Suna cikin wannan Halin ne Najwa ta shigo ta kuma ga Abinda suke Wanda yayi matukar Gigita ta har taja baya da sauri tana Shirin faduwa.
Basma ta saki mamman Wanda yake Shirin cire Mata harshe da kissing.
Basma ta Soma fada tana zagin Najwa akan shigowar ta Babu nocking.
Mamman ya Mike Yana Fadin
“Kyale yarinyar Nan haka Mana kike auna Mata irin wannan zagin?
Ya kamo Najwa da take Zubar da hawaye Yana Rarrashin ta Yana shafa kanta Yana Bata Hak’uri har ta wuce Uwar D’akin tana share HAWAYE.
Mamman ya Dubi Basma Yana Fadin
“Dauko gyalen ki muje ai Kuma kwana a Nan gidan zai Mana Wahala tunda yaran nan sun Soma wayo.
Babu musu Basma ta dauki gyalen ta da key din mota duk da tana son tambayar mamman inda zasu je amma kamar Mai karbar Umarni haka ya karbi key din motar ya bude suka shiga yaja su Suka fice daga gidan inda Yaya lami take tsaye tana kallon Basma da Wanda ya dauke ta a motar da Mamakin Kuma Ina zasuje . Amma sai ta Daina mamaki don ta iya yuwuwar duk cikin Neman yadda za ayi ta Haye manubar da ta shirya ne sai kawai ta wuce zuwa sashin Farida don duk lokaci tana Zuwa duba su musamman Farida da take cikin yanayin ciki duk da cikin yayi girma Sosai tamkar Mai Cikin Ya’ya biyar zama da kyar tashi da kyar
Hotel Basma taga mamman ya faka motar ya fito yace ta fito ta kuma fito suka shiga ya kama d’aki aka Basu key ya biya kudin D’akin suka wuce tana biye da shi duk da Ranta Bai Mata Dadi ba akan Zuwa hotel din Amma tamkar wacce aka daurewa Baki
Yadda ta San shi Yana Nan da Halin sa don haka mamman ya sauke gajiyar shi akan ta ba su Suka koma gida ba sai Tara saura Shima don ta matsa mishi da su koma Amma shi yadda ya so kwana yaso suyi Amma ta fada mishi ta baro su Najwa Dole ta Koma.
Haka ya dauko ta a motar suka Nufo gida Yana fada Mata shi Kam yanzu yake Jin sonta kuma tana gama takaba zai Fito suyi Aure
Suna shigowa Gidan yace zai wuce yace ta bar mishi key din motar ya Dan zaga gari da ita tace yaje da ita.
Suna cikin motar ma Basu Hak’ura da watsewa ba duk da Basma ba son Hakan take ba Kuma ta kasa ta Hana shi ko tace Bata so duk ta Kasa Dole ta ke biye mishi inda a motar ma bakin su a hade Yana shafa jikin ta .
Tamkar ance su juyo suka ga Yaya lami wacce tayi mutuwar tsaye Ganin Abinda yake faruwa ta kasa motsi idon ta Kur akan su Suma Kuma suka ga yadda take kallon su Dole jiki ya dauki Rawa .
Yaya lami taja kafar ta ta fice tana waiwayen su da Mamakin Abinda ta Gani.
Basma ta fita motar tana fadin
“Kaga Abinda kaja mini? Yanzu wannan matar duk Duniya sai taji Abinda mukayi har da k’arin gishiri duk sai tayi dama tana Daya Daga cikin masu son Ganin Wani Abu ya faru Dani sai Kuma gashi kaja mini .
“Rabu da ita da Allah Kar ma ki bari ta zama damuwar ki taje tayi ta barbadawa Mana ba itace da kunya ba? .
Yaja motar a guje ya fice.
