Kyakkyawan kofin tambulan ne a Hannun shi Yana kurbar Ruwan gahawa wato coffee MSI zafi Yana shafa Sumar fuskar sa Yana tunanin juriyar da ya iya Yi ta shanye wannan tsawon Lokacin ba tare da ya Saka idon shi akan su ba. Bare kuma bege na gangar jiki Wanda ya Saka shi Dole ya Soma daukar azumin litinin da alhamis.
Yayi shar tamkar jinsin da yake cikin su wato ARAB don hasken fatar sa ta saje da shi din amma kuma zuciyar sa cuke take da BEGE mai yawa musamman.
Kyakkyawar wayar shi Yar k’arama Mai kyau ta dauki tsuwwa ya jawo ta Yana duba Mai Kiran inda yaga Mai Kiran yayi saurin dauka Yana Fadin.
“Na Soma gajiya Hakan Nan don Allah a fidda ni Daga wannan wakafin da aka ajiye ni na tuba na bi Allah na bika Ina fa cike da damuwa Kai ma ka Sani .
Ya kyalkyale da Dariya Yana Fadin.
“K’ara Hak’uri mutumi na an kusa fiddo ka daga wakafin Nan yanzu ma na duba WhatsApp ne naga baka online shine na bugo na fada maka na tura maka sako in ka hau zaka Gani Amma in ka Gani kar kayi Wani motsi ko kace Zaka fito wannan wakafin da na Saka ka Ina da Hikima fa ka sani Ina son ka San Wani Abu fa a yanzu Al Amura sai bayyana suke to har yanzu ba Azo kan gab’ar da zan karya ba so be careful my man saura k’iris nace Maka come see.
“To na Gode Amma fa banyi Maka alkawarin bin maganar ka d’ari bisa d’ari ba kar ma ace sakon da ka tura min din ya zamo ya Sab’a da Ra ayi na Malam Ina Mai tabbatar maka da sai dai ku ganni kamar daga Sama .
Ya aje wayar yana Shan coffee din sa.
Ranar juma a da yamma Hanan da Saddam suna kofar gida motar Sameer ta faka a kofar gidan su Farida.
Da gudu yaran suka nufi motar hannan ta balle murfin motar ta shiga tana Fadin.
“Daddy Mamin mu fa ta haifi twins baby masu kyau Wallahi muje na Kai ka ka gansu.
Ya Zubawa Bakin Hanan ido tana zayyana mishi zancen Farida ta Haihu.
“Yaushe Mamin ta haihu?
Ya tambaye ta ta ware yatsun hannun ta biyu tana nuna Mishi.
Saddam dai Yana tsaye s waje Yana kallon Daddy da Hanan a motar .
Sameer ya fito daga motar Yana Rik’e da Hannun Saddam ya Rungume shi Yana Fadin.
“Daddy’ Sannu da Zuwa ya Aiki?
Ya duka Yana shafa fuskar Saddam Yana fadin
“Lafiya Lau Saddam ya makaranta kana karatu dai ko?.
Ya amsa da kad’a kanshi Yana fadin
“Inayi Daddy Hanan ta fada Maka Mamin mu ta haifi twins?.
“Ta fada min Saddam kunje ku duba su ko?.
“Munje har muka taho da su Salman suna nan wurin Hajiya.
Ya Mike Yana Rik’e da su Suka shiga cikin Gidan inda Haj take Rarrashin Sulaiman Wanda yake kuka shi wurin Mami zaije.
Sameer ya SHIGA da sallama Haj ta Amsa mishi tana mishi Sannu da Zuwa
Ya duka Yana daukar Sulaiman Wanda suffar sa ta juye sak Abdullahi Amma Salman Kam Yana daukar kama da Saddam Amma Kuma shi fari ne tas irin Uban sa yayin da Saddam da Hanan suke wankan tarwada irin Sameer .
Sameer ya Soma Rarrashin yaron ya Kuma Yi Shiru kafin suka Soma gaisawa da Haj Yana tambayar yaushe su Sulaiman Suka zo?.
Haj tace
“Yau kwanan su biyar Uwar tasu ce ta Haihu sai Naga dawainiyar Zatayi mata yawa sai nace ta kawo min su nan su kwana biyu shine fa kaji Yana Zamanin shi Uwar sa zaije .
