Shi kuwa dan aike da saurin sa yazo ya shaida masa abunda Widad tace, aikuwa ya fusata yace "tana ina"? yace "suna wajan bishiya wajan faculty din su".Yace "muje" Faruk yace " dan Allah ka kyaleta karta saka muje mutane su zuba mana ido" Affan yace "har ni zan kira wata shegiya ta ki zuwa to wallahi hukunchinta ya nin ku ,kuma Faruk sai naje naga dame take ta kama" yayi gaba suka biyo su a baya.
Sudais ne ya lallabo ta bayan su , suna karatu ya kwace handout dinta , tana dubawa, tayi saurin firgita tana juyawa , tana ganinsa tasa. . .