Abinda Basma Bata Sani ba shine mamman da Shirin shi yazo. Shirin da yake son ya yashe ta akan Gadon su Najwa da Nabeela idan ta karba saboda Yana da manufa akan Hakan wacce yayi nufin Ko a mutu ko ayi Rayuwa sai Kuma ya fito mata da sigar Aure don ta haka ne kawai burin nashi zai cika Amma sai taji ta Soma fad’a mishi su bar maganar inda ya Gane ba zata yarda sai kawai ya yanke shawarar zuwa wurin malamin shi don Dukkan Abinda ya fada haka akan irin jagwal da Rigimar da take kanshi iyakar Abinda ya fada Mata ne Amma ya Rufe wasu abubuwan da yawa daga ciki don ko wannan kudin da ya Bata ajiya wata Rigimar ce akan su Amma don ya fasawa Basma Kai yasa ya Bata AJIYAR su Kuma karya yake Babu wani tagullar Gold din da ya kawo sai ma zamba da manuba don haka sai ya Gane cewar akwai Datar da zai samu wurin Basma Amma Kuma Bai ga ta yadda za ayi ta yarda ta bashi Damar samun Datar Nan ba shine ya shiga ya fita ya zambato kud’in nan har ya biya ta bashin ta ya Kuma Yi mata kyautar ds zata nutsar da ita ba tare da ta kula ba shi Kuma yaje ga malamin tsubbun shi Wanda ya karantawa Yana so ya mallaki mace wacce komai yace Mata Bata Isa tayi mishi gardama ba Kuma duk Abinda zaice bani zata bashi Babu musu bare in Kari. Shine aka Bashi kwalli Wanda yace mishi matukar yayi ido Hudu da wacce yake so ya mallaka din to an gama in Ranta yace ta bayar zata bashi Babu gardama ko da Kuwa tana ji a Ranta ba Hakan taso ba ba Zatayi mishi gardama ba. Don haka a Ranar mamman ya fesa wanka ya Kuma samo Kayan Alfarma da kudin da ya zambato Wanda ya Siyarwa Wani mutum Wani Fili da bai san me shi ba Amma ya Yi takardar bogi ya bashi shine fa ya taho da wadan Nan kud’in don ya fasawa Basma Kai ya Kuma jaraba Aikin shi sai gashi ya Saka kwallo a Raga Kuma ya lura tazo Hannu Don haka mamman ya Soma tsula tsiyar sa da son ya bugi cikin Basma ta fada mishi inda kaddarorin Nan na marigayi Abdullahi ta Kuma soma fada mishi katon filin da ya mallaka har ya bawa kamfanin MTN haya suka kafa service din su Wanda Suke biyan haya duk shekara manyan kudade inda mamman ya Soma tunanin ta yadda za ayi ya kad’as da Filin Nan don milyoyi za a karba Amma ya Rasa hanyar da zaiyi Hakan ba don komai ba sai don service din da MTN suka kafa a wurin duk Wanda za a kawo zaice to in ya Siya ta Yaya zai iya tayar da kamfanin MTN Mai Zai Hana su kamfanin su Siya kawai Kai tsaye?
Ranshin Sanin inda branch din da suka karbi hayar ne ya kawo mishi tsaiko don haka ya Saka Basma Nemo mishi address ko Kuma samo Ina ne branch din Wanda Suka karbi hayar yake don wannan kaddarar itace mafi girman da za a karbi kudi masu Nauyi .
A duk Lokacin da zai bata Aikin samo address ko branch zatayi kamar ta kashe Kanta wurin Nemo mishi don bata iya Yi mishi musu ko gardama Amma da ya bar Gidan zata watsar haka yasa aka dauki dogon lokaci ba a iya samo address din ba Kuma kullum cikin auna Hikimar yadda zaiyi ya samo hanyar siyar da Filin Amma tamkar an Saka mishi jeck Al Amarin ya kasa Samuwa.
Ranar wata laraba Farida ta tashi da nakuda Allah yasa Yaya lami tazo tana tare da su don har su Saddam da Hanan sun zo Nan wurin ta suna ta fira Yaya lami tana son fadawa Farida Abinda ta Gani Amma Kuma tana son Rik’e girman ta kar ya zube Dole ta kame Bakin Ta Amma duk da haka sai da tacewa Farida
“Ni kuwa kwana biyu Ina ganin Wani mutum Yana safa da marwa sashin Basma Dan Uwan ta ne ko kuwa dai Wani nata?.
Farida ta Dube ta tana fadin
“Wallahi Nima na ganshi Yaya lami sau biyu Amma dai ban San mata ba ko Dan Uwan ta ne .
Sun Dade suna fira kafin Yaya lami tayi musu Sallama ne kugun Farida ya fara Rik’ewa kafin taji marar ta ta kulle duk yadda taso tayi jarumtar Hana Wani motsi ta kasa har Sai da Yaya lami tace ko abin ya taho ne?
Bata iya Bata Amsa ba saboda yadda ciwon ya taho gaba Daya Dole Yaya lami ta Kira Kabir ya iso da mota suka nufi Asibiti. Allah Cikin ikon shi Babu wata doguwar nakuda sai ga katon yaron jajir tamkar Abdullahi yayi kaki.