“Allah sarki yanzu Hanan take fada min Mamin su ta haifi twins baby masu kyau Allah ya Raya su bisa sunna anyi suna ne?.
“Anyi suna jiya ta samu Abdullahi da Abdurrahaman .
“Masha Allah haka Al Amarin Ubangiji yake Rayuwa kenan Mai Abu da yawa Rabon yaran Nan ne ya Raba mu dama ance Rabo in Bai kashe ba ai yayi da sauki shi Kuma Ajali iyaka ne duk Wanda yazo iyaka sai ya tsaya ba ga Abdullahi ba shi ya Tara’s da tashi iyakar? Allah yasa namu Rabon ne Kuma tafe. Ya fada Yana Duban Haj Yana Fadin.
“Haj Nazo a Yanzu na Kuma Rokon Alfarma zan dawo idan farida ta yarda mu mayar da Auren mu tunda yanzu ta fita Daga takaba Idan Kuma Bata yarda ba Haj ba zan matsa Mata ba.
“In Akayi hakan ma an kyauta Sameer shi Lamarin Allah ai haka yake yadda ya tsarawa bawa haka zai tafiyar. Bana tunanin zata k’i yarda in ma ba koma gareka ba ai Wani Mijin zata Jira Wanda ma Bata san ko waye ba.
“Nagode haj Amma zanje Naji ta Bakin mahaifiya ta idan har Bata Aminta da Hakan ba zanyi hak’uri na Rik’e matar da ta bani.
“Wannan gaskiya ne ayi ta ADDU A Kuma ana bawa Ubangiji zabi sai kaga ya kawo mafita Allah ya zaba Abinda yake shine Alherin.
Yana Rungume da Sulaiman Wanda yaki yarda ya Aje shi Dole ya mike Yana Rik’e da Sulaiman ya ajiwa yaran kayan tsarabar su Amma duk Hikimar da akayiwa Sulaiman akan ya taho Sameer ya wuce ya lik’e Mishi yaki yarda ya ajiye shi Dole Sameer ya wuce dashi inda Salman Shima yace zai bi Sameer sai su Saddam da Hanan ma Suka bi shi Dole ya zuba su a mota suka wuce . Yana tuk’i Yana shafa Sumar kan Sulaiman Yana Jin wata irin nadama akan Rayuwar da ya dauka ta keta haddin Ubangiji da son tab’a mace Wanda duka ya tattare su wuri Daya ya auna a mizanin hankali ya Kuma Gane mazinaci bashi da Abokin Hadi sai Dan Uwan sa mazinaci. Yayi abubuwa da yawa musamman na keta haddin Ubangiji da Aure ya so farida ta biye mishi don su kasafta ta shi da mijin ta amma ta nuna mishi har abada ba zatayi hakan ba. Da karfin tsiya yaso keta haddin ta Allah ya tsare ta . ko akan wannan kad’ai ya Isa Ubangiji ya jarrabe shi da mace irin wacce yake da ita a yanzu wacce har yanzu Bata Daina bibiyar Mustafa ba duk da ya Runtse ido ya karbe ta a matar Aure har ta Haihu Amma kuma ZUCIYA ta kasa tsayawa akan yaron nashi ne ko ba nashi ba Amma Dole ya karba tunda ya San yayi Shima kuma Dole ayi Mishi.
A nan ya tuno da matan auren da suka bibiya suna sane da igiyar auren su amma aka rufe kofa.
Ya kuma tuno da wasila wacce ya kawo gida amma farida ta dawo gidan duk da allah yana rufa asirin sa farida bats taba kama shi ba sai gashi uwar sa da matar sa har da kanin sa Allah ya bankada musu asirin sa.
Cikin sanyn jiki da nadama ya isa gidan su yana hango aika aikar da ya tafka
Hajiyar Sameer ta ganshi da yaran ta tarbi Saddam ta na Fadin
“Ikon Allah ku Kuma Daga Ina haka har da su mindau da Salmanu?.
Hanan ce tayi maza tace
“Haj ba fa haka ne sunan su ba shi wannan Salman ne sunan shi ba Salmanu ba shi Kuma Sulaiman ba mindau ba .
Sukayi Dariya Haj da Sameer tana Fadin .
“Ni Kuma haka na iya fada gwana Yar ka iya.
Ya zube a Gaban Haj Yana gaishe ta ta Amsa tana Fadin.
