Skip to content
Part 59 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

“Aikin Banza wai Zakara ya taka WUKA tun ana yin Abun a boye har an fito a Fili ? To Nan Gidan mutuwa ne a bari har ayi Arba in mana za a zo Nan filin Allah ta ala ana Mana shafe shafe da tsotse tsotse? To Yasin na Kuma Ganin kafar mutumin Nan a gidan Nan za a ga Abinda zai faru. Ya’ya Mata gareni in na bari suna Ganin wannan iskancin ni za a cuta.

Cewar Basma wacce ta Raka Sameer da wani matsiyacin kallo Lokacin da yake ficewa a Rikice kafin ta juyo ga Farida wacce ta kasa daga kafarta bare tayi jarumtar komawa ciki.

“Kar mutumin Nan ya Kuma Zuwa mini gida. In son Ganin yake yake daukar ki kuje hotel ko Wani wurin Amma don Allah a bar Mai gidan Nan ya Kwanta a kushewar sa lafiya ba tare da Kuna sakawa ana katse mishi bacci don a tayar Dashi yaga Abinda ke faruwa a gidan sa da iyalin sa. To a bari har lokaci yayi Mana alkalanci in kika tafi can haular ku in zakuyi Shekarun ANNABI nuhu a tare Kuna Abinda kuka ga Dama Babu laifi in Kuma kukayi hak’uri ma ai dama ce kuka samu ta komawa Auren ku Amma Nan dai Kam in na Kuma Ganin kafar gayen Nan Wallahi zance Wani Abu mu ci gaba da istigifari Kawai.

Ta juya ta shige sashin ta ta bar Farida sake da Baki ta kasa cewa uffan sai harbawar gaban ta da yake Hawa da sauka ba don komai ba kuwa sai hutunan da Basma tace ta tana da har da Masu motsi. Shin hoton meye wurin Basma?..

Tun Daga wannan Rana tashin hankalin Farida ya lunku don tana tsoron Sharri daga Basma Wanda zai Bata mata suna a Duniya ..

Kwanaki Arba in cif Wanda yayi daidai da kammala ibada ga maniyyatan da Ubangiji ya nufe su da Zuwa ziyartar manzon Allah suka Kuma sauke farali.

A jirgin farko garba ya iso kamar yadda sune jirgin farko a tafiya. Tafiyar da akayi ta tare da Amini Kuma Aboki sai gashi ya dawo shi kadai sai fa Kayan Abdullahi da ya taho da su tun daga Kan jakar sa da guzurin sa Wanda ya karba a Ranar da suka Sauka Saudi Arabia zuwa kudaden shi da suke aljihun shi da Kuma sauran kayan bukatar da ya tafi da su irin takalmi da da wayoyin hannu duka garba ya kammale su ya taho da su tare da kayan da sune a jikin shi Lokacin Da ya bar gida Nigeria ..

Daga Filin jirgin Saman malam Umar Musa Yar Adua da aka dauko garba Gidan Abdullahi ya zarto Kai tsaye inda Kuma ya Rasa sashin da zai fara Isa don ta ko Ina kowace tana da hakkin Hakan Kuma idan ya shiga sashin wata wata zata zargi Wani Abu musamman da ya iso da kayan Abdullahi..

Don haka Yana shigowa a farfajiyar Gidan ya daga waya ya Kira Basma yace gashi a kofar ta ya Kuma Kira Farida itama yace gashi a kofar sashin ta..

Basma ta fito wacce suka fito kusan a tare da Farida suka ga garba a farfajiyar Gidan zaune a Saman boot din motar jikin shi a sanyaye Yana k’arewa gidan kallo kusfa kusfa..

“Haba garba sai ka tsaya a waje sai kace Wani Bako? Cewar Basma..

Farida kam idon ta akan jakar Abdullahi wacce ya tafi da ita da ta Gani a gaban Motar..

“Masha Allah Alh garba sannu da Zuwa ya ibada ? .

