLAH yayiwa Abdullahi Rasuwa wata irin kururuwa ta fasa tana ta kwararaton Dole garba ya kashe wayar shi ya barta da ihun da take tamkar wata kaura.

Farida taji saukar Ruwan hawayen ta Yana jika mata Riga bata iya sharewa ba tayi karfin Halin Kiran wayar Yaya lami ta dauka tana Fadin

“Yaya lami kizo yanzu don Allah.

Yaya lami ta ce

“Lafiya dai Farida?.ko kunyi magna da Abdullahi ne?.

“Kizo Yaya lami don Allah kizo Yanzu.

Ta kashe wayar .

Da sauri Yaya lami ta Mike tana Fadin

“Wannan Kiran Wallahi ba na lafiya bane don banji Wani Aminci a cikin sa ba.

Isowar ta gidan ne yasa taji ihun da Basma take kwararawa sai ta shiga wurin Basma tana tambayar ta lafiya?.

“Baki sani ba ne Yaya lami? Yanzu aka Kira ni wai Abdullahi Babu shi ya Rasu Yaya lami an SHIGA UKU.

Sai ta Kuma kalla ihu tana tuma a k’asa.

Yaya lami ta dubi Basma tana maimaita Kalmar da ta fada Mata wai Abdullahi ya Rasu.

Ta zube k’asa dabas tana Raba idanu ita ba a Duniya ba ita ba a LAHIRA ba.

Kan kace me ? Mutuwar Abdullahi ta zaga ko Ina gida Kuma ya cika da Al Umma ta ko ina Basma da nata jama ar haka Farida da nata mutanen a kofar gida Kuma dangin su Yaya lami na birni da Karkara duk an Bazamo inda Matan Kuma Suke sauka wurin Yaya lami wacce take a sashin Farida Dole Yaya lami tace su kammala a sashi daya don takaitawa Mai Zuwa gaisuwa inda Basma tace Farida ce zata zo sashin ta a matsayin ta na Babba sai Yaya lami tace haka za ayi Dole Farida tazo sashin Basma ana zaman makoki Wanda Ake ta koke koke irin na gidan makokin da mutuwa ta ziyarta.

<< Tana Kasa Tana Dabo 55Tana Kasa Tana Dabo 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×