“Daga Ina kuke da wannan yaran ?.
“Nazo Gidan ne sai na Samu yaron Nan Sulaiman Yana Rigima shine da zan tafi yace Bai San zancen ba shine nace bari na tafi da shi shine Suma suka biyo Ni.
“Ayya Dake Uwar tasu ta Haihu na San don a rage Mata Aiki aka kawo su .
“Eh haka Haj ta fada min ance twins ta Haifa Allah ya Raya su da Imani.
“Ameen ya Rabb yanzu kazo ma ko? Ya amsa da Zuwan kenan .
“Yaya Aisha da Umar duk suna lafiya?.
“Lafiya Lau alhamdulillah Haj dama nazo ne na Roki Alfarmar ki Haj tunda Uwar yaran Nan Allah ya karbi Rayuwar mijin ta shine nake so na koma na dawo da ita Amma sai da yardar ki Haj sai kin Amince idan Baki Aminta ba zan Hak’ura Haj.
“A a Sameer Al Amarin Ubangiji waye yake shiga cikin sa matukar ba fatan ALHERI Zakayi ba? Allah ya sa Alheri ne komen naku Amma Farida ya kamata ka tuntuba don itace Mai Yi kuma ni in zan fada Maka ka yarda sai ka sauya daga yadda kake ka koma Wani Sameer din daban don matukar dai kana a yadda kake to bana Jin ko Kun koma zaku zauna lafiya duk da Kai ka baro Kari tun tubani Amma ni ADDU A ce tawa in Kun shirya kanku ai Alhamdulillah Amma wanna shawarar da na baka itace fitila.
“Nagode Sosai Haj Allah yaja da Rayuwa ai na sauya Wallahi tuni .
Ya Mike Yana Rungume da Sulaiman ya koma mota ya dauko tsarabar da ya Riko ya kawo Mata tana ADDU A da Saka Albarka
Haka ya fice da Yaran a mota Yana zaga gari da su Yana Kai su complex Yana Siya musu kayan kwalam har ya Siyawa Sulaiman takalma da kayan sanyi Wanda aka Saka Mishi tun a Nan su Salman da Saddam da Hanan kuwa jackets ya Siya musu da takalma Suma kafin ya mayar da su gida Amma ko a Nan Sulaiman Bai yarda ya Rabu da Sameer ba sai da akayi mishi Hikima kafin suka Rabu ana mishi dabara .
Kai tsaye Sameer ya nufi gidan Abdullahi don ya samu Farida da wannan maganar inda Kuma ya tuna barazanar da Basma tayi mishi na in ta Kuma Ganin shi a gidan zata FASA KWAI Amma sai ya tuna kakin da yake jikin shi Wanda a yanzu Bata Isa ta kawo mishi wargi ba sai yaji a yanzu Idan matar Nan ta nemi kawo mishi iskanci irin Wanda tayi a Ranar zai make ta ne ko don ta SHIGA taitayin ta don haka Bai ji ko dar ba ya Mike hanyar gidan.
A Ranar da akayi Kwanaki bakwai da Haihuwar Farida a Ranar ne Kuma Basma tace a Raba musu gadon su . A Ranar kuwa Yaya lami ta koma gida ta Kira Baba isuhu yazo ya Kuma ce a kotu take son ayi Rabon ko kuwa Gida? Basma tace alkaline zai zo Gida ya Raba Amma sai an auna jinin Salman da Sulaiman har ma da wadan Nan yaran da aka Haifa a Yanzu wato Abdullahi da Abdurrahaman don Bata yarda Ya’yan Abdullahi bane Basma da Najwa ne kadai Ya’yan Abdullahi.
“To kije ke da kike inkari akan Hakan ki Nemo alkalin ki Kuma dauko likitan da zai auna jinin Amma ta Yaya zamu Gane jinin nasu ba na Uban su bane tunda Uban nasu baya Raye.
“Shi likitan ai Yana da ilimin abin Baba ka barni dai kawai tunda ka bani WUKA da Nama ai ku jiraye ni don Yanzu zan Nemo alkalin da likitan in yaso nan da Gobe zaka tabbatar da Abinda nake nufin.
Ta juya ta dauki gyalen ta ta fito da nufin daukar mota Amma sai ta tuna tana Hannun mamman don haka sai ta Kira wayar shi tana Fadin.
