Shuraim da Affan sune suka fara tafiya kafin kowa , zuciyar su fes amma wani ban garan na zuciyarsu cike yake taf da fargabar abunda suka aikata.
A ka'idar masarautar ko mace ka kawo sai an gama bincike sosai San nan a baka damar auran ta in dan har tayi musu , shi kuwa gashi auran yayi ma ba tare da sanin Ahalin sa ba.
Affan ne da ya kasa boye damuwarsa yace" Yaya ya zamuyi mu fadawa su Papa kuma su fahimce mu?"
Shiru yayi na tsawan lokaci yace " ban sani ba Affan , idona ya rufe kar na rasa ta. . .