LITTAFI NA DAYA
A wani zamani mai tsawo da ya shuɗe, an yi wani babban Sarki ana kiransa Shamsuddini. Ya kasance mai girman iko. Mulkinsa ya watsu cikin ƙasashen duniya, tun daga Kurasana har zuwa Sistani har iyakar tekun hindu. Babban birninsa shi ne Kunaimu Madudu. Yana da Wazirai goma waɗanda ke mulkin wasu jihohin daga ƙasarsa. Ƙarƙashin kowane Waziri akwai hakimai dubu, da dagatai dubu goma, da sauran masu faɗa a ji. Yana da mayaƙa, da bayi, da hadimai, da dukiya mai ɗumbin yawa. Talakawa na sonsa saboda yawan adalcinsa da kyautayinsa gare su. . .
Wannan labri ya anfani jama,a .muna jiran sauran littafi nagaba.