Skip to content
Part 58 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Hajiyar Sameer wacce ta Dawo daga jigawa ta samu Labarin mutuwar Abdullahi. Ta kadu matuka Gaya da Jin mutuwar Nan Amma Babu Abinda yazo zuciyar ta shine Sameer.

Hankalin ta kwarai ya tashi ta Mike jiki a Sanyaye ta na Shirin Zuwa gidan gaisuwar Kuma sai ga Wani Arashi Sameer ya iso Gidan inda Gaban Haj yayi masifar Sarawa Domin kuwa zaton ta ya gama tabbata.

Sameer ya zube a Gaban Haj wacce ta saki Baki tana kallon shi ta kasa Amsawa gaisuwar da yake Mata don ta gama yarda shine makashin Abdullahi Saboda muguwar zuciyar shi sai kawai Haj taji hawaye suna bin gurbin idon ta Sameer ya Zame mata kaddara a ZURIAr ta.

“Subuhanallahi Haj me ya Saka ki kuka? Don Allah don ANNABI kiyi min gafara Wallahi Babu wani.

“In banyi hak’uri da Kai ba in Yi maka me Sameer? Yanzu sai da ka kashe Mijin Farida ne Hankalin ka ya kwanta? Me kake.

Ya zaro idanu a matukar Rikice Yana kallon Haj.

“Mijin Farida Haj? Wallahi tallahi na Rantse Miki da girman Ubangiji Rabo na da Abdullahi tun Ranar da na harbe shi ban Kuma Saka shi idona ba. .

“Kai kar ka yaudare ni Sameer Bayan kasha wannan Alwashin na kisan mutumin Nan Wanda har ka Saka Bakin bindiga da son tabbatar da Hakan ? Kana nufin duk ban San hakan bane Halan? Da ka nuna shi da bingida Zolayar sa kake halan kauna ce Hakan? To Burin ka ya cika ka kashe shi Amma ka sani Wallahi ! Tallahi ! Idan don Farida kayi Hakan ni Kuma na haramta Maka Komen Auren farida sannan Kuma na barka da Allah da fitar Rana da faduwar ta Dukkan Abinda kakeyi kana cin nasara ba Wai Allah Yana son ka bane Yana barin ka ka Tara ne Kuma kafin aje ko Ina zaka Gane har Abada karya Bata tab’a yin kama da gaskiya ba ko da Kuwa an canja Mata suna don Haka Allah ya biya ka yayi Maka Albarka.

Kalaman Haj sun firgita shi har sun Saka shi Zubar hawaye.

“Wallahi tallahi Haj bani da Sani a cikin Abinda ya samu Abdullahi. Idan na San Wani akan mutuwar sa kar Allah ya bani ikon tashi daga gaban ki . Wallahi zuwa na kenan Kuma Nazo ne don na Gaishe ki na samu Albarkar ki Haj Amma na Rantse Miki da girman Ubangiji ban San komai akan hakan ba.

“Ai Kuma na gama yarda da Kai tunda Kai din mayaudari ne Kuma ma ha inci Sameer ta Yaya kake son na yarda da Kai? Kai ne fa ka nuna mutumin Nan da bindiga har Kayi mishi Silar fidda jini da son ka kashe shi don Allah Kai da kanka idan kaji ya mutu ba zaka zargi kanka ba? Yanzun nan nake samun LABARIN Rasuwar sa sai Kuma ga ka Amma ka Saka ni a Gaba kana min Rantse Rantse? Ai Kuma shikenan Allah Yana kallon zukatan mu ma bare ayyukan mu? In ni ka yaudare ni ai baka Isa ka yaudari ALLAH ba Kuma dama shine Mai Mana hisabi.

Hawaye ne ke ta zarya a idon shi don hakika ba zaice yaji dadin Rasuwar me Gemu ba Amma yayi kaico da yadda sunan shi ya Baci wurin mahaifiyar sa shi da kanshi Kam ya yarda da Abinda ta fad’a.

“Allah ta ala yayi mishi Rahama Haj Allah yasa makwancin sa ya zama dausayin ALJANNAH idan Kuma Ina da Hannu a kisan sa Allah kayi gaggawar bi mishi KADI.

“To Ameen wannan fa ai jazaman ne tunda shi Allah baya zulunci ko baka ce ba Lokaci ne Kawai.

Cewar Haj wacce ta Mike tana Rufa mayafin ta ta fice daga gidan Bata Kuma bi ta kanshi ba .

Sai ya tashi Shima ya nufi gidan Hajiyar Farida inda ya Samu tarba da Oyoyo Daga Saddam da Hanan.

Haj ta Dube shi jikin shi a sanyaye.

Yana Rik’e da Hanan wacce ta zama Yan Mata shi kuwa Saddam ya zama saurayi .

Ya zube Yana Gaishe da haj wacce ta amsa tana tambayar shi Aiki.

“Haj sai Yanzu nazo nake samun LABARIN Rasuwar Abdullahi Wallahi ban Sani ba .

“Allah sarki yau kuwa kwana UKU kenan yau akayi Sadakar UKU.