Yaya lami tana Rik’e da yaron tana hawaye tana ta Fadin
“Iko sai Allah Abdullahi ya tafi Abdullahi Kuma ya Dawo.
Yaya lami ita da Kabir suna ta kambama kamar yaron da Uban sa sai ga Nas din ta Kuma Zuwa da wani yaron Shima dai kamar Dan Uwan sak Uban su .
Yaya lami sai ta Kuma saka kuka tana Rungume da yaran yayin da Kabir yake Rik’e da daya inda Yaya lami sai Fadi take .
“In ba Allah ba wa ya Isa? Wannan shine hannun Riga Yara kunzo Duniya lokacin da Uban ku ya barta. Ina ma ace kunyi nasarar Riskar sa da Rayuwa? Da Kun tabbatar da kauna da soyayya irin ta mahaifi.
Sai sambatu Yaya lami take inda Kabir ma sai da yayi wa yaran Hawayen tausayi
Aka kira Hajiyar Farida aka Sanar da ita aka kuma Kira su baba isuhu da Haj kulu duk aka fada musu Haihuwar Farida ta twins identical twins.
Zuwa yamma aka sallami Farida suka wuce Gida inda Yan Uwa da dangi suka Soma turarowa ganin Yara .
Basma Bata gida Lokacin da akayi Haihuwar mamman ya dauke ta zuwa hotel don tun da ya Soma kaita hotel din da sunan bad’ala Bai kuma Daga mata kafa ba don Haka suna can sai da suka gama wulakancin su Suka dawo inda Najwa ce take fadawa Basma maman su Sulaiman ta Haihu twins.
Da Wani matsiyacin firgici Basma take kallon Najwa tana Fadin
“Ke kika ce twins ? Mata ko Maza?.
“Baby boy ne Duka ni kuma naso ta haiho baby girl.
Da Wani irin sauri Basma ta buge bakin Najwa da bayan hannun ta da sauri Najwa ta kame Bakin ta tana kallon Uwar tata a tsorace.
Da sauri ta fito ta nufi sashin Farida inda ta iske su Goggo Amu da Hajiya kulu d’akin Farida a cike ta Ratsa tana Gaishe da su Goggo Amu da Haj tana fadin Ina Mai jego?
Farida ta fito wanka taga Basma wacce take a furgice tana fadin
“Sai yanzu Najwa ke fada min anyi Haihuwa saboda Allah a kasa fada Min ko Babu Abinda zanyi ai zai ce Allah ya Raya.
“A a fa ni na tura Saddam ya fada Miki Nabeela tace Kun fita da uncle mamnan ko uncle Mani? Oho dai haka ya dawo Yana fada min .
A tsora ce basma ta ce
“Eh Wallahi munje Asibiti ne .
Farida ta Miko mata yaran tana karba tana Gani kamar su da Abdullahi har ya Baci inda taji wani matsiyacin firgici Yaya Hudu ita da tana da Biyu?.
Tana shirin aje Yaran ne Baba isuhu ya iso ya shigo har ciki Yana yiwa Farida barka ya karbi yaran Yana musu hud’uba inda ya sakawa Hassan sunan Uban shi wato Abdullahi shi Kuma Hussaini aka Saka mishi sunan abdurrahaman.
Ya Dubi Farida Yana fadin
“Farida nayi Miki karambani na Sakawa Ya’yan ki suna ban sani ba ko kina da sunan da kike so ?.
Idon ta da Ruwan hawaye tace.
“Bakayi karambani ba baba sai dai Ina Rokon Alfarmar ka sakawa yaro Daya sunan marigayi Abdullahi Amma bayan Hakan duk yadda kayi yayi daidai Baba.
“Takbeer. Gaba Daya Yan D’akin suka dauki kabbara inda Baba isuhu ya ce
“Dama shi wannan Da akace shine hassan din shine Abdullahi shi kuma wannan Hussaini din shi Kuma abdurrahaman.
Suka Kuma daukar kabbara suna Fadin
“Allah ya jikan Abdullahi da Rahama ya shafe k’asa goshin sa yasa Yana dausayin ALJANNAH .
Basma ta fice tana tunanin kamar yaran Nan da Abdullahi da kuma irin sunan da aka Rad’a Musu.