Ya amsa da fad’in

“To ibada mun Godewa Allah Yaya mukaji da Hak’uri Kuma? To Allah ya Kara muku Hak’uri ya Kuma duba marayun ku da na sauran Wanda Suka Rasa Nasu iyayen..

Suka Amsa su Duka da Ameen Ameen

Ya Dube su Yana Fadin

“Rayuwa kenan Allah ya kaddara Mana tafiya tare da Abdullahi Amma Ashe Ajali ne ya Kira shi. Amma mun Godewa Allah da yasa tafiyar tashi ta zama farar tafiya ce ko Babu komai ya daura harami ya Kuma Soma ibada Kuma ya Rasu a gari mafi Daraja an Kuma binne shi a makabarta Mai Bai Daraja wato Bak’i A ko wannan kadai ya Isa yasa Mai Imani ya yarda Abdullahi ya dace . To dole ne nayi Muku Bayanin Halin da ya kasance a ciki har zuwan shi Asibiti da Kuma cikawar sa da janazar sa Wanda nine na zama jagoran komai ..

“To ni dai Abinda na sani mun fita masallaci muka gabatar da ibada wacce sai da akayi sallar Isha I muka baro masallaci bayan mun Soma Aiki. Mun karbi madarar labal tare da tuffa muka taho masaukin mu a Nan Abdullahi ya Debi Dambun Nama ya Soma ci yayi min tayi nace ni Kam na dagawa nama kafa saboda likita yace min na Rage cin sa kar na kamu da gawut..

Labal milk da tuffa kawai Nasha na kwanta Ina hutawa a lokacin Muna Dan tab’a fira Muna Kuma Kiran iyali Muna Jin lafiyar su inda yake fada min Yana Kiran wayar Basma Amma Taki dauka yayi Mata text Babu reply. Nace kayi laifi ne in kaga Hakan Hukunci ne kake karba ..

Ina Jin shi Yana ta surutu da Sulaiman da Salman kafin ya koma ga Farida..

Ni dai na Soma bacci sama sama na Soma Jin kakarin Amai na Bude ido na na ganshi kaca kaca cikin Amai..

“Subuhanallahi Abdullahi baka da lafiya Kuma baka tayar Dani ba?

Jikin shi yayi Sanyi matuka Domin Amai yayi Mai yawa ko da muka Isa Asibitin ma Ruwa Ake ta Kara mishi yayin da gwajin likita Kuma ya gama tabbatar da yaci a cikin abubuwan da yaci Guda UKU. Labal milk ko tuffa ko Kuma Naman Nan..

Gaban Basma ya Sara Domin kuwa taji Wani Abu Yana Hawa kanta duk da Bata iya Gane ko meye ba Amma ta girgije..

“Bamu tsaya bin diddigin ta Ina ya ci gubar ba. Domin kuwa Babu Abinda muke fata da buri irin muga ya dawo hayyacin sa Domin kuwa tunda muka Kai shi Asibitin Nan Bai farko ba sai dai Hawa da saukar numfashin sa shiyasa ma na Sanar da ku don a Taya mu da ADDU A Abinda bamu sani ba ma shine Al Amarin duk ya Kare dab Ake da tafiya wacce ba za a waigo ba sai dai a darusslam..

Farida ta share Hawayen ta tana fadin

“Allah kenan haka ya tsara mishi fatan Ubangiji yasa Yana cikin Aminci..

Ya amsa da Ameen Ameen.

Ya bude motar Yana fiddo jakar Abdullahi tare da wayoyin sa har da kayan da ya tafi dasu a jikin shi ya kawo su gaban su Basma da Farida Yana fadin..

“Ga wayoyin sa da kudaden sa har da guzurin sa wannan Kuma kayan Yara ne ya Soma Siya musu komai dai nashi Yana ciki .

“Bani su Nan garba .

Cewar Basma wacce ta Mika hannu ta karbe kayan ya Kuma Bata ..