“Allahu Akbar Allah ya jikan shi yayi mishi Rahama yasa kwanciya hutawa.

“Ameen Ameen allah Allah ya Bada Lada an Gode Sosai.

“Yayi jinya ne haj? Ya tambaya da son yaji ko yayi jinya.

“Eh to yayi jinya ne a can Saudi Arabia ya tafi Aikin Hajj. Kwanan shi uku ne ko biyar ya Soma Ciwon? To ance dai guba ce yaci Kuma tunda ya ci ta ya fita a hayyacin sa Bai Kuma sanin Wanda yake kanshi ba sai aikowa akayi Rai yayi Halin sa don a can ma akayi Mishi sutura ba Nan ba Rabon samun wannan tagomashin.

Ya sauke AJIYAR ZUCIYA Yana Fadin

“Allah ya jaddadda Rahama kabarin sa tare da dukkan muminai maza da Mata in Sha Allah zan samu zuwa nayi wa Farida ta aziyya kafin na Wuce.

“To Allah ya Bada iko Rayuwa kenan Mai Abu da yawa Sameer Ashe ganin karshe nayiwa bawan Allah Nan yazo min bankwana Yana ta Raha shi da su Saddam Ashe tafiyar da Babu Dawowa ce ganin na karshe ne. Kai Mai Rai Yana da Aiki a gaban sa ALLAH kayi Mana kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma Al Amarin da girgiza zukata yake Wallahi yanzu shikenan. Shi Kam anyi farar tafiya Wanda ya mutu wannan wuri ai ya dace.

Ya jima a gidan Hajiyar Farida tana kashe mishi jiki da kalaman ta akan wannan Rayuwar da Kuma Rasuwar Abdullahi.

Ya bawa Hanan da Saddam kayan da ya Ruko musu ya bawa Haj kudi kafin yayi sallama da su ya wuce majalisa inda ya samu su Mai naira Wanda Suke ta maganar mutuwar Mai gemu inda ya Gane garba Abubakar tare Suka tafi Saudi Arabia da Mai gemu Kuma a wurin garban Abdullahi ya cika. Ya Dade a majalisar sun Kuma jajantawa juna tare da yiwa Mai gemu ADDU AR samun Rahamar Ubangiji kafin ya bar majalisar cike da jimami da alhini da Kuma nadamar keta haddin da yayiwa Farida wacce take iyalin Abdullahi.

Haj ta iso gidan Abdullahi sashin Farida suka Rungume juna suna kukan tausawa Kai.

“Sannu Farida kinji ? Sannu da Hak’uri Allah ta ala ya kamawa Rayuwar ki ya Baki Hak’uri Amma kinyi Rashi don samun kamar Abdullahi Kam ba zance Babu ba Amma Yana da Wahala. Da wane idon zan Dube ki Farida? Nace Miki me Kuma? Wallahi sai a yau na Dawo daga jigawa muma a can din Rashi akayi mini na Yar Uwa ta Haj Jamila Dan fajo Ina dawowa Kuma na samu Labarin mutuwar Nan sai ga Sameer ya bayyana. Farida bana ko shakka Sameer ne da wannan Aikin ni kuwa ame Duniya zata kalle ni ?.

Farida ta Yi kokarin tsayar da kukan ta tana share HAWAYE tana bawa Haj wurin zama ta zauna Suka gaisa ta na Miata ta aziyyar Yar Uwar ta itama Haj ta Yi Mata ta Abdullahi.

“Kar ki boye mini Farida don nasan Babu haka a tsakanin mu saboda Allah me ya faru da mijin ki kafin Rasuwar sa ? Jinya yayi ko kuwa an Kuma tab’a lafiyar ta hanyar harbi ko Wani makami?.

“A a Haj Babu hannun Sameer a cikin Rasuwar sa don ba ma a Nan Nigeria ya Rasu ba. Sun tafi Aikin Hajj Saudi Arabia kwananki biyar kenan da tafiyar sa Amma kafin Nan ya kwanta jinya har kwana UKU inda likitoci suka tabbatar da yaci guba ne Kuma tunda ya ci gubar Bai Kuma sanin Wanda yake Kansa ba da yake Al Amarin yazo da k’arar kwana sai dai aikowa akayi Rai yayi Halin sa . Har ga Allah Babu Hannun Sameer Haj bana ma zaton ya San da Hakan don tun Ranar da kika ce Zakiyi mishi magana ko kira na Bai Kuma ba shiyasa ma ba zan iya Saka Naman sa a Wuta har runtsewa zan iya Yi cewa Babu Hannu shi a Nan.

“Banda a bakin ki naji Hakan Farida da ba zan iya yarda ba tunda ya iya nuna mijin ki da bindiga to kowaye ma Dole ya ce shine ya kashe shi tunda da wannan manufar ya harbe shi da bindiga Amma ALLAH yana Nan ya Kuma San Abinda bamu sani ba in ma Yana da Hannu ko baya da Hannu duk in yaso Zai FALLASA.