TANA komawa sashin ta ta kira Wayar mamman Wanda ya dauka Yana Fadin
“Yaya kin samo min address din Nan? Na Rantse Miki ko Baki samo shi ba yau din nan zan Soma bin sashi sashi na kamfanin MTN don na Gane in ba hakan nayi ba Babu Ranar da zan kad’as da Filin Nan don duk ciki shine Abinda Nafi hadawa yawu.
“Ai Kai Aiki ya Kwana mamman matar Nan ta Haihu Wallahi sai yanzu Najwa take fada Mini.
“To Ina zuwa bari Nazo gidan naji Yaya za ayi.
Basma ta Soma safa da marwa tana Jiran Zuwan mamman.
Mamman kuwa da yake can tsakiyar kasuwar motoci Yana cinikin motar Basma inda cinikin ya fada aka tura mishi kud’in ta a account din sa ya wuce Yana fadin zai kawo musu takardun motar shiyasa ma ba zai kwashe Kayan da suke cikin motar ba ya Wuce inda Sukayi mahad’a da bangis Wani dillalin gidaje Wanda Suka hadu zuwa gidan Abdullahi mamman Yana Bude mishi sashin nan da Babu kowa ya nuna Mishi Yana Fadin
“Yadda kaga nan haka sauran suke Kuma duka ukun za a Siyar sai dai ba zan shigar da Kai sauran sashin ba saboda akwai Matan Aure a ciki na basu notice Nan da karshen wata zasu bar Gidan don haka ayi min siyen gaskiya biyan gaskiya kaga dai yadda wuri yake ko wannan sashin kad’ai milyon Tara aka Siya ban Siyar ba don Haka Kai Muji naka tayin .
Bangis ya Kuma zagayawa ya duba inda Shima yace a Taran zai biya Amma mamman yace Albarka Bai siyar ba in Bai shirya siye ba ya tafi sai ya shirya akwai masu so da yawa.
Gaga Gaga dai bangis aka Siya milyon Sha Biyu Biyu Amma mamman yace in an Siya Sha Biyar ya Siyar in ba a Siya ba kuwa yaje ya fasa.
Sai gashi kuwa bangis yace yayi ya bari zuwa anjima zai fadawa Mai gidan shi a turo kudi don shi Bashi da matsala in dai na duba naga yayi to Shima yayi mishi ka saurare ni Zuwa Anjima
Aikuwa ba a Rufa awa UKU ba mamman yaji shigowa kudin Nan a account din da ya bayar milyon Sha Biyar sau UKU Arba in da Biyar kenan .
Ya Isa wurin Basma tana karanta mishi Abinda yake faruwa a yanzu.
“Muje kawai ki fara karbar kudaden kaddarorin sa kafin Azo kan maganar Gado.
Tuni kuwa Basma ta Mike tana daukar gyalen ta Suka fita inda duk ta San kaddarorin Abdullahi suke Basma ta nunawa mamman su inda yace gidan da suke ciki ya kamata ta fara siyarwa.
Ta Dube shi tana Fadin
“Ka samo mini Mai siyen gidan Nan duka mamman na saida su in yaso har wadan Nan din ma duk na siyar da su.
Mamman Kam ya samo Wani dillalin aka Kuma Dora Wani cinikin tamkar Bai Karbi kud’in su bangis ba nan ma cininki ya fad’a aka turawa Basma kudin ta ta account.
Kafin a juya ga sauran gidajen can mamman ya samu Gano sashin da suka karbi hayar flotin Abdullahi ya Kuma shigar musu da bukatar son Siyarwa inda sukace zasu Siya dama sun jima suna bin Kan Mai shi ya siyar musu Amma sunce sai sun ga takardar da Abdullahi yayi sign inda mamman ya tafi don ya samo sign din Abdullahi wurin Basma yayin da Wani daga Cikin ma aikatan ya Soma Sanar da su cewa Mai wurin Nan fa ya bar Duniya ayi bincike Sosai musamman ta wurin manajan Abdullahi wato Kabir Wanda shine su ka sani . A take kuwa aka Kira Kabir aka Sanar dashi Abinda yake faruwa ya Kuma ce idan Wanda yayi musu tallar ya dawo kawo musu sign din su taimaka shi su Rike shi ba ta sigar fitina ba sai ta sigar yaudara sai a Kira shi yazo yaga Mai wannan kokarin don ya tabbatar musu da ba a San waye Mai wannan Aikin ba wata Kil ma Wani taka Haye ne zaiyiwa marayu kasafi da kayan gadon su. Suka Kuma yarda da Abinda ya fada don mamman Kam ya Yi kama da munafukai don Haka suka jirayi dawowar mamman .