“Yanzu garba Yaya za ayi da kudin da ya biyawa su Yaya lami da yaran Farida jirgin yawo? Shin za a Karbo su ne tunda yanzu sun zama na magada?..

“Eh Dole ne a karbo su tunda ba a je ba ai Dole a dawo da kud’in Amma Kuma ba Wai Yana nufin sun zama na magada ba tunda ba wasiyya yayi ba kyauta ce yayi musu basa daga cikin kayan gado tunda yayi kyauta ne Yana Raye..

“A a garba ai Kai kanka sai dai kaki gaskiya Amma ta Yaya ga Najwa da Nabeela za ace anyiwa Salman da Sulaiman kujera tare da Yaya lami? Ai ka San ma ba zan yarda ba don Haka dama Kai nake Jira ka dawo don a tattara Mana dukkan kaddarorin Abdullahi don nayiwa Wani alkali magana Ina so ya Raba Mana gado don haka ka Soma mama kokarin hada mana kan Dukiyar shi ayi a sallami kowa..

“To Babu damuwa ku bani time don yanzu na dawo daga ibada kuyi min hak’uri zuwa nan da sati Daya Amma Zanyi kokarin Ganin na Sako Baba isuhu cikin Al Amarin don Dole sai da shi tunda shine matsayin Uba ga marigayi Abdullahi Kuma shine Uban Kabir Wanda shine manajan Abdullahi Shima ya San komai na Daga dukiyar da take shagon Nasu Shima Ina Ganin zai Rage Mana Aiki ..

“Babu matsala garba mun Gode Allah ya huta gajiya sai na jika.

Cewar Basma

Garba ya juyo Yana Duban Farida da baiji ta ce Komai ba .

“Farida Baki ce komai ba? Hakan yayi Miki ne ko kina da korafi?..

“Yayi garba bani da Wani korafi duk yadda akayi yayi mini daidai Allah ta ala yayiwa Abdullahi Rahama da gafara Kai Kuma Allah yasa kayi ibada karbabbiya.

.

Ya amsa da Ameen Ameen ya Rabb

Ya fito da zam zam da bagaruwa ya Basu ya Kuma ce sai ya Dawo Anjima..

Yayi musu sallama ya Wuce.

Satin da ya Ambata Bai cika ba suka gama tattare komai na game da Dukiyar Abdullahi tare da hadin gwiwar Kabir Dan gidan baba isuhu Wanda shine manajan Abdullahi Wanda ya San komai na daga office din su na canji har ma ya San wasu kaddarorin na Abdullahi don ya yarda da Kabir Wanda Shima ya tsayawa gaskiya har Abdullahi yayi mishi komai na Rayuwa don haka mutuwar Abdullahi sai ta zamo Tashin hankalin Kabir don shi Kam yayi Rashi

Baba isuhu Wanda har da shi tattare komai na Abdullahi Kuma aka karbo kudin jirgin da ya biyawa su Yaya lami inda Goggo Amu tace kudin da ya biyawa su lami kujera ai ba na gado bane ..

Basma tayi maza tace

“A a Goggo ta Yaya za ayi min wannan Rashin Darajar ni ba a biyawa Ya’ya na ba za a biyawa kannen su ko don su suna Maza? To ai a gadon ne kawai suke da banbanci Amma a Raye matsayin su Daya ne don haka ban yarda ayi Hakan ba in su Ya’yan shi ne ita Kuma Yaya lami fa?.