“Mamman kana Ina? In kana kusa kawo min motar Nan futa ta kamani Yanzu.
“Ke mota fa tana gareji taci kuturus Ina Zaki Kuma bayan Gani Nan Zuwa gidan na Nemo Wanda zasu suyi filin can har Gani nan Zuwa karbar sign din marigayin mijin ki don Dole sai da shi za a biya kud’in nan don har na Fara k’iyasin milyon d’ari Biyu da Hamsin koma d’ari UKU zaku karba?.
“Sai dai ka Jira ni mamman don Nima Wani hanzarin ne na gaggawa bari kawai na hau Napep naje na dawo.
Ta fice daga gidan ta tsayar da Napep suka shilla . Wurin alkalin Nan ta Soma zuwa ta sanar Dashi kason da za ayi musu a gida Gobe don matar ta Haihu shine Ake son a Raba a bawa kowa hakkin sa. Ya amsa da zai gobe ta bashi address yace su Duka masu hakkkin su Kira alwalin su ko Wani daga Cikin iyayen su su Kuma zama cikin shiri don Kar a Bata mishi lokaci Kuma a Tara komai yadda da yazo kasafi kawai za ayi.
Ta amsa da komai Yana Nan a kammale . Kuma zata sanar musu.
Da haka tayi Mishi sallama ta wuce zuwa babbar Asibitin federal medical center ta dauki kwararren likita a lab Wanda ya kware da auna jini tace tana so Gobe Idan Allah ya Kaimu da karfe goman safe ya taho da kayan Aiki don zaiyi Mata Aikin gwajin jini na Yara shida inda ta biya shi kudin shi ta Kuma Bashi address din gidan sukayi musayar lambar waya ta tafi.
A Ranar ta sanar da su baba isuhu Da Yaya lami Abinda alkali yace haka Kuma ta sanar da Farida itama wai ta sanar da alwalin ta Farida ta Kira Haj ta fada Mata tace Gali zai zo a matsayin alwalin nata da haka aka aje magana inda itama Basma ta Kira kanin Uwar ta Wanda zai tsaya alwalin ta.
Washe gari kuwa sai ga alkali kamar yadda yayi Alkawari ya iso goman safe Shima Dr arwan ya iso da kayan Aikin shi inda Basma ta fito da wata takarda wacce take dauke da group din jinin Abdullahi wacce akayi lokacin da yayi jinya ta mikawa Dr arwan Wanda ya duba ta yaga kalar jinin Abdullahi Wanda yake a group A ta Kuma ce so take ya auna mata yaran Nan duka har da su Najwa duk Wanda ya zamo jinin shi ba group A bane to ta tabbata ba Ahalin Abdullahi bane .
Dr arwan ya bawa alkali takardar ya duba ya tabbatar da awon Asibiti ne ba bogi ba inda akayi ta bawa su garba da Kabir da Gali Baba isuhu da Yaya lami har da Farida dai duka an Basu sun duba sun kuma ga kalar jinin Abdullahi wato group A don haka a take Dr arwan ya tayar da inji aka hada mishi wuta ya kunna kayan Aiki inda akace a fara da su Abdullahi da Abdurrahaman Wanda Farida ta bawa Yaya lami su aka tsira musu Allura aka zuk’i jinin su aka Dora akan injin gwajin idanun kowa Yana Kan injin din ana ganin yadda yake juya jinin har ya gama juya shi Alamar an gama . Dr arwan yayi Rubutu akan takardar yaja layi ya ajiye ta a gefe aka koma kan Salman da Sulaiman Suma akayi zuk’i jinin su Daya bayan Daya akan dorawa kan inji Suma yayi Rubutu akan takardar yaja layi ya Rubuta sunan kowa akan takardar shi ya ajiye.
Aka zo kan su Najwa da Nabeela suma Daya Bayan Daya aka zuk’i jinin su aka Dora kan inji kamar yadda akayiwa sauran Suma aka gwada akayi Rubutu akan takardar kowacce aka ja layi inda Basma tace in an gama Dr arwan ya bayyanawa kowa Bayanin jinin kowane Kuma abawa kowa takardar gwajin ya Gani don kar ma Wani yace an munafunce shi shiyasa ma akayi akan idon kowa Kuma za a bawa kowa ya Gani ya Kuma karanta.
Dr arwan ya dauki takardun guda shida Yana Fadin.