Haj ta taushi farida ta Kuma yiwa Abdullahi ADDU A tana tambayar Ina su Salman da Sulaiman? Tace suna waje don kwana biyu suna kukan Neman Uban su ne sai wata makociyar su nan take Jan su suna shiga gidan ta cikin yaran ta suna wasa har su debe kewa.

Haj ta koma gida tana tunanin Al Amarin Mijin Farida da aka ce yaci guba . Zuciyar ta ta kasa yarda da Babu Hannu Sameer don duk wanda yayi Alwashin kashe ka ta kowace hanya zai yi kokarin Ganin burin nashi ya cika

Ya faka motar a kofar gidan Abdullahi yakubu Mai Gemu da nufin yayiwa Farida ta aziyya sai Kuma ya tuna da kashedin da Haj tayi mishi na in ya Kuma Duban kofar gidan farida ma bare ya taka shi da kafar sa ta sallamawa DUNIYA shi.

Sai yaja ya tsaya cik Yana shawarar ya koma ko kuwa ya shiga kawai in ya so in ya fito sai ya nemi gafarar Haj ya Kuma fada Mata yazowa Farida gaisuwa.

Ya Daga kafa ya nufi sashin nata Wanda yake dauke da kanwar mahaifiyar ta wacce tazo tace zata Zauna da ita sai Kuma maman Umar da taxo Mata gaisuwa sai Kuma wasu Mata da bai waye su ba .

Yayi sallama a Bakin kofar inda Farida taji Wani Abu ya sauka a ZUCIYAR ta Kuma tashi Daya ta Gane Mai muryar wato Sameer.

Inna ladidi ce kanwar mahaifiyar ta ta leko ta ga shine tace

“Au baban Saddam ne? To shigo Mana.

Ta juya shi Kuma ya bi bayan ta har cikin falon inda suka gaisa da Matan da suke ciki yayi musu gaisuwa kafin yayiwa Farida ya Kuma ce su karanto salatin ANNABI MUHD S A W tare da kulhuwallahu UKU UKU yayi ADDU A Mai tsayi suka shafa ya Kara nemawa Abdullahi Rahama da gafara kafin ya Mike da nufin tafiya inda Farida ta biyo shi Suka fito bakin kofar sashin ta ya tsaya Yana Kara Yi Mata gaisuwa ta amsa tana Fadin

“Haj tazo har tana zaton mutuwar Rasuwar Abdullahi da Hannun ka ni Kuma na Sanar da ita tun Ranar da mukayi magana da ita ko waya ta baka Kuma Kira ba Ina ganin idan kayi Mata bayani zata fahimce ka .

“Nagode Farida kema na San don ba a k’asar Nan Abdullahi ya Rasu ba kema da na tabbatar Babu Mai fidda a wurin ki cewa ba ni ne na kashe shi ba. Kuma ni da kaina ma naji Ina zargin Kaina tunda na daure kaina da kaina Amma Allah ya sani nayi nadamar Abinda nayi Allah Kuma shine shaida .

Basma da da ta Daga labulen tagar ta ta hango Sameer tsaye da Farida sai ta sai ta Sako hijabin ta ta fito tayi musu tsaye tana auna musu wani Shegen kallo kafin tace.

“Wai har yanzu mutumin Nan Bai Hak’ura da Zuwa gidan Nan ba ? Duk mugun Aikin da ya tafka yanzu ma da Mai Gidan baya Raye ba za a Hak’ura ba ? To zo ka shige kar Kuma Tako kafar ka a gidan Nan Wallahi don yanzu wannan gida na ne duk Abinda na Gani baiyi min ba Zanyi magana zunubin da aka dauka Hakan ya Isa in Kuma ba haka ba Wallahi yanzu zan FASA KWAI na yaga Leda ko da biredi Bai Dadi ba Kuma ka saurari Kira don kayi shuka ne akan idon makwarwa Dukkan Abinda kake zaton a cikin Duhu kayi su ni a idona naga Komai Kuma ba zan tab’a bari ayi min lullubin biri ba don Haka da kaji Kira ni ce nayi shi don zaka zo ka bayar da Bayanin wasu hotuna da na dauke ku Kai da ita har da ma hoto Mai motsi Wanda baku isa ku karyata ni ba in Kun karyata ni din su zasu gasgata ni don Haka idan tayi tsami zakaji ko na Nemo tsohuwar ka wacce zata sanar da Kai don haka ga hanya fice min a Nan ko Kuma yanzu na Tara maka Al Ummar ANNABI nace ga kwarto.

Wani irin tsoro da firgici ya shigi Sameer da Farida Wanda Bai Boyu a fuskar su ba har Sameer ya saki kafa ya fice da sauri don Bai tab’a Jin tsoro a Rayuwar sa ba irin yau da matar Nan take Neman mayar mishi da k’asan shi ya koma sama . Me take nufi da wannan maganar? Wane irin Kira take nufin Yi mishi? Me take nufin sanar da Haj idan tayi tsami? A matukar Rikice ya fice daga yankin. Yana jin hakikatan duk Wanda yayi yadda yake so yadda baya son din tana Nan baya.

<< Tana Kasa Tana Dabo 57Tana Kasa Tana Dabo 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×