Baba isuhu ya Dubi Basma Yana Fadin

“Dole fa a fitar da kud’in Nan Basma a biyawa lami da Yan yaran Nan tunda kyauta ce yayi da wasiyya ya bari Babu Mai cika mishi ita Tunda dukkan mu mun San Komai don haka wadan Nan yaran Kai garba ka baiwa Uwar su kudin tafiyar su itama lami ka Bata nata don kud’in da ya biya musu basa cikin na gado tunda yayi kyautar ne Yana Raye Kuma kina Ina ke Basma lokacin da yayi kyautar me ya Hana ki kalubalen ce shi? Ai Ina ce dai ko Bai fad’a Miki ba kinji yayi Hakan me yasa Baki ce wani Abu ba? To dole a fiddawa Wanda yayiwa kyauta Abinda ya bayar Kai garba ku bawa lami kudin ta Suma yaran Nan Sulaiman da Salman bawa Uwar su kud’in su in zata kaisu ne can saudin Ruwan ta in Kuma zata Adana musu kud’in su ne duka dai Ruwan ta .

Garba ya karbi wayar Kabir wacce kudaden suke lode a ciki Yana yiwa Yaya lami transfer a account din ta na kud’in da suka karbo Wanda za a Raba su uku Sulaiman da Salman kaso Biyu sai Yaya lami kaso Daya. Tuni kuwa garba ya turawa Yaya lami kudin ta Suma su Sulaiman garba ya tura musu ta account din Farida ..

Basma Kam mikewa tayi tsaye tana Kuka tana Fadin

“Ni Dama na San ba zakuyi min Adalci ba baba isuhu shiyasa ma nayiwa kotu magana gashi Kuma tun ba aje ko Ina ba an fara da Rashin Adalci to Wallahi da Yaya lami da kudin da aka bawa Salman da Sulaiman sai sunyo aman su don ban yarda ba ba Kuma zan yarda ba . In Banda Rashin Adalci ace mini wadan can Yaran sun Fi su Najwa kaso Kuma ace an Kuma daukar wasu kudi an Basu Nima ai ya taba cewa zai Kai su Najwa Saudi ..

“Ki kawo shaida kema sai ayi Miki adalcin a Baki Abinda yace zai bawa su Najwa din ..

“Su ma shaida suka kawo da aka Basu wadan Nan kud’in? Sai nice za a ce na kawo shaida? Ni dai wannan Rabon son zuciyar Baiyi mini ba Wallahi muje kotu Kawai ayi a can don nasan can ba zasu zalunce ni irin Nan da Ake min zalunci ba..

“To Basma muje kotun Mana ai shi alkalin da zaiyi Rabon ba jahili bane Yana da ilimin abin muje Kawai.

Cewar Baba isuhu ..

Yaya lami ta dubi baba isuhu tana Fadin.

“Baba ni dai Kam na Hak’ura da kudin Nan a mayarwa Basma da kud’in Nan tun Bata Bude baki ta zage ka ba Amma Kuma hakikatan kudin su Salman da Sulaiman ba za a maido Mata su ba sai dai taje gaba da kotu ma ba za a dawo Mata da su ba Wai fa ita Nan duk borin kunya take kar su Salman su Fi nata Ya’yan gado to ta makara Wallahi Abinda Bata son ne zai faru..

“Gara dai ki maido wa Yara kudin su Yaya lami har su din Wallahi sai sun Kun maido don ban yarda ba Wallahi..

“Wallahi ba za a dawo Miki da kudin Nan ba Basma muje gaban kotun nafi son Hakan lami kudin ki sun zama naki har gaba da Abada ba Kuma Zaki dawo da su ba taje kotun Muna jiran Kiran alkalin..

Basma ta Kuma Saka kuka tana Fadin

“Ai kuwa Baba Wallahi Dole na Maka ku a kotu ko da banyi Niya ba sai kuma na Gane ba zakuyi min Adalci ba to Wallahi ku saurari sammaci dama ni na San Kuna jiran irin wannan Ranar da zaku nuna min iyaka ta gashi Kuma tazo to Nima ban yarda ba ba Kuma zan yarda ba zanyi magana da yaren da za a fahimce ni tunda Naga Nayi magana da yaren hausa Baku fahimta ba to ku Jira sammaci.

<< Tana Kasa Tana Dabo 58Tana Kasa Tana Dabo 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×